Gidauniyar Kannywood ta taya jaruma Aina’u Ade murnar naɗin da gwamnatin Kano ta yi mata

Spread the love

Daga AISHA ASAS 

Gidauniyar Kannywood ta bayyana farin cikinta tare da taya Aina’u Ade murna bisa naɗin da Mai Girma Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya yi mata a matsayin Mai Ba da Shawara ta Musamman kan Harkokin Kannywood.

A cikin wata sanarwa da Gidauniyar ta fitar, ta bayyana cewa nadin ya kasance ɗora ƙwarya a mazaunin ta, la’akari da shekaru na gogewa, ƙwazo da kuma manyan gudunmawar da Aina’u Ade ta bayar wajen bunƙasa da haɓaka masana’antar shirya fina-finai ta Kannywood. Gidauniyar ta jaddada cewa Aina’a Ade ta kasance ɗaya daga cikin fitattun matan da suka yi tasiri a fagen nishaɗi da al’adu, inda ta taka rawar gani wajen ƙarfafa martabar Kannywood a ciki da wajen Jihar Kano.

Sanarwar ta kuma nuna cewa naɗin ya zo a daidai lokacin da ya dace, musamman duba da rawar da mata ke takawa a harkokin mulki da hidimar jama’a. A cewar Gidauniyar, shigar mata masu basira da kwarewa cikin tsarin gwamnati na taimaka wa wajen samar da ra’ayoyi masu faɗi da tsare-tsaren da suka shafi ci gaban al’umma baki ɗaya.

Gidauniyar Kannywood ta bayyana cikakkiyar ƙwarin gwiwa a kan cewa Aina’u Ade za ta bayar da gudunmawa mai ma’ana wajen ci gaba da ɗaukaka Kannywood, tare da ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin gwamnatin jihar da masu ruwa da tsaki a masana’antar fina-finai, ciki har da ’yan wasa, daraktoci, masu shirya fina-finai da ƙungiyoyin ƙwararru.

A ƙarshe, Gidauniyar ta yi mata fatan nasara da aiki mai armashi a sabon muƙaminta, tare da fatan wannan dama za ta zama wata babbar kafa ta kawo sauye-sauye masu ɗorewa ga Kannywood da matasan da ke dogaro da ita.

By ukarofi