ukarofi

12654 Posts
Ayyukan raya ƙasa da gwamna ke aiwatarwa suka sa na shiga APC – Dr Aminu Waziri

Ayyukan raya ƙasa da gwamna ke aiwatarwa suka sa na shiga APC – Dr Aminu Waziri

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Tsohon babban sakatare a gwamnatin Masari Dr Aminu Waziri Malumfashi ya faɗa haka a wata hira da manema labarai a Katsina. Ya ce da shi aka kafa jam'iyar haɗaka ta ADC a jihar Katsina amma da tafiya tayi tafi sai ya lura cewa bata kai ƙarfin da za ta ƙalubalanci jam'iyar APC ba wanda ita take da gwamnati. Dr waziri Malumfashi wanda ya taɓa riƙe muƙamin shugaban hukumar bada agajin gaggawa a jihar Katsina ya ƙara bada wasu dalilai da suka sa ya bar jam'iyar adawar ta ADC a Katsina. Wasu daga ciki kuwa sun…
Read More
Tallafin Nuhu Ribadu: Yadda Musa Maisana’a ya raba abinci da kuɗi ga Jaruman Kannywood 

Tallafin Nuhu Ribadu: Yadda Musa Maisana’a ya raba abinci da kuɗi ga Jaruman Kannywood 

Daga MUKHTAR YAKUBU  Fitaccen jarumi a masana'antar Kannywood Musa Abdullahi, wanda aka fi sani da Musa Maisana'a, ya yi wani taro na rabon buhuhunan dhinkafa da kuɗaɗe ga wasu daga cikin jaruman Kannywood da suke cikin buƙatar taimako ta ɓangaren buƙatun rayuwar yau da kullum. Taron rabon kayan abinci da kuɗin wanda aka gudanar a ranar Litinin a cikin garin Kano ya samu halartar ɗimbin jama'a da suka halarci wajen domin samun rabon su na kuɗi da abinci da aka raba a wajen. A wajen taron dai an ga fuskokin tsofaffin jarumai masu yawa da suka halarci taron irin su…
Read More
Sharhin fim ɗin Balaraba

Sharhin fim ɗin Balaraba

Daga ABDULYASSAR AMINU ABUBAKAR Sunan fim: Balaraba Kamfani: Mai Shadda Global Resources Labari: Nura Hussaini Tsara Labari: Yakubu M. Kumo Daukar Hoto: Moses Stephen/Saifullahi Deen Sauti: Bello Minna Daukar Nauyi: Abubakar Bashir Mai Shadda Shiryawa: Abubakar Bashir Mai Shadda M/ Umarni: Sadik Sani Sadik Umarni: Abubakar Bashir Mai Shadda Fim ɗin Balaraba, wani fim ne da ya bayyana rayuwar wani matashi Umar Faruk,  mai tsananin fushi da hasala, ta yadda har ba ya iya yi wa harshensa linzami. Bai saurarawa kowa ba, abokai, dangi, kai har ma da mahaifinsa a wani takin. A tsaka da hakan ne auren shi ya…
Read More
Indiya ta tabbatar da samuwar cutar Nipah

Indiya ta tabbatar da samuwar cutar Nipah

*Kasar ta bayyana sabbin mutane biyu masu ɗauke da cutar Nipah a West Bengal Gwamnatin Indiya ta tabbatar da ɓullar sabbin cututtukan Nipah guda biyu a Jihar West Bengal da ke gabashin ƙasar, lamarin da ya janyo ƙarin tsauraran matakan binciken lafiyar matafiya a wasu ƙasashen kudu maso gabashin Asiya, musamman Thailand da Malaysia. Ma’aikatar Lafiya ta Indiya ta bayyana hakan ne a ranar 28 ga Janairu, 2026, inda ta ce an gano cututtukan tun daga watan Disamba, kuma ana ci gaba da sanya ido sosai domin hana yaɗuwar cutar. A cikin wata sanarwa, ma’aikatar ta gargadi jama’a da su…
Read More
Rikicin soja a Sudan ta Kudu: Sojojin gwamnati sun umurci farar hula da ma’aikatan agaji su fice daga yankunan

Rikicin soja a Sudan ta Kudu: Sojojin gwamnati sun umurci farar hula da ma’aikatan agaji su fice daga yankunan

Sudan ta Kudu na fuskantar rikici mai tsanani yayin da sojojin gwamnati suka bayar da umurnin gaggawa ga farar hula da ma’aikatan Majalisar ɗinkin Duniya (UNMISS) da NGOs su fice daga yankunan Jonglei. Wannan mataki ya biyo bayan ƙara tsananta rikicin sojojin gwamnati da ‘yan adawar SPLA‑IO, inda hare-hare suka fi yawa a Nyirol, Akobo da Uror. Gwamnatin ta bayyana cewa matakin na da nufin kare rayuka da dukiyoyin jama’a, tare da dawowa da oda a yankuna masu rikici. Sai dai Majalisar ɗinkin Duniya ta yi gargadin cewa wannan mataki zai iya jefa dubban farar hula cikin haɗari, yayin da…
Read More
Rikicin Greenland: NATO da ƙasashen Turai sun fara shirin atisaye don tabbatar da tsaro

