ukarofi

12654 Posts
‘Yan bindiga sun kashe mutane fiye da 20 a Katsina

‘Yan bindiga sun kashe mutane fiye da 20 a Katsina

' Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Lamarin ya faru a garin Doma da ke ƙaramar hukumar Faskari inda yanzu haka anyi wa waɗanda suka rasu sutura ,su kuma waɗanda su ka samu raunuka daban daban a kwashe su zuwa asibiti. Haka kuma wasu mazauna garin sun gudu ba a san inda suka yi ba. Bayanai sun nuna cewa yan bindigan sun shiga garin ne da rana tsaka a lokacin da wasu mutanen garin sun taru wajen rabon gado na gidan marigayi Ashiru Gari Doma. Nan take yan bindigan sukai ta harbe harbe tare da banka wa gidaje wuta. Bayanai sun…
Read More
Farfesa Haruna ya ƙaddamar da aikin gina hanyar kilomita 15 a Nasarawa

Farfesa Haruna ya ƙaddamar da aikin gina hanyar kilomita 15 a Nasarawa

Daga JOHN WADA, a Keffi Ɗan takarar kujerar gwamnan jihar Nasarawa a inuwar jam'iyyar APC mai ci a jihar, Farfesa Muhammed Sani Haruna ya ƙaddamar da wani aikin fara gina wani hanyar karkara da ya haɗa ƙauyukan Keffin-shanu da Gwagwa abbreviations da Takalafiya da Unguwar Gwandara duk a ƙananan hukumomin Karu da Nasarawa a jihar ta Nasarawa da nufin inganta harkokin kasuwanci da zirga-zirga a yankin. Da yake jawabin sa a wajen taron wanda aka gudanar a ƙauyen Keffin-shanu, ɗan takarar gwamnan Farfesa Muhammad Sani Haruna ya bayyana cewa wannan aiki na daga cikin ayukan agaji da yake gudanar wa…
Read More
Faɗi alkhari ko ka yi shiru

Faɗi alkhari ko ka yi shiru

Assalamu alaikum wa rahmatullahi wa barakatuhu. ’Yan uwa masu daraja, wannan wasiƙa tunatarwa ce ga zuciyarmu da harshenmu a wannan zamani da kalma guda ke iya gina rayuwa ko rusa ta. Addinin Musulunci ya ɗora wa kalma matsayi mai girma, domin daga baki ne alkhairi ke fita, kuma daga nan ne sharri ke bazuwa. Saboda haka Manzon Allah (SAW) ya yi gargaɗi mai tsanani da cewa: “Duk wanda ya yi imani da Allah da Ranar Lahira, to ya faɗi alkhairi ko kuma ya yi shiru.” Wannan hadisi shi ne tubalin wannan wasiƙa. A kwanakin nan, al’ummar mu sun shiga jimami…
Read More
A ci daɗi lafiya tare da dakon ƙididdiga 

A ci daɗi lafiya tare da dakon ƙididdiga 

Daga ALI ABUBAKAR SADIK Karshen dai tuka-tuki, tik. Gwamna da muƙarrabansa sun fice daga NNPP da shirin sauya sheka zuwa APC. To, a matsayina na Dan Kano wanda ya baiwa wannan gwamnati gudunmuwa don ta ci zabe a 2019 da 2023, ina jin cewa lallai an ci Amana ta, tudu biyu. Na farko Gwamna, a tsammaninmu, ya gaza fuskantar matsalolin da Kano ke fuskanta tun da aka zabe shi, sannan kuma a yanzu ya ci amanar kuri'ar kanawa ta hayar kokarin komawa APC. Saboda lalaci da lalacewa da al'ummar mu ta yi, za ka ga mutane wadanda su ka je…
Read More
Bambancin so da soyayya

Bambancin so da soyayya

Daga MOHAMMED BALA GARBA Wasu sun ɗauka da 'So' da 'Soyayya' duk abu ɗaya, sai dai ba haka abin yake ba. Ita Soyyaya aiki ce (verb); yayin da So kuma wani abu ne mai zaman kansa (independent), wanda wani lokacin shi yake samar da Soyayya. Amma kafin nan, bari mu yi duba ga yadda wasu suka ba da ma'anonin su. Ma'anar so. -So – wani sauki ne na zuci da ke ziyarar masoya guda biyu ba tare da ya shawarce su ba. ~ Aisha Abdullahi Muhammad  -So – wata iska ce mai yawo wanda babu wani ɗan adam ko dabba…
Read More
Hattara dai ’yan siyasar soshiyal midiya!

Hattara dai ’yan siyasar soshiyal midiya!

