ukarofi

12654 Posts
2027: Sauya takara Musulmi daga Arewa zai iya jefa APC cikin haɗarin rasa mulki — Hannatu Musawa

2027: Sauya takara Musulmi daga Arewa zai iya jefa APC cikin haɗarin rasa mulki — Hannatu Musawa

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Ministar Al’adu da Yawon Buɗe Ido, Hannatu Musawa, ta yi gargaɗi cewa jam’iyyar APC na iya fuskantar babbar barazana a zaben 2027 idan har ta yanke shawarar cire ɗan takarar Musulmi daga Arewacin Nijeriya a tikitin shugaban ƙasa na Shugaba Bola Ahmed Tinubu. Musawa ta bayyana hakan ne yayin wata hira da aka watsa a wani shiri na siyasa, inda ake ta cece-kuce kan yiwuwar sauya tsarin tikitin Musulmi da Musulmi wanda ya kai APC ga nasara a zaɓen 2023. Ta jaddada cewa duk wani sauyi da zai kawar da Mataimakin Shugaban ƙasa Kashim Shettima ko…
Read More
NDLEA ta kama ’yar Brazil da hodar iblis a Abuja

NDLEA ta kama ’yar Brazil da hodar iblis a Abuja

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun ƙwayoyi ta ƙasa (NDLEA) ta sanar da cafke wata ’yar ƙasar Brazil mai suna Ingrid Benevides, mai shekaru 30, da ake zargi da shigo da hodar iblis mai nauyin kilo 30.09 ta hanyar ɓoye ta cikin buhunan kofi a Filin Jirgin Sama na ƙasa da ƙasa na Nnamdi Azikiwe da ke Abuja. A cikin wata sanarwa da kakakin hukumar, Femi Babafemi, ya fitar, ya bayyana cewa an kama matar ne bayan ta iso Abuja ta jirgin ƙatar Airways, inda jami’an NDLEA suka daɗe suna bibiyarta ta hanyar bayanan sirri kafin…
Read More
Adadin ajiyar kuɗaɗen waje na Nijeriya ya haura Dala biliyan 46 cikin shekaru takwas

Adadin ajiyar kuɗaɗen waje na Nijeriya ya haura Dala biliyan 46 cikin shekaru takwas

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Adadin ajiyar kuɗaɗen waje na Nijeriya ya haura dala biliyan 46 karo na farko cikin kusan shekaru takwas, wani ci gaba da ke nuna daidaituwar tattalin arziki da kuma kyakkyawan tafiyar da harkokin musayar kuɗaɗen waje a ƙasar. Sabbin alƙaluman da Babban Bankin Nijeriya (CBN) ya fitar zuwa ranar 22 ga Janairu, 2026, sun nuna cewa ajiyar ya kai kusan dala biliyan 46, matakin da ƙasar ba ta kai ba tun daga watan Agustan 2018 lokacin da ya tsaya a kusan dala biliyan 45.9. Wannan ƙaruwa na zuwa ne sakamakon farfaɗowar da ta fara bayyana tun…
Read More
Shugaban Shell ya yaba wa Tinubu kan inganta hanyoyin zuba jari a Nijeriya

Shugaban Shell ya yaba wa Tinubu kan inganta hanyoyin zuba jari a Nijeriya

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Babban jami’in kamfanin mai na duniya, wato Shell, Wael Sawan, ya yaba wa Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu bisa matakan da gwamnatinsa ta ɗauka wanda ya ce sun farfaɗo da kwarin gwiwar masu zuba jari tare da inganta yanayin kasuwanci a Nijeriya. A wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban ƙasa, Bayo Onanuga, ya fitar, Sawan ya bayyana hakan ne yayin wata ganawa da suka yi da Shugaba Tinubu a Fadar Shugaban ƙasa da ke Abuja. A cewar shugaban na Shell, kamfanin na ƙara zurfafa jarinsa a Nijeriya tare da haɗin gwiwar wasu abokan hulɗa,…
Read More
Jirgin sojojin sama ya kashe mamoma biyu ‘bisa kuskure’ a ƙauyen Neja

