
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Mutum ɗaya tare da mai gari a Ƙauyen Sanyinna da ke Ƙaramar Hukumar Tangaza a Jihar Sakkwato sun rasu yayin da wasu da ake zargin mayaƙan Lakurawa ne suka farmaki ƙauyen a ranar Alhamis.
Mai taimaka wa Shugaban ƙaramar akan lamuran tsaro, Garzali Raccah ya tabbatar da aukuwar lamarin inda ya ce maharan sun je ƙauyen ne da misalin ƙarfe 1:30 na dare inda suka buɗe wa jama’a wuta gabanin zuwa gidan mai garin.
Ya bayyana cewa, wani ɓangare na Lakurawa ya gargaɗi mazauna ƙauyuka da kada su shiga aikin bijilante, lamarin da suka yi barazanar kisa ga duk wanda ya saɓa.
Shigar wasu mutane biyu cikin ƴan bijilanten ya fusata ƴan ta’addar bayan tsawon lokaci suna gargaɗi a kai.
Daga bisani jami’an sojoji ƙarƙashin atisayen FANSAR YAMMA suka halarci wajen da abin ya faru tare da ɗauke gawawwakin, sannan kuma suka cigaba da sintiri domin hana sake faruwar irin haka a gaba.
Harin ƙari ne akan adadin hare-haren da mayaƙan Lakurawa ke kai wa yankunan jihohin Sakkwato da Kebbi musamman ƙauyuka, wanda hakan ya sa mutane da dama suke gudun hijira daga muhallansu.
