
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Ana sa ran a ƴan kwanakin nan al’ummar Nijeriya za su samu rangwamen kuɗaɗe da suke biya wajen sayan katin kira da data yayin da Gwmanatin Tarayya ta sanar da soke harajin kaso 5 da a baya aka sanya wa kamfanonin telekoms.
Hukumar Wayar da kai ta Ƙasa NOA, ta sanar da hakan a wani saƙo da ta wallafa ta kafar X, ranar Alhamis.
A cewar saƙon, Mataimakin Shugaban Hukumar Sadarwa (NCC), Dakta Aminu Maida ya ce Shugaba Bola Tinubu ya umarci da a cire harajin a yayin da ake zaman tattaunawa akan aiwatar da sabuwar Dokar Kuɗi.
Dakta Maida ya bayyana cewa, an ɗauki matakin ne da nufi sauƙaƙe wa al’umma da kasuwanci adadin kuɗaɗen da suke kashewa a lamuran duba da hauhawar farashin kayayyaki da ƙarin kaso 50 da kamfanonin suka yi wa kwastomomi.
Ya kuma ce, hakan yunƙurin Shugaban ƙasar ne na rage nauyin kashe-kashen kuɗaɗe da ke kan al’umma da kuma tallafa wa ci-gaban tattalin zamani.
Ana tsammanin wannan ci-gaba ya samar da sauƙi ga sama da ƴan Nijeriya miliyan 171 da ke amfani da kayayyakin telekom a sassan ƙasar.
