Uwa ba tare da hannuwa ba: Fuskar da ke bayyana irin matsanancin halin da mata da yara ke ciki a Gaza

Spread the love

Nebal al-Hessi, wadda aka yanke hannuwanta, ta zama fuskar da ke bayyana irin matsanancin halin da mata da yara ke ciki a Gaza. 

Labarinta ya fito a manyan kafafen yada labarai na duniya a matsayin misalin illar yaƙi ga fararen hula.

Nebal ta bayyana yadda take kallon yaronta na girma ba tare da ta iya rungumarsa ba, ba tare da ta samu damar hidimta masa ba kamar yadda iya ke wa ‘ya’yansu na daga al’ada.

Lamarin wannan baiwar Allah na ƙara nuni da irin raunin kayan aƙaji da ake kai wa cikin Gaza da kuma girman bala’in da yankin yake ciki wanda ya zarta alkaluma da ake fitarwa.

Da wannan ne ƙungiyoyin jinƙai suka ƙara ƙaimi da kuma kira da a linka abinda ake yi don ceto fafaren hula a yankin inda suka bayyana cewa irin wannan hali na buƙatar ɗaukar mataki daga ƙasashen duniya, ba maganganu na fatar baki kaɗai ba.

By ukarofi