Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Tuni shugaban ƙasa Bola Tinubu ya tura jami’an ma’aikatan makamashi zuwa Katsina domin tattaunawa da takwarar su na jihar Katsina.
Mai ba gwamna shawara kan makamashi da lantarki Dr Hafiz Ahmed ya faɗi haka a wata hira da manema labarai a ofishin sa da ke Katsina.
Ya ce tuni jami’an sun kammala tattaunawa kuma sun miƙa rahoton su ga shugaban ƙasa wanda a ke jiran amincewar sa.
Dr Hafiz ya bayyana cewa tun da hawa mulki na gwamnati, gwamna Dikko Raɗɗa ya ziyarci kasar Faransa inda ya sadu da kamfanin da suka fara aikin samar da wutar lantarki na Lambar Rimi domin gano matsalar da ke tattare da aikin.
Ya ce yanzu haka Gwamna Dikko Raɗɗa na shirin komawa ƙasar Faransa a karo na uku domin dawo da kamfanin su cigaba da aikin samar da wutar lantarkin.
Aikin wutar lantarki na Lambar Rimi da aka fara tun lokacin da marigayi tsohon shugaban ƙasa Umaru Musa Yar’adua yana gwamnan Katsina shekara 17 da suka wuce ya ci karo da cikas sakamakon sace ɗaya daga cikin ma’aikatan kamfanin da suka fara aikin a Lambar Rimi.
Dr Hafiz ya kuma sanar da cewa Gwamna Raɗɗa ya ƙara samar da wutar lantarki (10 MW) mai amfani da hasken rana da injinan Transformer guda 200 damin al’ummar.
Ya ce jihar Katsina ita tafi jihohin Jigawa da Kano zuba jari na kashi 17 bisa ɗari a kamfanin samar da wutar lantarki na ƙasa.
Dr Hafiz ya bayyana cewa haƙƙin kamfanin samar da wutar lantarki ne su samar da Transformer ga al’ummar,amma duk da haka Gwamna domin kyautata wa al’ummar sa ya sayi waɗannan na’urar Transformer,sai dai dole gwamnati da haɗin gwiwar kamfanin za su biya kuɗin Transformer da gwamnatin ta saya.
Ya kuma bayyana cewa jihar Katsina na buƙatar (70MW)na wutar lantarki mai amfani da hasken rana,amma ya zuwa yanzu (30MW) kai gare ta amma ana sa rai kafin gwamna Dikko Raɗɗa ya kammala wa’adin na biyu idan Allah ya bashi nasara za ta cimma (70MW).
“Idan jihar Katsina ta sami wannan adadin ta samu wadataccen wutar lantarki mai amfani da hasken rana a jihar da zai sa muyi sallama da wutar lantarki na ƙasa.
Dangane da masu lalata kayayyakin wutar lantarkin mai amfani da hasken rana kuwa, Dr Hafiz ya sanar da cewa yanzu haka gwamnatin jihar ta aikewa majalisar dokoki na jihar buƙatar tanadar da dokokin da za su hukunta masu aikata wannan ɓarna kuma da zaran majalisar ta zartar da ƙudirin, gwamnati za ta fara aiwatar da hukuncin masu aikata wannan ɓarna.
