ukarofi

12654 Posts
Zargin juyin mulki: Manyan shugabannin Nijeriya da aka shirya kamawa ko kashewa

Zargin juyin mulki: Manyan shugabannin Nijeriya da aka shirya kamawa ko kashewa

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Hedikwatar Tsaron Nijeriya (DHƙ) ta tabbatar da cewa binciken da aka kammala kan wasu jami’an soji ya gano zarge-zargen shirin kifar da gwamnatin farar hula, lamarin da ya sake tayar da muhawara kan tsaron dimokuraɗiyyar Nijeriya. Bayanin ya biyo bayan rahotannin da suka daɗe suna yawo cewa wasu jami’ai sun riƙa gudanar da taruka a asirce domin tsara yadda za a hambarar da gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu. A cewar DHƙ, binciken da aka gudanar bisa ƙa’idojin soja ya gano cewa wasu daga cikin jami’an da aka kama tun a bara na da tambayoyin da za…
Read More
Cacar-baki ta kaure da Ndume a Majalisar Wakilai kan sahihancin sabbin dokokin haraji

Cacar-baki ta kaure da Ndume a Majalisar Wakilai kan sahihancin sabbin dokokin haraji

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Wata sabuwar taƙaddama ta ɓarke a tsakanin Sanata Ali Ndume mai wakiltar Borno ta Kudu da Majalisar Wakilai, lamarin da ya sake jawo hankali kan batun gaskiya da bin ƙa’ida a harkokin dokokin ƙasa. Rigimar ta kunno kai ne bayan zargin akwai bambanci tsakanin sigar dokokin haraji da Majalisar Dokoki ta amince da su da kuma wadda aka ce Shugaban ƙasa ya rattaba wa hannu. Rahotanni sun nuna cewa saɓanin ya ɗauki sabon salo ne bayan Mataimakin Kakakin Majalisar Wakilai, Philip Agbese, ya zargi Sanata Ndume da yaɗa ruɗani ta hanyar iƙirarin cewa an sauya wasu…
Read More
Bello Turji ya sako ɗan bindigar da ya jagoranci sulhu a Katsina

Bello Turji ya sako ɗan bindigar da ya jagoranci sulhu a Katsina

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Kasurgumin ɗan bindiga, Bello Turji, ya sako jagoran ’yan bindiga da ya jagoranci sulhu da al’ummomin Jihar Katsina, Abdu Lankai. Bayan Turji ya kama Abdu Lanaki da kwanaki biyar ne ya sako shi bayan sanya bakin wasu shugabannin Fulani. Manhaja ta samu rahoto cewa a yammacin ranar Litinin magoya bayan Lankai suka, suka tarbe shi a bisa babura. Abdu Lankai ya fada tarkon su Turji ne a ranar Larabar satin da ya gabata bayan wata gayyata da suka yi mashi da sunan yadda za a yi sasanci a yankin Zamfara inda shi Turji yake…
Read More
Juyin mulkin da aka yi yunƙurin yi an shirya shi ne tun kafin rantsar da Tinubu – Ministan tsaro

Juyin mulkin da aka yi yunƙurin yi an shirya shi ne tun kafin rantsar da Tinubu – Ministan tsaro

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Ministan Tsaro, Janar Christopher Musa mai ritaya, ya bayyana cewa an fara shirya juyin mulki a Nijeriya tun kafin rantsar da Shugaba Bola Ahmed Tinubu a ranar 29 ga Mayu, 2023. Musa ya bayyana hakan ne yayin wata hira da aka yi da shi a shirin Sunday Politics na tashar Channels Tɓ, inda ya ce mafi yawan wadanda ake zargi da hannu a shirin an kama su.  Ya ce lamarin ya samo asali ne daga wani kanar da ya fusata saboda rashin karin girma, wanda daga baya ya jawo wasu jami’ai da suka nuna…
Read More
Yadda ‘yan bindiga suka ƙone fadar Sarki da kashe mutane a Kwara

Yadda ‘yan bindiga suka ƙone fadar Sarki da kashe mutane a Kwara

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Al'ummar jihar Kwara a yankin Irepodun na zaman ɗarɗar sakamakon wani mummunan hari da 'yan bindiga suka kai inda suka halaka mutane da dama. Shugabannin yankin sun ce sama da mutum 30 aka kashe a harin na ranar Talata da 'yan bindiga suka kai a garin Woro ɗauke da muggan makamai suna harbi kan mai uwa da wabi. "An shaida muna cewa an ƙirga gawawwakin mutum 35 zuwa 45 duk da cewa ba mu tabbatar ba," kamar yadda Hon Sa'idu Baba Ahmed, ɗan majalisar jiha da ke wakiltar yankin a jihar Kwara ya shaida…
Read More
Arsenal na sa ran lashe Carabao Cup domin dawo da martabarta – Timber

