ukarofi

12654 Posts
Gwamnonin Arewa sun buƙaci ɗauki tsauraran matakai kan kashe-kashen yankin

Gwamnonin Arewa sun buƙaci ɗauki tsauraran matakai kan kashe-kashen yankin

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Kungiyar Gwamnonin Jihohi ta Arewa (NSGF) ta yi kakkausar suka kan sabbin hare-haren ta’addanci da suka janyo asarar rayuka a wasu sassan jihohin Kwara, Katsina da Benuwe, inda ta bayyana lamarin a matsayin dabbanci da kuma barazana ga zaman lafiyar ƙasa baki ɗaya. Shugaban ƙungiyar kuma Gwamnan Jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, ne ya bayyana haka a cikin wata sanarwa, yana mai nuna matuƙar baƙin ciki kan yadda ake ci gaba da kai hare-hare kan fararen hula marasa laifi. Hakan na zuwa ne bayan rahotannin hare-hare a garuruwan Woro da Nuku a ƙaramar Hukumar Kaiama ta…
Read More
An kai hari kurkukun Kangiwa

An kai hari kurkukun Kangiwa

Daga JAMIL GULMA a Kebbi  Ranar Talatar da ta gabata waɗansu mutane ɗauke da makamai kan babura da ake kyautata zaton masu garkuwa da mutane ne sun kai hari gidan gyaran hali da ke garin Kangiwa da ke jihar Kebbi. Wani mazauni garin Kangiwa Malam Yusuf Aliyu ya bayyanawa wakilin mu da cewa lokacin da mutanen suka zo sun ƙwace babur hannun wani mutum inda suka yi amfani da shi ta hanyar jingina babur ɗin jikin ƙofar shiga gidan suka cinna masa wuta ƙofar ta buɗe. Bayan sun samu shiga gidan suka ƙona motar hukumar daga baya jami'an tsaro suka…
Read More
Manoman Zariya sun koka kan ƙwace musu gonakin da sojoji suka yi

Manoman Zariya sun koka kan ƙwace musu gonakin da sojoji suka yi

Daga MOH BELLO HABIB a Zariya  Manoman rani dake Gyallesu da maƙwabtaka da Cibiyar Horas da Kuratan Sojoji (Depot Nigerian Army) dake Zariya cikin jihar Kaduna sun koka akan abin da suka kira zalunci da mahunta makarantar suka yi na gonakin da suka gada daga kakannin su sama da shekaru 150 da suka gabata. Da yake zantawa da manema labarai jim kaɗan bayan kammala sallah da adu'o'i na musamman da manoman suka gabatar don neman taimakon ya ƙwato masu gonakinsu kimanin 500 da sojoji suka yi tare da shigar cikin haraban barikinsu, mai magana da yawun manoman, Malam Musa Muhammad…
Read More
Gidauniyar Gwagware Musa ta yi ta’aziyar mutanen da ‘yan bindiga suka kashe a Doma

Gidauniyar Gwagware Musa ta yi ta’aziyar mutanen da ‘yan bindiga suka kashe a Doma

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Shugaban Gidauniyar kwamred Mannir Suleiman ya faɗi haka a wata takardar da ya fitar wanda aka rabawa manema labarai a Katsina. Ya ce mutuwar waɗannan bayin Allah ba ƙaramin asara bane ga al'ummar jihar Katsina har da ƙasa baki ɗaya. Ya ce gidauniyar ta nuna alhinin kan waɗannan mutane da basu ji ba basu gani kawai 'yan bindiga su buɗe masu wuta ba tare da dalili ba. Sun kashe masu ruwa da tsaki na garin tare da ƙona gidaje,kasuwanni makarantu da sauran muhimman wurare don rashin imani. Kwamred Suleiman yayi fatan Allah mayar masu da…
Read More
Kotu ta ɗaure tsohon shugaban NEXIM shekaru 490 kan badaƙalar kuɗi

Kotu ta ɗaure tsohon shugaban NEXIM shekaru 490 kan badaƙalar kuɗi

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Babbar Kotun Tarayya da ke zamanta a Abuja ta yanke hukuncin ɗaurin shekaru 490 ga tsohon Manajan Darakta na Bankin Fitar da Kaya da Shigo da Kaya na Nijeriya (NEXIM), Robert Orya, bayan samunsa da laifi a kan zarge-zargen badaƙala da suka kai kimanin Naira Biliyan 2.4. Alƙalin kotun, Mai shari’a F.E. Messiri, ne ya yanke hukuncin bayan ya tabbatar cewa masu ƙara sun gabatar da hujjoji gamsassu da suka tabbatar da laifuffuka 49 da suka shafi cin amanar ofis, haɗa baki da kuma karkatar da kuɗaɗen gwamnati. Kotun ta yanke masa hukuncin ɗaurin shekaru 10…
Read More
Sabuwar dokar zaɓe: Muhimman abubuwan da Majalisar Dattawa ta amincewa

