Ba za a dakatar da asusun bankunan ƴan Nijeriya ba saboda rashin lambar haraji – JTB

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Hukumar Haɗaka ta Haraji JTB, ta ƙaryata rahotannin da ke cewa za a dakatar da asusun bankuna na ƴan Nijeriyar da ba su da lambar haraji, wato Tax ID daga ranar 1 ga Janairun 2026.

Hakan na zuwa ne bayan da Kwamitin Shugaban Ƙasa akan Kasafi da Gyare-gyaren Haraji ya fitar da wani kundi, wanda a ciki akwai batun cewa ta yiwu waɗanda ba su da Tax ID su rasa damar gudanar da asusun bankuna, tsare-tsaren inshora, kuɗaɗen fansho of kuma lamuran zuba jari bayan kwanan watan da aka bayyana.

A wata takarda da Kakakinta, Akpe E. Adoh ya fitar, JTB ta tabbatar wa ƴan Nijeriya cewa za su cigaba da amfani da asusun bankunansu da wasu harkokin da suka shafi kuɗaɗe ba tare da wani tsaiko ba ko mutun na da Tax ID ko ba shi da shi.

JTB ta bayyana cewa, gyare-gyaren haraji abu ne da ake yi da nufin sauƙaƙe hanyoyoyin ƙarba da biya daga al’ummar ƙasa da rage biya sama da ƙa’ida da kuma ƙara fito da shi fili ga kowane ɗan ƙasa.

Haka kuma, ta ce za a tsame marasa galihu da masu ƙananan sana’o’i daga sahun masu biya yayin da da dama daga ƴan Nijeriya za su riƙa biyan kuɗin haraji mara yawa a sabon tsarin.

Ta ƙara da cewa, tana aiki tare da haɗin-gwiwar Hukumar tattara haraji ta ƙasa (FIRS) da hukumomin haraji na jihohi wajen mayar da tsarin karɓar haraji na bai-ɗaya.

By Babaji