ukarofi

12654 Posts
Uwa ba tare da hannuwa ba: Fuskar da ke bayyana irin matsanancin halin da mata da yara ke ciki a Gaza

Uwa ba tare da hannuwa ba: Fuskar da ke bayyana irin matsanancin halin da mata da yara ke ciki a Gaza

Nebal al-Hessi, wadda aka yanke hannuwanta, ta zama fuskar da ke bayyana irin matsanancin halin da mata da yara ke ciki a Gaza.  Labarinta ya fito a manyan kafafen yada labarai na duniya a matsayin misalin illar yaƙi ga fararen hula. Nebal ta bayyana yadda take kallon yaronta na girma ba tare da ta iya rungumarsa ba, ba tare da ta samu damar hidimta masa ba kamar yadda iya ke wa 'ya'yansu na daga al'ada. Lamarin wannan baiwar Allah na ƙara nuni da irin raunin kayan aƙaji da ake kai wa cikin Gaza da kuma girman bala’in da yankin yake…
Read More
‘Yan bindiga sun halaka ɗan Marigayi Gaddafi, Saif al-Islam a Libiya

‘Yan bindiga sun halaka ɗan Marigayi Gaddafi, Saif al-Islam a Libiya

Rahotanni daga ƙasar Libiya sun nuna cewa wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne, sun halaka Saif al-Islam Gaddafi, wanda ɗan tsohon shugaban ƙasar Marigayi Muammar Gaddafi ne. A cewar Al Jazeera ana ganin an harbe Saif al-Islam ne a yankin Zintan da ke Yammacin Libiya inda a nan yake zaune tsawon shekaru da dama. Kawo yanzu dai ba a san musabbabin kashe Saif al-Islam ba. Wata ‘yar uwarsa ta shaida wa gidan talabijin na ƙasar cewa ya mutu ne a kusa da iyakar ƙasar da Aljeriya, ba tare da bayyana ta yadda ya mutu ba. An daɗe ana ɗaukarsa…
Read More
Matashi ya daddatsa mahaifinsa da adda har lahira

Matashi ya daddatsa mahaifinsa da adda har lahira

Rundunar ’yan sanda ta kama wani matashi kan zargin sa da kashe mahaifinsa ta hanyar daddatsa shi da adda a Jihar Kuros Riba. Ana zargin Bassey Ubi, ya yi wa mahaifinsa kisan gilla ne bayan sun sanu saɓani a ranar Asabar. Washegari bayan kowannensu ya dawo daga coci cacar baki ta kaure tsakaninsu a gidan nasu da ke unguwar kusa da fadar basaraken O-3 , Usaja, da ke Ikpakapit Abgarun Ugep, hedikwatar ƙaramar Hukumar Yakurr, Jihar Kuros Riba. Kisan gillar da ɗan ya yi wa mahaifinsa ya yi matuƙar harzuƙa matasan unguwar inda su ma suka yi kukan kura suka…
Read More
Dariya ta rikiɗe zuwa kuka bayan matashi ya manne laɓɓansa yayin barkwanci

Dariya ta rikiɗe zuwa kuka bayan matashi ya manne laɓɓansa yayin barkwanci

Kwanan nan ne wani bidiyo na wani mutum ɗan ƙasar Philippines ya ɗauki hankalin jama’a a intanet. A cikin bidiyon, mutumin ya shafa sufa-gilu a laɓɓansa a matsayin wani ɓangaren na wasan barkwanci, amma lamarin ya sauya zuwa wani abun daban. Mai wasan barkwanci ya liƙe laɓɓansa bayan da ya shafa musu gam ɗin sufa-gilu a yayin da yake yin bidiyo kai-tsaye domin ƙayatar da masu bibiyarsa. Mutumin ya shafa gilu ne, inda ya manne laɓɓansa, wanda cikin dakika kaɗan, mannewar ta kama fatar laɓɓan kamar yadda ya so, inda hakan ya sa yabar laɓɓansa a rufe sosai. A zamanin…
Read More
Yadda gobara ta laƙume dukiyar miliyoyin Naira a kasuwar Singer ta Kano

Yadda gobara ta laƙume dukiyar miliyoyin Naira a kasuwar Singer ta Kano

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Wata gobara da ta tashi da sanyin safiyar Litinin ta yi ɓarna a wasu sassa na babbar kasuwar Singer da ke birnin Jihar Kano, lamarin da ya jawo fargaba a tsakanin ’yan kasuwa da mazauna yankin. Rahotanni sun nuna cewa wutar ta kama ne da misalin ƙarfe uku da mintuna sha shida na asuba, inda ta fara ƙonewa a wasu shaguna kafin ta bazu zuwa wasu wurare na kasuwar mai cike da cunkoso da harkokin kasuwanci. Mai magana da yawun Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kano, Saminu Yusif, ya tabbatar da faruwar lamarin, yana mai cewa…
Read More
Gwamnatin Tarayya ta ƙaddamar da shirin horar da ’yan Nijeriya miliyan 10 hada-hadar kuɗi

