ukarofi

12654 Posts
Jama’a sun hallaka matashin da ya kashe matar aure da adda a Zamfara

Jama’a sun hallaka matashin da ya kashe matar aure da adda a Zamfara

Wani matashi mai suna Hassan ɗan Chanji ya hallaka wata matar aure mai suna Rakiyaya, matar Malam Maikuddi, a ƙauyen Dambo da ke ƙaramar hukumar Bakura a jihar Zamfara, lamarin da daga bisani ya rikiɗe zuwa ramuwar gayya inda shi ma ya rasa ransa. Wani mazaunin ƙauyen, Malam Tukur Dambo, ya shaida wa manema labarai ta wayar tarho cewa al’amarin ya faru ne da yammacin ranar Alhamis bayan wata hatsaniya ta ɓarke tsakanin wanda ake zargi da marigayiyar. A cewarsa, bayan cacar baki ta tsananta, matashin ya shiga cikin gida ya ɗauko adda, inda ya sare matar har ta mutu.…
Read More
Amarya ta zuba wa angonta maganin ɓera a abinci

Amarya ta zuba wa angonta maganin ɓera a abinci

Rundunar ’yan sandan jihar Jigawa ta cafke wata sabuwar amarya bisa zargin hallaka mijinta ta hanyar sanya masa maganin ɓera a abinci, lamarin da ya girgiza al’umma a ƙauyen Gauza da ke ƙaramar Hukumar Jahun ta jihar Jigawa. Rahotanni sun nuna cewa al’amarin ya faru ne da misalin ƙarfe 5:00 na yamma ranar 23 ga Janairu, 2026. Marigayin, wanda ba a bayyana sunansa nan take ba, ya dawo gida inda ya ci abincin da aka tanadar masa, kafin daga bisani ya fara jin jiki yana tabarbarewa cikin gaggawa. Mai magana da yawun rundunar ’yan sandan jihar, SP Shi’isu Adam, ya…
Read More
Nijeriya ta dawo sahun gaba a taron tattalin arzikin duniya – Shettima

Nijeriya ta dawo sahun gaba a taron tattalin arzikin duniya – Shettima

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Mataimakin Shugaban Nijeriya, Kashim Shettima, ya dawo Abuja bayan kammala wata ziyara ta mako guda zuwa Guinea-Conakry da kuma Switzerland, inda ya bayyana cewa Nijeriya ta sake komawa sahun gaba a tattaunawar tattalin arziki da manufofin duniya. A wata sanarwa da mai taimaka masa na musamman kan harkokin yaɗa labarai da sadarwa, Stanley Nkwocha, ya fitar, an ce Mataimakin Shugaban ƙasar ya iso Filin Jiragen Sama na Nnamdi Azikiwe da ke Abuja a ranar Asabar. Shettima ya wakilci Shugaba Bola Ahmed Tinubu a bikin rantsar da sabon shugaban ƙasar Guinea, Mamadi Doumbouya, kafin daga bisani ya…
Read More
Yadda iskar gas ta CNG ta samu karɓuwa duk da ƙalubalen tashoshin sayarwa da tsada

Yadda iskar gas ta CNG ta samu karɓuwa duk da ƙalubalen tashoshin sayarwa da tsada

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Shirin amfani da iskar gas ta CNG da Gwamnatin Tarayya ta ƙaddamar a matsayin madadin fetur ya fara samun karɓuwa a wurin ’yan Nijeriya, duk da cewa masu ruwa da tsaki na ci gaba da roƙon gwamnati ta magance matsalolin samuwar sa, ƙarancin ababen more rayuwa da kuma tsadar sauya injin mota zuwa inji mai amfani da CNG. Wannan tsari na daga cikin muhimman sauye-sauyen da gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta ɓullo da su a fannin makamashi, inda ake ƙoƙarin rage dogaro da fetur tare da bunƙasa amfani da ɗimbin arzikin iskar gas da ƙasar…
Read More
Tinubu na gyara tattalin arziki domin kare dimukraɗiyyar Nijeriya – Dare

Tinubu na gyara tattalin arziki domin kare dimukraɗiyyar Nijeriya – Dare

Daga MAHD MUSA MUHAMMAD Mai ba Shugaban ƙasa shawara kan harkokin yaɗa labarai da sadarwar jama’a, Sunday Dare, ya buƙaci ’yan Nijeriya su ba da goyon baya ga sauye-sauyen tattalin arziki da gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ke aiwatarwa ƙarƙashin ajandar “Renewed Hope”. Dare ya bayyana haka ne yayin gabatar da lacca a taron jama’a da jaridar Daily Trust ta shirya a Abuja, inda ya ce lokacin da Tinubu ya karɓi mulki a shekarar 2023, Nijeriya na fuskantar hauhawar farashi, tangarɗar canjin kuɗi, tarin basussuka da kuma raunin kwarin gwiwar masu zuba jari. A cewarsa, cire tallafin man fetur da…
Read More
Hukumar Kwastom ta tara Naira tiriliyan 7.28 a 2025

