ukarofi

12654 Posts
Mai Kaltungo ya kai ziyarar godiya ga Sarkin Haɗeja

Mai Kaltungo ya kai ziyarar godiya ga Sarkin Haɗeja

Daga  RABIU SANUSI a Kano Uban ƙasa Mai Martaba Injiniya Saleh Muhammad Umar, (Mai Kaltungo) tare da wata tawaga mai ƙarfi daga Masarautar Kaltungo, sun kai ziyarar girmamawa da godiya zuwa Fadar Sarkin Haɗeja a Jihar Jigawa, HRH Dr. Adamu Abubakar Maje Shugaban Majalisar Sarakunan Jihar Jigawa. Tawagar ta kunshi manyan hakiman Masarautar Kaltungo, ciki har da Magayakin Kaltungo wanda shi ne Shugaban Kwamitin Shirye-shiryen Bikin Baje Kolin Al’adun Masarautar Kaltungo na shekarar 2025, Madugun Kaltungo, Sa’in Kaltungo, Cikasoron Kaltungo, Sarkin Rafin Kaltungo, Jarumar Kaltungo, Malafan Kaltungo, da sauran manyan fadawa. Ziyarar ta biyo bayan amsa gayyatar da Sarkin Hadejia…
Read More
Shugaban KAROTA ya nemi haɗin kan jama’a don inganta tsarin zirga-zirga a Kano

Shugaban KAROTA ya nemi haɗin kan jama’a don inganta tsarin zirga-zirga a Kano

Daga RABIU SANUSI a Kano Darakta Janar na Hukumar Kula da Zirga-zirgar Ababen Hawa ta Jihar Kano (KAROTA) Injiniya Faisal Mahmud ya yi kira ga al’ummar jihar da su ba hukumar cikakken haɗin kai domin ta samu damar aiwatar da ayyukanta yadda ya kamata wajen tabbatar da tsari da tsaro a kan hanyoyi. Injiniya Faisal Mahmud ya bayyana hakan ne yayin wata ganawa da manema labarai a ofishinsa da ke Kano, inda ya jaddada ƙudirin KAROTA na kare rayuka da dukiyoyin jama’a ta hanyar tabbatar da bin dokokin zirga-zirga a faɗin jihar. Ya ce haɗin kan direbobi, masu motocin haya…
Read More
Matashi ya kashe kishiyar kakarsa a Filato

Matashi ya kashe kishiyar kakarsa a Filato

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Ana zargin wani matashi mai shekaru 20, Ibrahim Mutari da hallaka abokiyar zaman kakarsa ta ɓangaren mahaifinsa, Hauwa Abubakar mai shekaru 70. Manhaja ta ruwaito cewa, lamarin da ya faru da misalin ƙarfe 3:00 na ranar Lahadin da ta gabata ya auku ne a garin Yanbula da ke ƙaramar Hukumar Jos ta Arewa Jihar Filato. Mahaifin matashin da ake zargi, Abubakar Shuaibu, ya yi Allah-wadai da kisan yana mai bayyana aukuwar lamarin a matsayin muguwar nifaƙa. Ya yi zargin cewa ɗan nasa ya kashe masa mata bayan maƙure mata wuya sannan ya soka mata…
Read More
ICPC ta tsare tsohon shugaban NIMASA, Bashir Jamoh

ICPC ta tsare tsohon shugaban NIMASA, Bashir Jamoh

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Jami’an Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa ta ICPC sun tsare tsohon shugaban Hukumar Kula da Harkokin Ruwa da Tsaro ta Nijeriya (NIMASA), Bashir Jamoh. Majiyoyi masu inganci sun shaida wa Manhaja cewa Bashir, wanda ya jagoranci hukumar daga 2020 zuwa 2023, har yanzu yana tsare a hannun hukumar a lokacin da ake rubuta wannan rahoto. ɗaya daga cikin majiyoyin ya ce an kama tsohon shugaban na NIMASA ne bayan ya gaza amsa gayyatar da hukumar ta yi masa sau da dama, bayan korafe-korafe da aka shigar a kansa. A cewar majiyar, ɗaya…
Read More
Wani riƙaƙƙen ɗan daba ya faɗa komar ’yan sanda a Kano

Wani riƙaƙƙen ɗan daba ya faɗa komar ’yan sanda a Kano

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Rundunar ‘yan sandan Jihar Kano ta kama wani riƙaƙƙen ɗan daba mai suna Auwalu Ali, wanda aka fi sani da Auwalu ɗan Daba, a unguwar ɗorayi da ke birnin Kano, bisa zargin jagoranci da shirya ayyukan daba da yi wa jama’a fashi da makami. Hakan na ƙunshe cikin wata sanarwa da rundunar ta fitar ta hannun mai magana da yawunta, CSP Abdullahi Haruna Kiyawa. Sanarwar da rundunar ta fitar ta ce an kama Auwalu mai shekaru 26 ne ranar 31 ga watan Janairun 2026, bayan samun sahihan bayanan sirri. Kiyawa ya ce jami’an ‘yan…
Read More
Muna kiran likitoci ’yan Kano da ke aiki a jihohi maƙwabta da su dawo gida – Gwamna Yusuf

