Ƙungiyar haɗin kan Funtua ta taya Dikko Raɗɗa murnar cika shekara 59

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina.

An bayyana gwamna Dikko Raɗɗa a matsayin mutum mai haɗaka, jajircewa da hangen nesa.

Shugaban ƙungiyar haɗin kan Funtua kwamred Mannir Suleiman ya sanar da haka a wata hira da manema labarai a Katsina.

Ya ce babu shakka, biyayya ga iyaye, sadaukar da kai yasa gwamna Dikko Raɗɗa ya tsawon rayuwarsa da yayi a duniya yayi ta samun ɗaukaka da har ta kai shi ga wannan matsayi.

Kwamred Suleiman ya bayyana cewa Dikko Raɗɗa mutum ne mai sauraren al’ummar sa “ya ji koke koken su ,ya kuma share masu hawaye,”inji kwamred.

Ya faɗi wasu ayyuka na alheri da gwamnan ya aiwatar da ya taɓa rayuwar al’ummar jihar.

“Ya ɗauki malaman makaranta primary 7000 aiki na dindindin ya gina manyan tagwayen hanyoyi a inda ake buƙata,ya maida cibiyoyin kiwon lafiya zuwa manyan asibitoci da sakarwa ƙananan hukumomi kuɗaɗen su na wata,”kwamred Suleiman ya ce.

Ya ce waɗannan ma kaɗai sun isa a jinjina masa da sauran aikace aikace na na bunƙasa jihar da gwamnan ya aiwatar.

Shugaban ƙungiyar ya kuma yabawa gwamna wanda yace ya kawo cigaba da aka daɗe ana jira a yankin Funtua.

“Dikko Raɗɗa yana ɗaya daga cikin waɗanda sukai ruwa da tsaki wajen ganin Funtua ta sami jami’a, ya gina manyan tagwayen hanyoyi da sauran abubuwa na alheri da ya kawo ma yankin,”inji kwamred Suleiman.

Sai yayi addu’a Allah kara wa gwamnan lafiya da karfin gwiwar cigaba da zuba ayyuka na alheri a faɗin jihar.

Kwamred Suleiman ya kuma kira ga gwamnan Dikko Raɗɗa da ya kara jajircewa wajan kokarin da yake yi na magance matsalar tsaro da ya addabi wasu sassan jihar musamman kudancin Katsina.

By ukarofi