Hukumar Kwastom ta tara Naira tiriliyan 7.28 a 2025

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Hukumar Kwastom ta Nijeriya (NCS) ta sanar da tara kuɗin shiga da suka kai Naira tiriliyan 7.28 a shekarar 2025, wani ci gaba da aka bayyana a matsayin ɗaya daga cikin manyan nasarorin tattalin arziki da hukumar ta taɓa samu cikin ‘yan shekarun nan. Babban Kwanturola Janar na Hukumar Kwastom, Bashir Adeniyi, ne ya bayyana hakan a Abuja yayin bikin Ranar Kwastom ta Duniya ta 2026, inda ya jaddada cewa sauye-sauyen da aka aiwatar a tsarin aiki, amfani da fasaha ta zamani da kuma ƙarfafa haɗin gwiwa da masu ruwa da tsaki ne suka haifar da…
Read More
CBN na tsara sabuwar doka kan katin cire kuɗi da ayyukan ATM

CBN na tsara sabuwar doka kan katin cire kuɗi da ayyukan ATM

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Babban Bankin Nijeriya (CBN) ya sanar da shirin fitar da sabuwar ƙa’ida da za ta sauƙaƙa samar da katinan cire kuɗi tare da inganta yadda na’urorin ATM ke aiki a faɗin ƙasar. Gwamnan CBN, Olayemi Cardoso, ne ya bayyana hakan ta bakin mai ba shi shawara na musamman, Fatai Karim, a wani taro da aka gudanar a ƙarshen mako. Ya ce matakin na daga cikin ƙoƙarin da bankin ke yi na magance matsalolin samun kuɗi a hannu da kuma dawo da amincewar jama’a ga tsarin biyan kuɗi ta na’urorin zamani. A cewar CBN, sabuwar manufar za…
Read More
Manoma 74,000 za su fara noman kanunfari a faɗin Nijeriya – Kungiyar Masu Noman Kanunfari

Manoma 74,000 za su fara noman kanunfari a faɗin Nijeriya – Kungiyar Masu Noman Kanunfari

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Kungiyar Masu Noma, Sarrafawa da Tallan Kanunfari a Nujeriya ta sanar da shirin fara noman wannan amfanin gona karo na farko a tarihin ƙasar nan, inda ake sa ran manoma sama da 74,000 za su shiga aikin a lokacin daminar shekarar 2026. Babban Mai Tsara Ayyukan ƙungiyar, Abdullahi Shuaibu, ne ya bayyana hakan a ƙarshen wani taron horas da masu neman a yankin Arewa maso Yamma, wanda aka gudanar a Cibiyar Binciken Noma ta IAR da ke Jami’ar Ahmadu Bello, Zariya. Ya bayyana cewa, shirin zai haɗa aƙalla manoma 2,000 daga kowace jiha cikin jihohi 36…
Read More
Masanin kasuwar jari ya nemi a tsawaita wa’adin cika sabbin sharuɗɗan hukumar SEC

Masanin kasuwar jari ya nemi a tsawaita wa’adin cika sabbin sharuɗɗan hukumar SEC

Daga MAHDI MUSA MUHAMAMD Shugaban ƙungiyar Masana Kasuwar Jari ta Nijeriya (CMAN), Farfesa Uche Uwaleke, ya bayyana cikakken goyon bayansa ga shirin Hukumar Kula da Kasuwar Jari ta ƙasa (SEC) na tilasta wa kamfanonin da ke aiki a kasuwar jari ƙara jarinsu, yana mai cewa matakin na da matuƙar muhimmanci wajen kare masu zuba jari da kuma ƙarfafa ɗorewar kasuwar. Uwaleke, wanda kuma shi ne Daraktan Cibiyar Nazarin Kasuwar Jari a Jami’ar Jihar Nasarawa, ya ce tsarin jarin da ake aiki da shi tun daga shekarar 2015 ya daina dacewa da yanayin tattalin arzikin yanzu, musamman la’akari da fazuwar darajar…
Read More
ACF ta danganta kisan uwa da ’ya’yanta shida a Kano da matsalar shaye-shaye

ACF ta danganta kisan uwa da ’ya’yanta shida a Kano da matsalar shaye-shaye

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Kungiyar tuntuɓa ta Arewa (ACF) ta danganta mummunan kisan da aka yi wa wata uwa da ’ya’yanta shida a Kano da ƙaruwar matsalar shaye-shayen miyagun ƙwayoyi, inda ta buƙaci a ɗauki matakan gaggawa na haɗin gwiwar al’umma domin daƙile wannan barazana. Sakataren yaɗa labarai na ACF reshen Jihar Kano, Nasiru Yusuf Ibrahim, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da aka rabawa manema labarai a ranar Litinin. Waɗanda aka kashe sun haɗa da Fatima Abubakar da ’ya’yanta shida, lamarin da ya girgiza mazauna unguwar Dorayi Chiranchi da ke cikin birnin Kano a makon da ya gabata.…
Read More