ukarofi

12654 Posts
Gwamnatin Sakkwato ta rage aƙalla kashi 60 a farashin takin zamani ga manoman jihar

Gwamnatin Sakkwato ta rage aƙalla kashi 60 a farashin takin zamani ga manoman jihar

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Gwamnatin jihar Sakkwato ta ƙaddamar da sayar da takin zamani ga manoman jihar a farashi mai rahusa, wanda a cewar gwamnatin zai ba su damar gudanar da noman rani cikin sauƙi. Gwamnan jihar, Ahmed Aliyu ne ya ƙaddamar da rabon takin a ƙaramar hukumar Wurno ta jihar a ranar Laraba 4 ga watan Fabrairu, inda ya ce inganta harkokin noma na cikin manyan ƙudurorin gwamnatinsa. Gwamnan ya ce sun sayo tirela 52 na takin Urea da tirela 50 na NPK, kuma za a raba su ne ga ƙananan hukumomin jihar guda 23. "Kowace ƙaramar…
Read More
HJRBDA ta horar da matasa 2,000 kan noman zamani, ta ƙaddamar da cibiyoyin horarwa

HJRBDA ta horar da matasa 2,000 kan noman zamani, ta ƙaddamar da cibiyoyin horarwa

Daga SULAIMAN HUSSAINI D/KUDU a Kano A wani mataki na bunƙasa harkokin noma da samar wa matasa aikin yi domin su dogara da kansu tare da ƙara wadatar abinci a ƙasar nan, Hukumar Raya Kogunan Hadeja-Jama’are (HJRBDA) ta horar da matasa maza da mata 2,000 kan dabarun noma na zamani. Shirin horon ya haɗa da raba matasan gida huɗu, inda aka horar da matasan 500 kan noman ban-ruwa ta ƙasa, yayin da wasu 500 aka koya musu yadda ake noma ta hanyar Green House. Haka kuma, an horas da wasu 500 kan dabarun noman gida ta amfani da buhu ko…
Read More
Amurka ta tabbatar da tura sojojinta zuwa Nijeriya

Amurka ta tabbatar da tura sojojinta zuwa Nijeriya

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Kasar Amurka ta ce tura wata karamar rundunar sojoji zuwa Nijeriya bayan sabuwar yarjejeniyar haɗin gwiwar tsaro da ta kulla tsakaninta da Nijeriyar. Kwamandan da ke jagorantar rundunar Amurka a nahiyar Afirka (AFRICOM), Janar Dagvin Anderson ne ya bayyana hakan a taron manema labarai da aka gudanar a ranar Talata. Wannan shi ne karo na farko da aka tabbatar da kasancewar sojojin kasa na Amurka a cikin Nijeriya tun lokacin da gwamnatin Donald Trump ta kaddamar da hare-haren makami mai linzami kan ’yan ta’adda a jihar Sakkwato a ranar Kirsimeti. Anderson ya ce matakin…
Read More
Hon. Jibga da Sa’in Kano sun jagoranci bikin cika shekaru 30 da kafuwar ƙaramar Hukumar Makoɗa

Hon. Jibga da Sa’in Kano sun jagoranci bikin cika shekaru 30 da kafuwar ƙaramar Hukumar Makoɗa

Daga MUHAMMADU MUJITABA a Kano Shugaban ƙaramar Hukumar Makoda, Hon. Alhaji Isah Jibga, tare da Sa’in Kano kuma Hakimin Makoda, Arc. Alhaji Ali Mukhtar, sun jagoranci bikin cika shekaru 30 da kafuwar ƙaramar Hukumar Makoda, wadda aka kirkira a shekarar 1996 daga tsohuwar ƙaramar Hukumar Danbatta. An gudanar da bikin ne a harabar fadar Masarautar Makoda a makon da ya gabata, inda manyan baki, shugabannin siyasa, sarakunan gargajiya, malamai da al’ummar yankin suka halarta domin tunawa da gagarumar gwagwarmayar da aka yi har aka samu kafuwar ƙaramar hukumar. Tun da farko a jawabinsa, Hon. Alhaji Isah Jibga ya bayyana ranar…
Read More
Masu ruwa da tsaki na APC a Dawakin Tofa sun tattauna hanyar kawo cigaban ƙaramar hukumar

Masu ruwa da tsaki na APC a Dawakin Tofa sun tattauna hanyar kawo cigaban ƙaramar hukumar

Daga RABIU SANUSI a Kano  Masu ruwa da tsaki na jam’iyyar APC a karamar hukumar Dawakin Tofa sun gudanar da taro na musamman da yammacin ranar Litinin, domin tattauna muhimman batutuwa da za su taimaka wajen bunkasa cigaba da hadin kai a karamar hukumar. Taron wanda ya samu halartar manyan jagorori da jiga-jigan jam’iyyar daga matakai daban-daban.  Daga cikin mahalarta akwai Babban Daraktan Yada Labarai na Gwamnatin Jihar Kano, Alhaji Sanusi Bature D-Tofa. Sauran wadanda suka halarta sun hada da Shugaban Karamar Hukumar Dawakin Tofa, Alhaji Adamu Shehu Bello Danmaliki,tsohon dan takarar Majalisar Tarayya a jam’iyyar APC a zaben 2023,…
Read More
Gina Port Golf: Matasa da dama sun samu aikin yi a Kano – Fahad Muhammad