Arsenal na sa ran lashe Carabao Cup domin dawo da martabarta – Timber

Jurrien Timber na ganin cewa lashe kofin Carabao Cup na iya zama wata hanya ta buɗe ƙofofin samun manyan nasarori ga Arsenal a wannan kakar ta bana. Kungiyar da Mikel Arteta ke jagoranta tana daf da kawo ƙarshen shekara shida ba tare da kofi ba, bayan da ta doke Chelsea a filin Emirates 1-0, kenan ta kai wasan ƙarshe da cin 4-2 gida da waje. Arsenal ta kare a mataki na biyu sau uku a teburin Premier League, sai dai a bana tana kan teburi da tazarar maki shida tsakani da Manchester City ta biyu - kuma ita ce ta…
Read More
Kante ya koma Fenerbahce daga Al-Ittihad

Kante ya koma Fenerbahce daga Al-Ittihad

Fenerbahce ta tabbatar da ɗaukar ɗan wasan tawagar Faransa, N'Golo Kante, daga Al-Ittihad mai buga babbar gasar tamaula ta Saudiyya. A ranar Talata, shirin ɗan wasan Faransan na komawa Turkiyya ya kusan rushewa, bayan Fenerbahce ta fitar da sanarwa tana zargin Al-Ittihad da haddasa kawo cikas a cinikin. Fenerbahce ta ce Al-Ittihad ta kasa cika takardun da ake buƙata don kammala kulla yarjejeniya daga ciki ɗan wasan tawagar Moroko, Youssef En-Nesyri ya koma Al-Ittihad. Sai dai a ranar Laraba, Fenerbahce ta tabbatar da cewa an warware matsalar da ke tsakaninsu, kuma Kante tsohon ɗan wasan Chelsea ya koma Turkiya, bayan…
Read More
Abokan hamayyarmu sun fi mu kashe kuɗi wajen sayen ’yan wasa – Guardiola

Abokan hamayyarmu sun fi mu kashe kuɗi wajen sayen ’yan wasa – Guardiola

Kocin Manchester City, Pep Guardiola, ya yi barkwanci yana mai cewa yana ɗan jin haushin ƙungiyarsa, saboda abokan hamayyarsu sun fi su kashe maƙudan kuɗi wajen cefane. Man City ce ta fi kashe kuɗi a kasuwar saye da sayar da ’yan ƙwallo da ta ci ta watse a watan Janairu, inda ta sayi Antoine Semenyo daga Bournemouth da Marc Guehi daga Crystal Palace kan kusan fam miliyan 84 gabaki ɗayansu. Sai dai Guardiola ya ce abokan hamayyarsa a gasar Premier League sun fi zuba jari mafi yawa. Idan har za a yi ƙididdigar cefane, Man City ta kashe sama da…
Read More
Ronaldo ya koma atisaye da Al Nassr bayan raɗe-raɗen saɓani da ƙungiyar

Ronaldo ya koma atisaye da Al Nassr bayan raɗe-raɗen saɓani da ƙungiyar

Fitaccen ɗan wasan ƙwallon ƙafa na Portugal, Cristiano Ronaldo, ya koma atisaye tare da ƙungiyar Al Nassr, lamarin da ya rage zazzafar jita-jitar da ta yaɗu cewa tauraron ya nuna rashin jin daɗi kan yadda ake tafiyar da jarin kulob ɗin idan aka kwatanta da sauran ƙungiyoyin da Asusun Zuba Jari na Saudiyya (PIF) ke marawa baya. Ronaldo, mai shekaru 40, ya kasance a tsakiyar muhawara a ’yan kwanakin nan bayan rahotanni sun ce yana tunanin barin Saudiyya sakamakon abin da ya ɗauka a matsayin banbanci wajen rabon tallafi tsakanin Al Nassr da manyan abokan hamayyarta kamar Al Hilal da…
Read More
Gwamnatin Katsina za ta ɗauki malaman lafiya da malaman firamare 4000

Gwamnatin Katsina za ta ɗauki malaman lafiya da malaman firamare 4000

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina A na sa ran nan ba da jimawa ba gwamnatin za ta fara fitar da wasiƙun ɗaukar aiki ga ma’aikatan lafiya sama da 1,000, tare da shirin ɗaukar ƙarin ma’aikata 2,000 domin magance ƙarancin ma’aikata a asibitoci da cibiyoyin kiwon lafiya na farko a sassan jihar. Gwamna Dikko Umaru Raɗɗa ya bayyana haka a yayin da yake sa ido kan aikin tantance ma’aikata da kwamiti na musamman da ke gudanar da tantance ma’aikatan gwamnati ke yi a ofishinsa. Ya ce ɗaukar ma’aikatan lafiyar na daga cikin muhimman ƙudurorin gwamnatinsa na tabbatar da ingantaccen tsarin kula…
Read More