ukarofi

12654 Posts
An gudanar da taron ƙarfafa ƙwarewa kan PPP ga Majalisar Zartarwar Jihar Katsina

An gudanar da taron ƙarfafa ƙwarewa kan PPP ga Majalisar Zartarwar Jihar Katsina

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Gwamnan Jihar Malam Dikko Raɗɗa ne ya ayyana buɗe taron horaswa na kwana guda da aka shirya wa yan majalisar zartarwa na jihar kan tsarin haɗin gwiwar gwamnati da masu zaman kansu (Public–Private Partnership – PPP) wanda hukumar bunƙasa zuba jari a jihar (KIPA) ke jagoranta. Taron dai na nufin ƙarfafa fahimtar manufofi a matakin shugabanci da kuma kulawa ta manyan jami’ai kan PPP a matsayin muhimmin kayan aiki wajen bunƙasa ababen more rayuwa, inganta ayyukan hidima, da samar da ci gaban tattalin arziki mai ɗorewa a jihar. Yayin da yake ayyana buɗe taron, Gwamna…
Read More
Gwamnatin Katsina ta jajanta wa al’ummar garin Doma, tare da alƙawarin ƙara tabbatar da tsaro

Gwamnatin Katsina ta jajanta wa al’ummar garin Doma, tare da alƙawarin ƙara tabbatar da tsaro

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Gwamnatin Jihar Katsina ta yi alƙawarin ƙara tsaurara matakan tsaro a garin Doma da ke ƙaramar hukumar Faskari, biyo bayan mummunan harin ’yan bindiga da ya yi sanadin mutuwar mutane fiye da 20 tare da lalata dukiyoyi masu yawa. Gwamna Malam Dikko Raɗɗa ya isar da wannan sakon ta hannun wata tawaga ta musamman ƙarƙashin jagorancin sakataren gwamnatin jihar, Barista Abdullahi Garba Faskari, yayin ziyarar jajantawa da tawagar ta kai wa al’ummar garin. Tawagar ta ƙunshi sakataren gwamnatin jihar, sakataren dindindin na ofishin SGS, mataimaki na musamman ga gwamna kan harkokin tsaro, kwamishinan ’yan sanda…
Read More
‘Yan takarar gwamnan APC a Nasarawa sun amince da Farfesa Haruna a matsayin shugaban su

‘Yan takarar gwamnan APC a Nasarawa sun amince da Farfesa Haruna a matsayin shugaban su

DAGA JOHN WADA a Keffi Duka 'yan takaran kujerar gwamnan jihar Nasarawa a inuwar jam'iyyar APC a zaɓen 2027 da ke tafe daga shiyar Yammacin jihar sun amince da Farfesa Injiniya Muhammad Sani Haruna a matsayin shugaban su. Shugaban jam'iyyar ta APC na karamar hukumar Keffi, Alhaji Mohammed Bello Soja ne ya sanar da haka a jawabin sa a wajen wani taron ƙaddamar da aikin gina wata babbar katanga irin na zamani da ake kira perimeter fencing a turance a makarantar yara na Abdu-Zanga da ke garin Keffi, wanda Farfesa Haruna ɗin ya ɗauki nauyin gudanarwa. Yace zaɓin Prof. Haruna…
Read More
‘Yan bindiga sun kashe mutum 21 a harin ramuwar gayya a Katsina

‘Yan bindiga sun kashe mutum 21 a harin ramuwar gayya a Katsina

Daga UMAR GARBA a Katsina Aƙalla mutum 21 ne suka mutu a wani hari da 'yan bindiga suka kai a yankin Tafoki da ke ƙaramar hukumar Faskari a jihar Katsina kamar yadda shugaban ƙaramar hukumar ya shaida wa manema labarai. A tattaunawar sa da BBC, shugaban ƙaramar hukumar, Surajo Aliyu Daudawa, ya ce 'yan bindigar sun kashe mutanen ne a matsayin ramuwar gayya bayan kashe wani nasu da aka yi a yankin duk da cewa an yi sulhu da su kusan watanni biyar da suka wuce. "Mazauna yankin sun wayi gari cikin tashin hankali bayan harin, duk da cewa kafin…
Read More
NAHCON ta kammala kama wa maniyyatan Nijeriya masaukai a Makka da Madina

NAHCON ta kammala kama wa maniyyatan Nijeriya masaukai a Makka da Madina

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Hukumar Alhazai ta ƙasa (NAHCON) ta kammala kama wa maniyyatan Nijeriya a Hajjin 2026 masaukai a Makkah da Madinah, gabanin wa’adin da hukumomin Saudiyya suka gindaya.Shugaban hukumar, Farfesa Abdullahi Usman ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da hadiminsa kan harkokin yaɗa labarai, Ahmed Mu’azu, ya fitar a ranar Litinin.Sanarwar ta ce an samu nasarar saka bayanan masaukin Nijeriya tare da amincewar Ma’aikatar Hajji da Umrah ta Saudiyya, bisa bin jadawalin da aka tanada. Wannan ya biyo bayan umarnin mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima, wanda ya buƙaci a kammala muhimman shirye-shiryen Hajji cikin…
Read More
Mai Ali Ghaji: Tushen ƙarfin daular Borno

