Gwamnatin Katsina ba ta rufe cibiyoyin shirye-shiryen NCE, difloma da digiri a Jami’ar FUDMA ba – Kwamishinan Ilimi

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Kwamishinan Ilimi mai zurfi na Katsina Hon. Muhammadu Isa, ya yi wannan tsokaci da yake musanta rahotannin da ake ta haɗawa cewa gwamnatin Katsina ta rufe cibiyoyin. Ya bayyana cewa Gwamnatin Katsina ba ta soke ko rufe cibiyoyin shirye-shiryen karatun NCE, difloma, da digiri a Jami’ar FUDMA da ke Dutsinma.

Ya ƙara da cewa, ko a kwamitin da aka ƙaddamar tun a baya ya nuna cewa, wasu manyan makarantu masu zaman kansu suna gudanar da shirye-shiryen NCE, Difloma, da Digiri ba bisa ƙa’ida ba, kuma ba tare da izini daga hukumar NCCE ko NUC ba, wanda yawancin waɗannan cibiyoyi suna amfani da makarantun Firamare da Sakandare mallakar gwamnati, wanda hakan ba daidai ne ba a ɓangaren ilimi.

Kwamishinan ya yi ƙarin haske da cewa, cibiyoyin da ba a amince da su ba ne kawai aka umarci a rufe har sai sun cika ƙa’idojin da ake buƙata don kare martabar ilimi a jihar.

Ya kuma buƙaci jami’ar tarayyar dake Dutsin-Ma, da ta samar da gini nasu na kansu, da kuma samar da ingantattun kayan aiki idan suna son gudanar da cibiyoyin, maimakon dogaro da Makarantu mallakar Gwamnati a lokacin koyarwa.

Bada jimawa ba gwamnatin jihar ta sanar da rufe makarantu na gaba da sakandare masu zaman kansu da ke koyar da shirye shiryen NCE, Diploma na Digiri ba bisa ƙa’ida ba.

By ukarofi