Daga AISHA ASAS
Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa ta ƙasa (EFCC) ta kama fitacciyar jarumar Kannywood, Samha Inuwa, bisa zargin wulaƙanta kuɗin Najeriya, bayan bazuwar wani bidiyo da ke nuna tana amfani da takardun Naira wajen share majina daga hancinta. Bidiyon ya yaɗu cikin sauri a kafafen sada zumunta, inda jama’a suka rarrabu tsakanin masu kira da a hukunta ta da masu ganin a bi doka cikin natsuwa.
Masana doka sun jaddada cewa, wulaƙanta Naira ba karamin laifi ba ne, kasancewar kuɗin ƙasa alama ce ta ’yancin kai da mutuncin ƙasa. EFCC ta bayyana cewa, wannan mataki na cikin ƙoƙarinta na daƙile wulaƙanta kuɗin ƙasa, musamman a bidiyoyi da bukukuwa da ke yaɗuwa a yanar gizo.
Hukumar ta ce, ana tsare da jarumar a Kano yayin da ake ci gaba da bincike, kuma za a gurfanar da ita gaban kotu bayan kammala binciken. Lamarin na iya zama darasi ga fitattun mutane da ke raina dokokin kuɗin ƙasa.
