Kogunan Gusau ya bayyana sha’awarsa ta neman kujerar gwamnan Zamfara a APC

Spread the love

Daga SANUSI MUHAMMAD, a Gusau

Alhaji Muktar Shehu Idris, wanda aka fi sani da Kogunan Gusau, wani jigo a jam’iyyar APC a jihar Zamfara, ya bayyana sha’awarsa ta tsayawa takarar kujerar gwamnan jihar Zamfara a karkashin jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a shekarar 2027.

Koguna ya bayyana hakan ne a lokacin da yake jawabi ga magoya bayansa a Gusau, babban birnin jihar.

Duk da hukuncin kotun ƙoli da ya tabbatar da Bello Matawalle na PDP a matsayin wanda ya lashe zaɓen 2019, Alhaji Muktar Shehu Idris ya kasance fitaccen mutum a siyasar jihar Zamfara.

Alhaji Muktar Shehu Idris ya yi nuni da cewar bisa la’akari da goyon baya da kiraye kirayen da magoya bayansa suke masa tun farko a faɗin jihar, shi yasa ya aminta da ya fito don tsayawa takarar kujerar Gwamna a zaɓen 2027 ƙarƙashin jam’iyyar APC.

Ya buƙaci magoya bayansa da su kwantar da hankalinsu su kuma bi doka, yana mai jaddada muhimmancin haɗin kan dukkanin mambobin jam’iyyar APC da magoya bayan ta a jihar ta Zamfara.

Kogunan Gusau ya ƙara jaddada buƙatar magoya bayansa su girmama tsarin shugabancin jam’iyyar kuma su guji ayyukan da za su iya raba jam’iyyar ko ɓata mata suna. Yana mai jaddada muhimmancin zaman lafiya da bin doka wajen cimma ci gaba mai ma’ana a cikin mulkin dimokuraɗiyya.

Ya kuma ƙarfafa mutane su shiga cikin aikin yin rijistar katin zaɓe na ƙasa da kuma yin rijistar mambobin jam’iyyar ta APC, yana mai alƙawarin bin ƙa’idodi da kundin tsarin mulkin jam’iyyar ya tanada a ko yaushe don samun Nasarar Jam’iyyar a Jihar ta Zamfara.

Blueprint Manhaja ta tattaro cewa sanarwar Alhaji Muktar Shehu Idris ta nuna wani yunƙurin siyasa mai ƙarfi daka iya girgiza gwamnatin Jihar Zamfara yayin da zaɓen gwamna na 2027 ke gabatowa.

By ukarofi