Sojojin Pakistan sun ce sun kashe ’yan bindiga 145 bayan hare-haren da suka kashe kusan mutane 50. Wannan na daga cikin mafi girman hare-haren ramuwar gayya da gwamnati ta taɓa kaiwa a yankin.
Jaridun duniya sun bayyana cewa rikicin Balochistan ya samo asali ne daga korafin rashin adalci, rabon arziki da siyasar tsakiya, wanda ke kara rikitar da matakan soja.
Pakistan ta sake zargin Indiya da Afghanistan, yayin da kasashen ke musanta hannu a cikin kowanne irin rikici da ƙasar ke fuskanta.
Saidai duk da hakan lamarin na kara tsananta rikicin diflomasiyya a yankin Kudancin Asiya.
