
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Gwamnatin Jihar Inugu ta zargi shugaban kamfanin Sujimoto Luxury Construction Limited, Olasijibomi Ogundele da damfarar jihar Naira biliyan 5.7 da aka biya na kwangilar gina makarantun Smart Green guda 22 a jihar.
Kakakin Gwamna Peter Mba ya sanar da haka a ranar Juma’a.
Da fari, Hukumar Hana yi wa Tattalin Arziƙin Ƙasa Ta’annati EFCC, ta sanar da neman Ogundele ruwa-a-jallo bisa zargin sa da sauya akalar kuɗaɗen gwamnati.
Sa’o’i kaɗan da haka ne aka gan sa a wani faifan bidiyo yana zubar da ƙwalla tare musanta zargin da ake yi masa akan al’amarin.
A cewarsa, zargin ya samo asalin ne daga wata kwangila da ya karɓa daga hannun gwamnatin jihar duk da tsaiko na kulawa da farashi.
Ya bayyana cewa, hauhawar farashi da hare-hare akan ma’aikatansa ya sa suka gaza aiwatar da kwangilar, inda ya bada misali da tashin farashin siminti daga N7,000 zuwa 10,000 ga kowane buhu.
Gwamnatin jihar ta ce, Ogundele ya karɓi kaso 50 na aikin, inda daga lokacin ya bar aikin makaratun wanda ba a yi kaso mafi girma daga ciki ba.
Ta kuma zargi ɗan kwangilar da yin amfani da asusun kamfanin na bankin Zenith a madadin na bankin Ja’iz, wanda da shi ne aka amince ya karɓi kwangilar, lamarin da ya sa aka rasa damar ɗora alhakin akan bankin.
