ukarofi

12654 Posts
Kwankwaso bai tattauna batun sauya sheƙa zuwa APC da Tinubu ba – NNPP

Kwankwaso bai tattauna batun sauya sheƙa zuwa APC da Tinubu ba – NNPP

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Jam’iyyar NNPP ta musanta rahotannin da ke cewa jagoranta na kasa kuma tsohon Gwamnan Jihar Kano, Rabiu Musa Kwankwaso, ya tattauna ko yana shirin sauya sheƙa zuwa Jam’iyyar APC. A cikin wata sanarwa da sakataren yada labarai na kasa na jam’iyyar, Ladipo Johnson, ya fitar, ya bayyana zarge-zargen a matsayin karya da kuma wani yunkuri na wasu jiga-jigan siyasa na bata sunan Kwankwaso. Ya ce Kwankwaso bai taba tunanin shiga APC ba, kuma bai taba ganawa da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ko wakilansa domin tattauna batun sauya sheƙa ba. Johnson ya ce ganawar karshe…
Read More
An yi musayar yawu tsakanin APC da ADC kan rajistar ‘yan jam’iyyar APC da ake yi ta intanet

An yi musayar yawu tsakanin APC da ADC kan rajistar ‘yan jam’iyyar APC da ake yi ta intanet

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Jam’iyyar APC ta yi watsi da ƙaryata zargin da jam’iyyar ADC ta yi mata na tilasta ma’aikatan gwamnati wajen yin rajistar shaidar zama ‘yan APC a rajistar da jam’iyyar ke yi a faɗin Nijeriya. A cikin jawabin da sakataren yaɗa labaran jam’iyyar APC ya sa wa hannu, Feliɗ Morka, ya ce, fargaba da tsoro ne suka sa ADC furta wannan zargi saboda irin dubban mutanen da suke zuwa yin rajistar shiga jam’iyyar. A ranar Lahadi ce ADC, ta hannun sakataren yaɗa labaranta na ƙasa, Bolaji Abdullahi, ta nuna damuwarta game da rahotanni da ke…
Read More
Atiku da Abdulaziz Yari sun yi ganawar sirri

Atiku da Abdulaziz Yari sun yi ganawar sirri

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Tsohon Mataimakin Shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, ya yi wata ganawar sirri da tsohon Gwamnan Jihar Zamfara kuma Sanatan Zamfara ta Yamma, Abdulaziz Yari. Atiku ya yi wannan ganawa ta sirri da Yari ne, bayan ya karɓi baƙuncin tsohon gwamnan a gidansa da ke Abuja. Bayan ganawar tasu, wadda ba tare da shigar ’yan jarida ba, har yanzu ba a bayyana abin da suka tattauna ba. Wannan na zuwa ne a yayin da shirye-shiryen babban zaɓen shekarar 2027 ke ƙara ƙarfi a yayin da fitattun ’yan siyasa ke sauya sheƙa. A kwanakin baya Atiku Abubakar…
Read More
Grammy Awards 2026: Daren da ya sanya duniya ta sake sanin ƙarfin waƙa

Grammy Awards 2026: Daren da ya sanya duniya ta sake sanin ƙarfin waƙa

Daga AISHA ASAS  A daren Lahadi, 1 ga Fabrairu, 2026, idanuwan duniya suka karkata zuwa birnin Los Angeles na ƙasar Amurka, inda aka gudanar da bikin karrama mawaka na Grammy Awards karo na 68 a babban dandalin Crypto.com Arena. Wannan taro, wanda ke ɗaya daga cikin manyan abubuwan nishaɗi a duniya, ya sake nuna matsayin sa a matsayin madubi da ke bayyana halin da duniyar waƙa ke ciki a kowace shekara. Rahotanni daga wajen taron sun bayyana cewa, dubban fitattun mawaƙa, masu shirya waƙoƙi, marubutan baitoci, da manyan jiga‑jigan masana’antar kiɗa sun halarci bikin, yayin da miliyoyin mutane a faɗin…
Read More
EFCC ta cika hannu da fitacciyar Jarumar Kannywood bisa zargin wulaƙanta Naira

EFCC ta cika hannu da fitacciyar Jarumar Kannywood bisa zargin wulaƙanta Naira

Daga AISHA ASAS  Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa ta ƙasa (EFCC) ta kama fitacciyar jarumar Kannywood, Samha Inuwa, bisa zargin wulaƙanta kuɗin Najeriya, bayan bazuwar wani bidiyo da ke nuna tana amfani da takardun Naira wajen share majina daga hancinta. Bidiyon ya yaɗu cikin sauri a kafafen sada zumunta, inda jama’a suka rarrabu tsakanin masu kira da a hukunta ta da masu ganin a bi doka cikin natsuwa. Masana doka sun jaddada cewa, wulaƙanta Naira ba karamin laifi ba ne, kasancewar kuɗin ƙasa alama ce ta ’yancin kai da mutuncin ƙasa. EFCC ta bayyana cewa, wannan mataki na…
Read More
Gidauniyar Kannywood ta taya jaruma Aina’u Ade murnar naɗin da gwamnatin Kano ta yi mata