Mai Ali Ghaji: Tushen ƙarfin daular Borno

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD A tarihin Afirka, daular Kanem-Borno ta kasance ɗaya daga cikin manyan masarautu waɗanda suka yi fice a Arewacin nahiyar, tare da zaman kanta kusan shekaru ɗari tara. A cikin jerin sarakunan da suka yi tasiri wajen kafa ƙarfi da daidaito a wannan daula, ɗaya daga cikin fitattun masu mulki shi ne Mai Ali Ghaji — wanda aka fi sani da Ali I Gaji ko kuma Ghaji, wanda ya yi mulki daga kusan shekara ta 1470/1472 zuwa 1503/1504.  Mai Ali Ghaji ya zo a kan gaba a lokacin da daular Kanem-Borno ke fuskantar ƙalubale na siyasa da…
Read More
Lamiyya: Nazarin waƙar  ‘La’ila’ ta Alhaji Auwal Umar Dangawuna

Lamiyya: Nazarin waƙar  ‘La’ila’ ta Alhaji Auwal Umar Dangawuna

Daga MD ASNANIC 1.0 Gabatarwa Bayyanannen abu ne cewa, mutanen da suka fara tsara waƙoƙi musamman domin yabon Annabi Muhammad (SAW) a duniya sun haɗa da: mahaifiyarsa Aminatu 'yar Wahabi da kakansa Abdulmuɗallib ɗan Hashim da mai rainonsa Halimatus Sa'adiya. Sai dai mutanen da suka fi shura a yabonsa bayan risala sun haɗa da Hassanu ɗan Sabitu da Ka'abu ɗan Zubairu da Abdullahi ɗan Rawaha. A ƙasar Hausa kuwa, mutanen da ake tunanin su suka fara tsara yabon Annabi (SAW) a waƙe tun a ƙarni na 13 zuwa na 17 sun haɗa da Wali ɗanmarina da Wali ɗanmasani da Abdullahi…
Read More
Muhimman hanyoyi 10 na kula da fata (2)

Muhimman hanyoyi 10 na kula da fata (2)

Daga AISHA ASAS Mai karatu barkanmu da sake kasancewa a wannan shafi na Kwalliya. Sannunku da jimirin bibiyar mu. A ci gaba da tattaunawa kan muhimman hanyoyin kula da fata, idan mai karatu bai manta ba, mun kawo guda biyu a makon da ya gabata, bayan mun yi shimfiɗa kan abinda ake nufi da kula da fata. 3. Amfani da man kare fata daga rana: Rana na ɗaya daga cikin ababen da ke yi wa fata lahani, idan na ce rana ina nufin ranar da zata fito sosai, kamar daga sha ɗaya na safe zuwa sama. Domin a cewar masana…
Read More
Dandalin Shawara: Ina son in hana matata aiki don ba na cin komai daga abinda take samu

Dandalin Shawara: Ina son in hana matata aiki don ba na cin komai daga abinda take samu

(ci gaba daga makon jiya) Daga AISHA ASAS TAMBAYA: Assalamu alaikum. Malama Aisah da farko ina neman ahuwa kan aiko da sako ta murya ba ta rubutu ba. Ni dai matsalata guda zuwa biyu. Matata tana aiki don malamar makaranta ce. To matsalar dai ita ce, ko dannan zuwa can ba ta so ta yi mani nasiha akan sha'anin gida. Bansan ranar da ta siye ko sabulu a gidan ba da niyyar rage min ɗawainiya. Kuma ko Naira biyar na ara to hankali bayya kwanciya sai na biya ta ita. Ko yaranta ma ba abinda take iya yi masu cikin…
Read More
2027: Jam’iyyar APC a Zamfara ta ƙaryata raɗe raɗin tsayar da ɗan takara

2027: Jam’iyyar APC a Zamfara ta ƙaryata raɗe raɗin tsayar da ɗan takara

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau Jam'iyyar APC a Jihar Zamfara tayi watsi da jita Jihar da ke yawo a kafafen sada zumunta cewar ta tsaida ɗan takarar ta a zaɓen shekarar 2027 da ke tafe. Sakataren yaɗa labarai na jam'iyyar a jihar ne Yusuf Idris ya bayyana hakan ga manema labarai yau Talata. A cewar sa jita jitar ƙarya ce tsagwaron ta, yana mai bayyana cewar masu yaɗa jita jitar sunyi ne bada yawun jam'iyyar ba. "Ina amfani da wannan damar in sanar da cewar har yanzu jam'iyyar APC a jihar Zamfara babu wani ɗan takara da aka zaɓa. Ya…
Read More