
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Rundunar ƴan sanda a Abuja, ta ce ta fara gudanar da bincike akan wata gawa da aka gano a harabar Majalisar Dokoki ta Ƙasa, wadda aka jibge acikin mota.
An gano cewa, gawar ta wani mutum ce mai suna Gaddafi Iwar ɗan shekeru 55, wanda kuma ɗan ƙabilar Tibi ne. Haka kuma, lebura ne shi a wani wajen aikin gini da ke kewayen majalisar..
An gano gawar ne a wata mota ƙirar ‘Peugeot 406’ mai lambar BWR-577 BF da misalin ƙarfe 9 na daren Lahadi wayewar Litinin.
Lamarin da ya jefa ma’aikata da masu gadi a majalisar cikin jimami gabanin ƴan sandan su shigo cikin al’amarin.
Kakakin ƴan sandan birnin tarayya, SP Josephine Adeh a wata takarda, ta tabbatar da aukuwar lamarin, inda ta ce ofishinsu ya samu kiraye-kirayen gaggawa daga majalisar game da batun.
Akan haka ne rundunar ta shirya wata tawaga ta musamman domin gudanar da bincike akan al’amarin.
Kazalika, ta kuma tabbatar da cewa za su cigaba da ba al’umma ba’asi game da sakamakon binciken nasu.