Gwamnatin Tarayya ta ƙaddamar da shirin horar da ’yan Nijeriya miliyan 10 hada-hadar kuɗi

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Gwamnatin Tarayyar Nijeriya ta ƙaddamar da shirin horas da ’yan ƙasa miliyan 10 kyauta kan ilimin hada-hadar kuɗi da shigar kuɗi cikin tsari, inda ta ce matasa da mata ne ginshiƙin cin gajiyar yawan al’ummar ƙasar.  Mataimakin Shugaban ƙasa, Sanata Kashim Shettima, ya bayyana hakan a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja, yayin da yake wakiltar Shugaba Bola Ahmed Tinubu. Ya ce ba za a iya gina tattalin arzikin dala tiriliyan ɗaya ba tare da kwararrun ma’aikata, nagartattun ƙa’idoji da ingantaccen tsarin sana’o’i ba. A yayin taron, Ofishin Mataimakin Shugaban ƙasa ta hannun Kwamitin Shugaban ƙasa…
Read More
’Yan kasuwar Onitsha sun buɗe shaguna bayan umarnin gwamna Soludo

’Yan kasuwar Onitsha sun buɗe shaguna bayan umarnin gwamna Soludo

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD ’Yan kasuwar babbar kasuwar Onitsha a jihar Anambra sun koma bakin aiki tare da buɗe shagunan su, bayan bin umarnin da Gwamna Chukwuma Soludo ya bayar na dakatar da biyayya ga dokar zaman gida da wasu ƙungiyoyi ke ƙaƙaba wa a yankin Kudu maso Gabas. Rahotanni sun nuna cewa mako guda bayan gwamnatin jihar ta rufe kasuwar domin ladabtar da masu ƙin bin umarni, ’yan kasuwar sun fara komawa tun da sassafe domin ci gaba da harkokin su na yau da kullum. Tun misalin ƙarfe 8:45 na safiyar ranar Litinin, an fara ganin masu saye da…
Read More
Sauye-sauyen Tinubu sun farfaɗo da arzikin jihohi 27 – Idris

Sauye-sauyen Tinubu sun farfaɗo da arzikin jihohi 27 – Idris

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya bayyana cewa sauye-sauyen tattalin arziki da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ƙaddamar sun ceci aƙalla jihohi 27 na Nijeriya daga faɗawa halin durƙushewar tattalin arziki. Idris ya yi wannan bayani ne yayin da yake gabatar da lakca a bikin yaye ɗalibai karo na 34 da kuma bikin cika shekaru 43 da kafuwar Jami’ar Fasaha ta Tarayya da ke Minna, a ranar Asabar. Lakcar da ministan ya gabatar ta mayar da hankali kan rawar da matasa za su taka wajen gina ƙasa a wannan zamani na…
Read More
Sai an inganta rayuwar matasa ƙasa za ta bunƙasa – Tinubu

Sai an inganta rayuwar matasa ƙasa za ta bunƙasa – Tinubu

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu ya bayyana cewa babu wata ƙasa da za ta iya samun ci gaba mai ɗorewa idan ba ta zuba jari kai tsaye a rayuwar matasanta ba, musamman ta fuskar ilimi da bunƙasa ƙwarewa. Shugaban ya bayyana hakan ne ta bakin ƙaramar Ministar Ilimi, Farfesa Suwaiba Sa’id-Ahmad, wadda ta wakilce shi a bikin yaye ɗalibai karo na 34 da kuma cikar jami’ar shekaru 43 da kafuwa na Jami’ar Fasaha ta Tarayya da ke Minna (FUT Minna). A cewar shugaban, bai kamata wani ɗan Nijeriya ya rasa damar samun ingantaccen ilimi ba saboda…
Read More
PDP ba ta mutu ba, za mu farfaɗo da ita, inji Ortom

PDP ba ta mutu ba, za mu farfaɗo da ita, inji Ortom

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Tsohon gwamnan jihar Benuwai, Samuel Ortom, ya ce, jam’iyyar PDP za ta kawo ƙarshen ƙalubalen da take fama da su tare da neman magoya bayan jam’iyyar da ka da gwiwarsu ta sare. Ortom ya yi wannan kira ne a ranar Lahadi a yayin da ya kai ziyara gidan tsohon mai taimaka masa a Makurdi. Tsohon gwamnan ya ce, ba za ta mutu ba saboda shugabannin jam’iyyar na ƙoƙarin yin duk mai yiwuwa wajen inganta jam’iyyar a dukkan matakai. Ya kuma bayyana cewa har yanzu tana da ƙarfinta, yana mai cewa babbar kwamitin jam’iyyar zai…
Read More