Gwamnati ta mayar da darasin Tarihi wajibi ga ƴan firamare da sakandare

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Gwamnatin Tarayya ta sanar da sake gabatar da Tarihi a matsayin ɗaya daga cikin wajibabbun darussa a baki ɗaya makarantun firamare da ƙaramar sakandare da nufin farfaɗo da haɗin kai da kishin ƙasa acikin al’umma.

A ranar Laraba Ma’aikatar Ilimi ta sanar da haka ta shafinta na X, inda ta ce a karo na farko cikin shekaru da dama za a cigaba da koyar da yara darasin tun daga aji 1 a firamare zuwa aji 3 a ƙaramar sakandare.

Ta ce, za a riƙa amfani da ‘Civic and Heritage Studies’, ‘Integrated History’ da kuma ‘Civic Education’ a yayin karantarwar.

Ƴan aji 1 zuwa 6 a firamare za a riƙa koyar da su tarihi akan asalin Nijeriya, gwaraza, sarakuna, al’adu da yaruka, siyasa, tattalin arziƙi, addinai, mulkin mallaka da mulki gabanin samun ƴancin kai.

A ɗaya gefen kuwa, za a riƙa koya wa ƴan aji 1 zuwa 3 a JSS wayewa da ci-gaban Nijeriya a fannoni daban-daban, tsofaffin masarautu, rabe-raben kasuwanci, alaƙa da Turawa, haɗa arewa da kudancin Nijeriya, ƴancin kai, dimukraɗiyya da martabobin ƙasa.

Haka kuma, ƴan aji 1 zuwa 3 a SSS za a ke koyar da su sabon darasi mai suna ‘Civic and Heritage Studies’, wanda ya haɗe Civic Education da wasu muhimman ɓangarori na tarihin Nijeriya domin sanin kimar zama ɗan ƙasa da zurfafa alfahari da ƙasa.

Ma’aikatar ta bayyana sauyin a matsayin kyauta ta musamman ga goben ƙasa duba da yadda hakan zai taimaka wajen kusanto da yara da asalinsu don alfahari da ƙasar, haɗin kai da sanin ciwon kai.

By Babaji