Gina Port Golf: Matasa da dama sun samu aikin yi a Kano – Fahad Muhammad

Daga MUHAMMADU MUJITABA a Kano Masaukin baƙi na Port Golf da ake ginawa a birnin Kano ya samar da ayyukan yi ga matasa da dama, kamar yadda Fahad Muhammad, jami’in kula da ma’aikata da kayan aiki na Port Golf, ya bayyana a madadin Babban Manajan wurin, GM Oliver Jonathan. Fahad Muhammad ya bayyana hakan ne a ranar Talata da ta gabata, inda ya ce aikin gina Port Golf ya bai wa matasa da dama damar samun aikin yi kai tsaye da kuma na wucin gadi, wanda hakan ke taimakawa wajen rage zaman banza da inganta tattalin arzikin matasa a jihar.…
Read More
Kulafa’ur Rashidin Islamiyya ta yaye ɗalibai 167 a karo na 22

Kulafa’ur Rashidin Islamiyya ta yaye ɗalibai 167 a karo na 22

Daga SULAIMAN HUSSAINI D/KUDU a Kano Makarantar Kulafa’ur Rashidin Islamiyya da ke Hausawa Sabon Titi a Jihar Kano ta gudanar da bikin saukar karatun Alƙur’ani mai girma na dalibai 167 karo na 22, wanda aka yi a filin makarantar firamare ta Ado Gwaram. Da yake jawabi a wajen bikin, Shugaban makarantar Malam Auwalu Umar Ahmad ya bayyana cewa makarantar na samun gagarumar nasara idan aka kwatanta da shekarun baya, musamman wajen yawan daliban da ke sauka duk shekara. Sai dai ya bayyana cewa makarantar na fuskantar ƙalubale da suka haɗa da rashin isasshen wajen zama da kuma rashin wadatattun bandakuna.…
Read More
Shigar Gwamna Abba APC babbar nasara ce – Hon. Nasiru Matage

Shigar Gwamna Abba APC babbar nasara ce – Hon. Nasiru Matage

Daga SULAIMAN HUSSAINI D/KUDU a Kano Tsohon Shugaban ƙaramar Hukumar Dawakin Kudu, Hon. Nasiru Ibrahim Matage, ya bayyana shigar Gwamnan Jihar Kano Abba Kabir Yusuf cikin Jam’iyyar APC a matsayin babbar nasara ga jihar. Hon. Matage ya bayyana hakan ne yayin zantawa da manema labarai a gidansa da ke garin Matage, bayan karɓar Shugaban ƙaramar Hukumar Dawakin Kudu, Hon. Sani Ahmad Mai Rago, wanda shi ma ya shiga jam’iyyar APC. Ya ce dawowar gwamnan cikin APC zai ƙarfafa haɗin kai a jam’iyyar tare da buɗe ƙofofin samun ayyukan ci gaba daga gwamnatin tarayya. Hon. Matage ya shawarci masu neman mukaman…
Read More
Soyayyar Annabi ce ke ba ni ƙwarin gwiwar shirya mauludi duk shekara – Sunusi Dawaki

Soyayyar Annabi ce ke ba ni ƙwarin gwiwar shirya mauludi duk shekara – Sunusi Dawaki

Daga SULEIMAN HUSSAINI D/KUDU a Kano Alhaji Sunusi Aminu Abubakar Dawaki ya bayyana cewa soyayya da ƙaunar Annabi Muhammad (SAW) ce ke ba shi ƙwarin gwiwar shirya bikin Mauludi duk shekara. Ya bayyana hakan ne yayin ganawa da manema labarai a gidansa a lokacin gudanar da Mauludin karo na biyu. Ya ce duk wanda ya himmatu wajen hidimtawa Annabi Muhammad (SAW), Allah zai albarkaci dukiyarsa da rayuwarsa. Ya ƙara da cewa duk lokacin da ya shirya gudanar da Mauludi, Allah na buɗe masa hanyoyin samun nasara ba tare da neman tallafi daga kowa ba. Ya yi kira ga mahalarta bikin…
Read More
Nijeriya ta tabbatar da zuwan sojojin Amurka ƙasar

Nijeriya ta tabbatar da zuwan sojojin Amurka ƙasar

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Ministan tsaron Nijeriya, Janar Christopher Musa, ya tabbatar wa BBC cewa wata ƙaramar tawagar sojojin Amurka tana aiki a cikin ƙasar. Ya ce sojojin na Amurka za su kasance suna bayar da horo ga sojojin Nijeriya domin shiryasu wajen gudanar da ayyuka. Ministan bai bayyana yawan sojojin ba, ko lokacin da suka isa ƙasar, ko inda aka jibge su, ko tsawon lokacin da za su zauna a Nijeriya ba. Sojojin Amurka da na Nijeriya sun shafe shekaru masu yawa suna gudanar da bayar da horo na haɗin gwiwa, da nufin ƙarfafa ƙwarewar Nijeriya a…
Read More