Rikicin Greenland: NATO da ƙasashen Turai sun fara shirin atisaye don tabbatar da tsaro

Shugaban Amurka Donald Trump ya ƙara ta da ƙayar baya kan Greenland, wani yanki mai muhimmanci a tsaron Arctic da ke ƙarƙashin ikon Denmark.  Rahotanni sun nuna cewa Amurka na so ta ƙara samun iko a yankin, wanda ya jawo ce-ce-ku-ce a Turai. ƙasashen Turai sun bayyana damuwa kan wannan mataki, inda Faransa ta nemi atisayen NATO a Greenland domin tabbatar da tsaro da haɗin kai a yankin Arctic. Shugaba Emmanuel Macron ya ce: “Turai ba za ta janye ko ta amince da tilastawa ba; haɗin kai da mutunta dokokin ƙasa da ƙasa su ne ginshiƙin tsaron duniya.”
Read More
Ranar International Holocaust Remembrance: Duniya ta tuna mummunan kisan da aka yi a yammacin Turai

Ranar International Holocaust Remembrance: Duniya ta tuna mummunan kisan da aka yi a yammacin Turai

International Holocaust Remembrance Day, rana ce da ake tuna wa da kisan kiyashi da aka yi wa miliyoyin mutane a lokacin Yaƙin Duniya na II, musamman a sansanin Auschwitz da sauran wurare. Ana gudanar da taron addu’a, ƙona kyandir, da karatun tarihi a birane kamar Berlin, London, New York da Warsaw. Masana tarihi da shugabanni suna jaddada darussan baya a matsayin hanyar ƙarfafa zaman lafiya, mutunta bambance-bambance da hana faruwar irin wannan ɓarna a nan gaba. “Tarihi ya koya mana cewa rashin mutunta juna da wariya na haifar da ɓarna; duniya na buƙatar zaman lafiya da adalci,” inji wani malami…
Read More
Aƙalla Mutane 5,777 sun rasa rayukansu a Iran – Rahoton Kungiyar Kare Hakkin Dan Adam

Aƙalla Mutane 5,777 sun rasa rayukansu a Iran – Rahoton Kungiyar Kare Hakkin Dan Adam

Kungiyar masu rajin kare haƙƙin ɗan adam mai suna Human Rights Activists News Agency ta fitar da rahoto cewa “jami’an tsaro na Iran sun kashe aƙalla mutane 5,777, ciki har da yara ƙanana 86, yayin da ake ƙoƙarin murƙushe zanga‑zangar lumana da ƙaruwar adawa da gwamnati.” Wannan rahoto ya kuma nuna cewa aƙalla mutane kusan 42,000 an kama su yayin rikicin da ya ɗauki hankali a cikin 'yan watanni.  Rahoton ya jawo cece‑kuce sosai, inda ƙungiyoyin kare haƙƙin ɗan adam ke bayyana cewa ana amfani da makamai da ƙarfi fiye da kima wajen murƙushe ‘yan adawa, lamarin da ya jawo…
Read More
An tilasta Falasɗinawa fiye 37,000 barin gidajensu a 2025 – Majalisar Dinkin Duniya 

An tilasta Falasɗinawa fiye 37,000 barin gidajensu a 2025 – Majalisar Dinkin Duniya 

A cikin wani rahoton da ƙungiyar Majalisar ɗinkin Duniya ta fitar a ranar Talata, an bayyana cewa fiye da 37,000 Falasɗinawa ne aka tilasta su barin gidajensu a shekarar 2025 a Yammacin Banki (West Bank), yawanci dalilin irin aayyukan ɓarna da sojojin Isra’ila ke aikatawa da sunan matakan tsaro waɗanda suka shafi sansanonin ‘yan gudun hijira. Wannan adadi ya jawo ƙarin damuwa daga ƙasashen duniya, waɗanda ke kira ga ɗaukar matakin rage tashin hankali da tallafa wa waɗanda rikicin ya shafa.  Rahoton ya ce wannan ƙaura ta tilastawa ta faru ne a lokacin da ake ƙoƙarin sake ƙoƙarin kwaɗaita zaman…
Read More
Tsohon Shugaban Philippines na fuskantar tuhume-tuhumen laifukan yaƙi

Tsohon Shugaban Philippines na fuskantar tuhume-tuhumen laifukan yaƙi

Kotun Harkokin Laifuka ta Duniya (ICC) ta yanke hukuncin cewa tsohon shugaban ƙasar Philippines, Rodrigo Duterte, yana da lafiya da hankali da zai iya halartar zaman tabbatar da tuhuma da ake yi masa a kotun, dangane da zargin aikata laifukan yaƙi da tu'ammali da muyaggun kwayoyi tare da cin zarafin ɗan adam.  Wannan hukunci ya tabbatar da cewa da yiwar a ɗage zaman tabbatar da tuhuma da aka shirya a ranar 23 Fabrairu 2026, domin isa kai tsaye a shari’a kan laifukan da ake zargin ya aikata.  Masu rajin kare haƙƙin ɗan adam da masu sharhi sun bayyana wannan mataki a matsayin…
Read More