Gidauniyar Kannywood ta taya jaruma Aina’u Ade murnar naɗin da gwamnatin Kano ta yi mata

Daga AISHA ASAS  Gidauniyar Kannywood ta bayyana farin cikinta tare da taya Aina’u Ade murna bisa naɗin da Mai Girma Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya yi mata a matsayin Mai Ba da Shawara ta Musamman kan Harkokin Kannywood. A cikin wata sanarwa da Gidauniyar ta fitar, ta bayyana cewa nadin ya kasance ɗora ƙwarya a mazaunin ta, la’akari da shekaru na gogewa, ƙwazo da kuma manyan gudunmawar da Aina’u Ade ta bayar wajen bunƙasa da haɓaka masana’antar shirya fina-finai ta Kannywood. Gidauniyar ta jaddada cewa Aina’a Ade ta kasance ɗaya daga cikin fitattun matan da suka yi…
Read More
Rashin tsaro barazana ce ga tattalin arzikin Arewa — NYEEF

Rashin tsaro barazana ce ga tattalin arzikin Arewa — NYEEF

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Kungiyar ƙarfafa Matasan Arewa da Wayar Musu da Kai, wato Northern Youth Empowerment & Enlightenment Forum (NYEEF), ta fitar da wata muhimmiyar sanarwar manufofi bayan kammala Taron Tattaunawa na Shekara karo na uku da ta gudanar a watan Janairun 2026 a jihar Kaduna. Taron, wanda aka shirya domin karrama marigayi Alhaji Suleiman Abubakar Uban Doman Gudu, tsohon Daraktan Harkokin Sarauta na ƙungiyar, ya haɗa manyan malamai, shugabannin addini, kwararrun harkokin tsaro, masu tsara manufofi, shugabannin matasa da kuma ‘yan jarida domin nazarin manyan matsalolin da ke addabar Arewacin Nijeriya da ma kasa baki ɗaya. A sanarwar…
Read More
Kungiyar KAPAG ta ziyarci shugaban ƙaramar hukumar Tarauni

Kungiyar KAPAG ta ziyarci shugaban ƙaramar hukumar Tarauni

Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano Kungiyar KAPAG ƙarƙashin jagorancin Hajiya Balaraba Ibrahim ta kai ziyarar girmamawa ga shugaban ƙaramar Hukumar Tarauni, Hon. Sekure, a sakatariyar ƙaramar hukumar a ranar Litinin. Hajiya Balaraba ta bayyana cewa dawowar Gwamnan Jihar Kano, Injiniya Abba Kabir Yusuf, jam’iyyar APC wani muhimmin al’amari ne a tarihin siyasar jihar, tana mai cewa siyasa tafiya ce ta haɗin kai duk da sauye-sauyen jam’iyyu da ake samu lokaci zuwa lokaci. Ta ce, a matsayinsu na ƙungiya da ta dade tana aiki tun daga tushe sama da shekaru 25, sun ga dacewar su mara wa duk wanda ya dawo…
Read More
An gudanar da taron addu’o’i na musamman domin neman ƙarin zaman lafiya a Kano

An gudanar da taron addu’o’i na musamman domin neman ƙarin zaman lafiya a Kano

Daga DAUDA USMAN Wani matashi kuma ɗan kasuwa a Kano, Alhaji Salisu Haruna, mazaunin garin Jajirawa da ke ƙaramar Hukumar Kiru a Jihar Kano, ya jagoranci gudanar da taron addu’o’i na musamman domin neman ƙarin zaman lafiya a jihar Kano da kuma ƙasa baki ɗaya. Taron ya samu halartar malamai, magabata, da ɗumbin al’ummar garin Jajirawa da Kiru, har ma da wasu daga sassan jihar Kano. An gudanar da taron ne a harabar Masallacin Juma’a na garin Jajirawa a ranar Asabar da ta gabata. Daga cikin iyayen taron akwai Mai Martaba Dagacin garin Bargone, Alhaji Abdullahi Muhammad, da Mai Unguwar…
Read More
Ƙungiyar Dillalan Ma’adinai ta Kebbi ta kai ziyarar girmamawa ga sabon Shugaban Hukumar Ma’adanai

Ƙungiyar Dillalan Ma’adinai ta Kebbi ta kai ziyarar girmamawa ga sabon Shugaban Hukumar Ma’adanai

Daga JAMIL GULMA a Kebbi Ƙungiyar Masu Haƙa da Sarrafa Ma’adinai a Jihar Kebbi, ƙarƙashin jagorancin Alhaji Ahmad Yusuf, ta kai ziyarar girmamawa ga sabon shugaban Hukumar Kula da Harkokin Ma’adinai ta Jihar Kebbi, Honarabul Buhari Abdullahi Warrah. A jawabin da ya gabatar yayin ziyarar, shugaban ƙungiyar ya bayyana aniyar mambobinsu na bai wa hukumar cikakken goyon baya tare da kiyaye dokoki da ƙa’idojin da aka shimfiɗa domin tafiyar da ayyukan ma’adinai a jihar. Ya ce ƙungiyar na da burin yin aiki kafaɗa da kafaɗa da hukumar domin tabbatar da gaskiya, tsari da kuma ci gaba mai ɗorewa a fannin.…
Read More