Gwamnatin Tarayya ta gana da MACBAN kan shanun da ke yawo a titunan Abuja

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

A ƙarshen makon da ya gabata ne Gwamnatin Tarayya, Sarkin Musulmi, Alhaji Sa’ad Abubakar III, da sauran masu ruwa da tsaki suka gana da shugabannin ƙungiyar Makiyaya ta Miyetti-Allah (MACBAN) kan rahotannin da ake samu na cewa shanu suna yawo a titunan Abuja.

An gudanar da zaman tattaunawar ne a babban masallacin ƙasa da ke Abuja, a wajen Sarkin Musulmi, wanda kuma shi ne shugaban kwamitin amintattu na ƙungiyar MACBAN.

Taron ya kuma samu halartar manyan masu ruwa da tsaki da suka haɗa da Ministan Dabbobi, Alhaji Idi Mukhtar Maiha, babban sakataren hukumar kula da ilimin makiyaya ta ƙasa (NCNE), Kaduna – Farfesa Bashir H. Usman, da shugabannin al’ummar makiyaya a ƙananan hukumomi 6 na babban birnin tarayya Abuja da dai sauransu.

Da yake jawabi a wajen tattaunawar, Sarkin ya buƙaci masu kiwon shanu da su sanya ‘ya’yansu makaranta, inda ya bayyana cewa ilimin boko na da matuƙar muhimmanci ga ci gaban su da kuma jin daɗin su baki ɗaya.

Sarkin Musulmi ya ce, ya kamata makiyaya su fifita ilimi fiye da saka jarin kiwo a rayuwar ‘ya’yan su.

Da yake jawabi ga manema labarai bayan tattaunawar, babban mataimaki na musamman ga shugaban ƙasa kan Harkokin Raya Dabbobi, Idris Abiola-Ajimobi, ya ce gwamnatin shugaban ƙasa Bola Tinubu na haɗa kai da hukumomin da abin ya shafa domin magance musabbabin matsalolin da ake samu na shanun da ke yawo a babban birnin ƙasar.

Ya ce, a matsayin mafita mai ɗorewa ga matsalolin da ke addabar makiyaya a ƙasar nan, gwamnatin tarayya na aiki da wuraren kiwo da kuma farfaɗo da wuraren kiwo, ciki har da yankin sarrafa masana’antu na musamman na Agro.

Ya ce: “Mun zo nan ne domin taron tattaunawa na masu ruwa da tsaki, taro ne don tattaunawa da masu ruwa da tsaki a harkar kiwo don fahimtar da ƙoƙarin da gwamnatin shugaba Tinubu ke yi.

“Muna aiki tare da Ma’aikatar Raya Dabbobi da sauran hukumomin da abin ya shafa don magance tushen matsalolin, matsalar dabbobin da ke yawo a titunan Abuja, mu fara magance matsalar kiwo, muna aikin kiwo, muna kuma aiki da wani yankin sarrafa masana’antu na Agro na musamman.

“Har ila yau, muna aiki kan farfaɗo da wuraren kiwo, samar da abinci da kiwo ta yadda makiyaya za su iya samun wani yanki mai aminci don gudanar da rayuwa da zaman tare tare da samun dukkanin abubuwan more rayuwa da suke buƙata, kamar abinci, ruwa, tsarin kiwon lafiya, asibitocin dabbobi da sauran muhimman ayyuka.”

By ukarofi