01
Feb
Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Ministar Al’adu da Yawon Buɗe Ido, Hannatu Musawa, ta yi gargaɗin cewa jam’iyyar APC na iya fuskantar matsala a zaɓen shugaban ƙasa na 2027 muddin ta cire Mataimakin Shugaban ƙasa, Kashim Shettima, daga tikitin takara tare da Shugaba Bola Ahmed Tinubu. Musawa wadda ta yi wannan tsokaci yayin wata hira da da fitaccen ɗan jaridar nan, Seun Okinbaloye , ta ce cire Shettima ko maye gurbinsa da wanda ba Musulmi ɗan Arewa ba na iya janyo babbar matsala ga APC, musamman a jihohin Arewa ta Tsakiya da Arewa maso Yamma, inda siyasa ke da…
