06
Feb
Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Kungiyar Matasan Nijeriya (NYCN), reshen ƙaramar Hukumar Giwa a Jihar Kaduna ta yaba wa gwamnatin jihar ƙarƙashin jagorancin Gwamna Sanata Uba Sani bisa ƙoƙarin da take yi wajen bunƙasa harkokin ci gaba da walwalar al’umma a sassa daban-daban na jihar. Shugaban ƙungiyar na ƙaramar hukumar, Kwamared Nuhu Haruna Sani, wanda aka fi sani da Alkurkawee, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ga manema labarai, inda ya ce matasan Giwa na jin daɗin yadda gwamnatin jihar ke aiwatar da manufofin raya kasa musamman a fannin tsaro, ilimi da bunƙasa tattalin arzikin…