Sabuwar dokar zaɓe: Muhimman abubuwan da Majalisar Dattawa ta amincewa

*Majalisar Wakilai ta kafa kwamitin daidaito Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Majalisar Dattawa ta Nijeriya ta zartar da dokar zaɓe ta 2022 da aka yi wa garambawul. An zartar da ƙudurin dokar ne bayan nazari da amincewa da sassa 155 da ke ƙunshe a cikin ta. ɗaya daga cikin gyare-gyaren da aka yi wa dokar ta 2022 shi ne rage wa’adin da Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta ƙasa (INEC) ke da shi na futar da sanarwar zaɓe daga 360 zuwa kwana 180. Hakan ya biyo bayan amincewa da ƙudirin da Sanata Tahir Monguno ya gabatar na rage kwanakin…
Read More
Kogunan Gusau ya bayyana sha’awarsa ta neman kujerar gwamnan Zamfara a APC

Kogunan Gusau ya bayyana sha’awarsa ta neman kujerar gwamnan Zamfara a APC

Daga SANUSI MUHAMMAD, a Gusau Alhaji Muktar Shehu Idris, wanda aka fi sani da Kogunan Gusau, wani jigo a jam'iyyar APC a jihar Zamfara, ya bayyana sha'awarsa ta tsayawa takarar kujerar gwamnan jihar Zamfara a karkashin jam'iyyar All Progressives Congress (APC) a shekarar 2027. Koguna ya bayyana hakan ne a lokacin da yake jawabi ga magoya bayansa a Gusau, babban birnin jihar. Duk da hukuncin kotun ƙoli da ya tabbatar da Bello Matawalle na PDP a matsayin wanda ya lashe zaɓen 2019, Alhaji Muktar Shehu Idris ya kasance fitaccen mutum a siyasar jihar Zamfara. Alhaji Muktar Shehu Idris ya yi…
Read More
Gwamnatin Tarayya na gab da miƙa tashar wutar lantarki ta Lambar Rimi ga gwamnatin Katsina

Gwamnatin Tarayya na gab da miƙa tashar wutar lantarki ta Lambar Rimi ga gwamnatin Katsina

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Tuni shugaban ƙasa Bola Tinubu ya tura jami'an ma'aikatan makamashi zuwa Katsina domin tattaunawa da takwarar su na jihar Katsina. Mai ba gwamna shawara kan makamashi da lantarki Dr Hafiz Ahmed ya faɗi haka a wata hira da manema labarai a ofishin sa da ke Katsina. Ya ce tuni jami'an sun kammala tattaunawa kuma sun miƙa rahoton su ga shugaban ƙasa wanda a ke jiran amincewar sa. Dr Hafiz ya bayyana cewa tun da hawa mulki na gwamnati, gwamna Dikko Raɗɗa ya ziyarci kasar Faransa inda ya sadu da kamfanin da suka fara aikin samar…
Read More
Alƙalancin gasar rubutu

Alƙalancin gasar rubutu

Daga KABIRU YUSUF FAGGE Bayan da na saurari bayanan wasu alƙalan gasannin rubuce-rubucen ƙagaggun labarai a mabambantan gasanni, na tsinkayi akwai abubuwan da za su amfani marubuta masu sha’awar shiga gasa don yin nasara. ɗabi’ar karatu Wannan a bayyane yake cewa, yanzu al’umma sun fi son su kalla ko su saurara fiye da karantawa. Idan haka ne, to kai marubuci kana da gagarumin ƙalubale rubuta labarin da zai sa alƙalan gasa ko suna so ko ba sa so za su karanta, wato ko ba don aikin da aka ba su na karanta labarin su yi alƙalanci ba, ko don salo…
Read More
Gwamnatin Katsina za ta sayi taransifoma guda 200

Gwamnatin Katsina za ta sayi taransifoma guda 200

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Bayanin zaman majalisar zartaswa ta Jihar Katsina na uku a wannan shekara ƙarƙashin jagorancin gwamna Dikko Raɗɗa ta amince da wannan. Haka kuma majalisar ta aminta da samar da na'urar wutar lantarki mai amfani da hasken rana (solar PV)mai ƙarfin 2MWH donin amfani da su a wasu ma'aikatu wanda hakan zai rage kuɗaɗen da ake kashewa wajan man fetur,da inganta ɗorewar samar da wutar lantarki a muhimman gine ginen gwamnati. Kamar yadda kwamishinan yaɗa labarai Dr Salisu Bala Zango ya ce a bayanin da ya faɗawa manema labarai, majalisar ta amince da tsarin shirin da…
Read More