Muna kiran likitoci ’yan Kano da ke aiki a jihohi maƙwabta da su dawo gida – Gwamna Yusuf

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Gwamnatin Kano ta sanar da cewa ta tanadi aiki kai tsaye ga duk wasu likitoci ’yan asalin jihar da ke aiki a wasu jihohi maƙwabta, a wani mataki na ƙara ƙarfafa harkokin kiwon lafiya a asibitocin gwamnati da ke faɗin jihar. Gwamna Abba Kabir Yusuf ne ya bayar da wannan amincewar, kamar yadda wata sanarwa da Hukumar Kula da Asibitocin Kano ta fitar ta bayyana. Sanarwar ta ce gwamnatin tana kira ga duk likitocin ’yan Kano da ke aiki a waje da su dawo gida domin karɓar aiki a asibitocin jihar, da zummar cike…
Read More
Yadda APC ta saka tsohon shugabanta, Abdullahi Adamu cikin kwamitin babban taronta

Yadda APC ta saka tsohon shugabanta, Abdullahi Adamu cikin kwamitin babban taronta

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Jam’iyyar APC mai mulkin Nijeriya ta ɗauki mataki domin magance jita-jitar rikici da sauya sheƙa a cikin ta, bayan sake saka tsohon Shugaban Jam’iyyar na ƙasa, Sanata Abdullahi Adamu, a shirye-shiryen babban taron ƙasa na jam’iyyar da za a yi a shekarar 2026. Jam’iyyar ta bayyana kwamitin mutum 73 da zai jagoranci shirye-shiryen taron, inda aka saka sunan Adamu a cikin jerin mambobin kwamitin.  Wannan mataki ya jawo hankalin masu bibiyar siyasa, duba da raɗe-raɗin da suka daɗe suna yawo kan makomarsa a siyasa. Dawowar Adamu na da muhimmanci matuƙa, musamman ganin cewa a shekarar 2023…
Read More
’Yan kasuwar fetur sun yi gargaɗin yiwuwar tashin farashi zuwa N1,000

’Yan kasuwar fetur sun yi gargaɗin yiwuwar tashin farashi zuwa N1,000

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Masu sana’ar sayar da man fetur a faɗin Nijeriya sun bayyana damuwarsu kan sabon ƙarin farashin mai, suna cewa lamarin na matuƙar takura harkokinsu yayin da ƙarfin jari ke raguwa kuma buƙatar man daga masu saye ke ƙara raguwa. 'Yan kasuwar sun ce ƙarin farashi ya rage musu ikon sake sayo kaya, lamarin da ya sa wasu daga cikinsu ke haɗawa da juna domin tara kuɗin da za su iya sayen sabon man fetur. A cewarsu, wannan yanayi na nuna yadda kasuwancin ke shiga wani hali na matsin lamba mai tsanani. Sun kuma bayyana cewa yawan…
Read More
Nijeriya na tunkarar kai wa mai tattalin arzikin Dala tiriliyan ɗaya – Idris

Nijeriya na tunkarar kai wa mai tattalin arzikin Dala tiriliyan ɗaya – Idris

Daga MAHDI MUSA MUHAMAMD Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai na Nijeriya, Mohammed Idris, ya bayyana cewa matakan gyaran tattalin arziki masu ƙarfin gaske da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya fara tun shekarar 2023 sun fara kai Nijeriya kan hanyar ci gaba, duk da ƙalubale da suka taso a farkon aiwatar da su. Ministan ya bayyana hakan ne yayin da yake gabatar da lakca ta bikin yaye ɗalibai karo na 34 a Jami’ar Fasaha ta Tarayya da ke Minna, Jihar Neja. Taken lakcar shi ne: “Matasa da Gina ƙasa: Cin Gajiyar Zamanin Sauye-sauyen ƙasa.” Idris ya ce, sauye-sauyen da…
Read More
Gwamnatin Tarayya ta bai wa ’yan Nijeriya wa’adi kan sabuwar dokar haraji

Gwamnatin Tarayya ta bai wa ’yan Nijeriya wa’adi kan sabuwar dokar haraji

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Fadar Shugaban ƙasa ta yi kira ga dukkan ’yan Nijeriya, ɗaiɗaikun mutane da kuma masu ɗaukar ma’aikata, da su tabbatar sun cika ƙa’idojin doka ta hanyar miƙa takardun bayanan harajinsu na shekara kafin ko a ranar 31 ga Maris, tana mai gargaɗin cewa rashin bin doka a fannin haraji na ci gaba da zama babbar matsala ga tsarin tattalin arzikin ƙasar. Shugaban Kwamitin Shugaban ƙasa kan Manufofin Kuɗi da Gyaran Haraji, Taiwo Oyedele, ne ya bayyana hakan yayin wani taron yanar gizo da aka shirya domin jami’an kula da albarkatun ma’aikata, masu kula da albashi, manyan…
Read More