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU Ana ci gaba da samun sauye-sauye a harkokin siyasa a ƙasar nan, yayin da ake ƙara kusantar Babban Zaɓe na shekarar 2027. 'Yan siyasa, musamman sabbin yanka masu neman a san da su da gwamnoni masu neman tazarce suna ta ƙoƙarin sauyin sheƙa daga wannan jam’iyya zuwa waccan. Mun ga yadda jihohi irin su Kano, Filato, da Taraba, gwamnoninsu suka yi sauyin jam'iyya zuwa babbar jam’iyya mai mulki ta APC. Matakin da wasu ke kallo a matsayin wayon a ci ne, wato kowa ƙoƙari yake yi a dama da shi a siyasar tarayya, a sha romon…
Read More
Shin amsa sunan Larabawa watsi da al’adar Bahaushe ne?

Shin amsa sunan Larabawa watsi da al’adar Bahaushe ne?

Daga NASIRU ADAMU EL-HIKAYA Wani shafin yanar gizo mai taken THE NIGERIAN BAHAUSHE ya yi wuf ya wallafa wani rubutu da ɗaya daga ‘yan Hausa zalla Aliyu Ammani ya rubuta tun 2019 ya na nuna fargaba cewa sunayen gargajiya na Hausawa za su bace don daukar na Larabawa. Ammani bai tsaya ba sai da ya caccaki wani abu da ya zayyana da wankewa Hausawa kwakwalwa da nau’in musulunci na daban da Jihadin Sakkwato (na Shehu Mujaddadi) ya kawo na goge duk wasu alamu da al’adu na Hausawa kafin zuwan Musulunci. Ammani dai a nan bai kawo aya ko Hadisi daga…
Read More
Masu ruwa da tsaki na APC a Dawakin Tofa sun tattauna hanyar kawo cigaban ƙaramar hukumar

Masu ruwa da tsaki na APC a Dawakin Tofa sun tattauna hanyar kawo cigaban ƙaramar hukumar

Daga RABIU SANUSI a Kano Masu ruwa da tsaki na jam’iyyar APC a ƙaramar hukumar Dawakin Tofa sun gudanar da taro na musamman da yammacin ranar Litinin, domin tattauna muhimman batutuwa da za su taimaka wajen bunƙasa cigaba da hadin kai a ƙaramar hukumar. Taron wanda ya samu halartar manyan jagorori da jiga-jigan jam’iyyar daga matakai daban-daban. Daga cikin mahalarta akwai babban daraktan yada labarai na Gwamnatin Jihar Kano, Alhaji Sanusi Bature D-Tofa. Sauran waɗanda suka halarta sun haɗa da shugaban ƙaramar hukumar Dawakin Tofa, Alhaji Adamu Shehu Bello Danmaliki,tsohon ɗan takarar majalisar tarayya a jam’iyyar APC a zaɓen 2023,…
Read More
Zaɓen 2027: APC ta yadda da Tinubu da Dikko Raɗɗa su zarce

Zaɓen 2027: APC ta yadda da Tinubu da Dikko Raɗɗa su zarce

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Shugaban masu ruwa da tsaki a jam'iyar APC a jihar Katsina Alhaji Salisu Mamman kaɗanɗanni ya miƙa buƙatar haka ga dimbin magoyan ya'yan da suka taru a filin wasa na Muhammadu Dikko a Katsina. A yayin taron, Manyan jiga-jigai da shugabannin Jam’iyar a Jihar Katsina sun bayyana cikakkiyar amincewarsu ga shugaban ƙasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, , da kuma Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Raɗɗa, a matsayin ‘yan takarar Shugaban ƙasa da Gwamna na jam’iyyar APC a zaɓen shekarar 2027. A jawabinsa bayan amince da buƙatar,shugaban masu ruwa da tsaki na APC a jihar…
Read More
Gwamnatin Katsina za ta tallafa wa mata ‘yan kasuwa da Naira miliyan 500

Gwamnatin Katsina za ta tallafa wa mata ‘yan kasuwa da Naira miliyan 500

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Gwamnan Jihar Malam Dikko Umaru Raɗɗa ya sake jaddada ƙudirin gwamnatinsa na ƙarfafa mata, inda ya bayyana taron “Where Influence Meets Investment” a matsayin muhimmin dandali na bunƙasa tattalin arziki mai haɗa kowa da kowa da kuma samar da ci gaba mai ɗorewa. Da yake jawabi a babban taron Katsina Inner Wheel Development Initiative (KIWDI), wanda aka shirya tare da haɗin gwiwar ma’aikatar harkokin mata, Gwamna Raɗɗa ya ce taron ya samar da muhimmiyar dama ga shugabannin mata, ’yan kasuwa, masu zuba jari da abokan hulɗar ci gaba domin bincika hanyoyi masu amfani na ƙarfafa…
Read More