EU Da UNICEF sun samar da sabon tsarin ƙarfafa ilimi a Jigawa

Spread the love

Daga UMAR AKILU MAJERI a Dutse

Ƙungiyar Tarayyar Turai (EU) da Asusun Kula da ƙananan Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya UNICEF, tare da haɗin gwiwar SUBEB sun ƙaddamar da gangamin wayar da kai kan sanya yara a makarantu a Jigawa.

Shirin ya fara ne a ƙananan hukumomi bakwai na jihar ta Jigawa da aka zaɓa a matsayin cibiyoyin da aka fara aiwatar da shirin a matsayin gwaji .

Kwamitocin kula da makarantu (SBMCs) sun yaba da wannan ƙoƙari, inda suka bayyana cewa ya dace da lokacin da sabon zangon karatu ya fara.

A Jahun, Malam Ja’afar Danbaba ya ce shirin ya tara masu ruwa da tsaki daga sassa daban-daban, tare da bayyana musu muhimmancin da suke da shi wajen ɗaukar yara makaranta.

Shugaban SBMC na Birnin Kudu, Malam Ahmad Chiroma, ya yi kira da a tabbatar da ɗorewar shirin don ƙara shiga makarantu a jihar.

A Hadejia kuwa, Malam Aminu Hassan ya ce shirin ya kawo canji mai kyau, musamman da aka haɗa mata cikin tattaunawa kan ilimi.

Shi ma Malam Ali Babale na Kafin Hausa ya ce halartar jama’a gamgamin ya ƙayatar matuƙa, wanda ake sa ran zai haifar da ɗa mai ido.

Ya yi kira ga gwamnati da abokan hulɗa da su tabbatar da ɗorewar shirin zuwa tsawon lokaci.

Babale ya kuma nemi haɗin kan dukkan ƙananan hukumomi domin a samu ci gaba mai yawa a fannin ɗaukar yara makaranta.

By ukarofi