Jirgin sojojin sama ya kashe mamoma biyu ‘bisa kuskure’ a ƙauyen Neja

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Aƙalla manoma biyu sun rasa rayukansu, yayin da wasu da dama ciki har da ƙananan yara suka jikkata a harin sama da aka kai garin Kurgi da ke ƙaramar hukumar Mariga ta Jihar Neja. Mazauna yankin sun shaida wa Manhaja cewa wani jirgin sama mai bincike, wanda ake zargin na rundunar sojin saman Nijeriya ne, ya yi ta shawagi a sama na tsawon mintuna a ranar Lahadi kafin ya fara harbi kan mutanen da ke gudanar da harkokinsu na yau da kullum. Wani mazaunin yankin ya ce harsashin ya afka wa mazauna yankin har…
Read More
Abba Kabir zai samu wa’adi na biyu a 2027 — Ganduje

Abba Kabir zai samu wa’adi na biyu a 2027 — Ganduje

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Tsohon Shugaban Jam’iyyar APC na ƙasa, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya tabbatar wa Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, cewa zai yi nasara a zaɓen gwamna na 2027, yana mai cewa jam’iyyar APC za ta ba shi cikakken goyon baya domin samun wa’adi na biyu. Ganduje ya faɗi hakan ne a Kano yayin tarbar Abba Kabir Yusuf da ya sake komawa APC, inda ya bayyana komawar tasa a matsayin tarihi kuma abin alheri ga jam’iyyar da jihar baki ɗaya. “Za ka yi nasara a wa’adi na biyu a 2027. Mun tattauna da duk masu…
Read More
Za mu yi wa sojoji 16 shari’a kan yunƙurin juyin mulki a Nijeriya – Rundunar tsaro

Za mu yi wa sojoji 16 shari’a kan yunƙurin juyin mulki a Nijeriya – Rundunar tsaro

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Rundunar tsaron Nijeriya ta ce ta kammala binciken da take yi kan yunƙurin kifar da gwamnati a Nijeriya wanda aka yi a shekarar da ta gabata, inda ta ce nan gaba kaɗan za ta gabatar da sojoji a gaban kotun sojoji domin fuskantar shari'a. Wannan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da rundunar ta fitar a ranar Litinin, wanda wannan ne karo na farko da ta fito ta tabbatar da an yi yunƙurin juyin mulkin. A cikin sanarwar, wadda mai magana da yawun rundunar, Manjo Janar Samaila Uba ya fitar, ya ce tuni…
Read More
Za mu fara aiwatar da dokar taƙaita kashe kuɗin aure — Gwamnan Sakkwato

Za mu fara aiwatar da dokar taƙaita kashe kuɗin aure — Gwamnan Sakkwato

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Gwamnan Sakkwato Ahmed Aliyu ya sanar cewa nan ba da jimawa ba gwamnatinsa za ta fara aiwatar da dokar hana kashe kuɗi fiye da ƙima a harkokin aure a jihar. Da yake buɗe Masallacin Zawiyya Sheikh Aliyu Bunza da makarantar Islamiyya a Sakkwato, gwamnan ya ce, “Nan ba da dadewa ba za mu zauna da masu ruwa da tsaki a jiha domin sake duba dokar hana kashe kuɗi fiye da ƙima ga harkokin aure a jiha.” Ya bayyana cewa ɗaukar matakin ya zama wajibi ne ganin yadda masu shirin aure suke shan wahala a…
Read More
Za a haifi jarirai 700,000 a Kano bana – Rahoto

Za a haifi jarirai 700,000 a Kano bana – Rahoto

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Gwamnatin Kano ta ƙiyasta samun haihuwar jarirai tsakanin 600,000 zuwa 700,000 a shekarar 2026, lamarin da ta ce ka iya ƙara matsin lamba ga ɓangaren kiwon lafiyar jihar. Babban Sakataren Hukumar Kula da Asibitocin Kano, Dakta Mansur Mudi Nagoda ne ya bayyana hakan a ƙarshen mako yayin bikin yaye ɗalibai na farko na Kwalejin Kimiyyar Kiwon Lafiya da Fasaha ta Sardauna da aka gudanar a Kano. A cewarsa, an yi wannan ƙiyasi ne bisa ƙididdigar ƙaruwar yawan jama’a daga ƙidayar ’yan ƙasa da aka gudanar tun a 2006, wadda ta nuna cewa yawan al’ummar…
Read More
Nijeriya da Turkiyya sun ƙulla yarjejeniya kan yaƙi da ta’addanci

Nijeriya da Turkiyya sun ƙulla yarjejeniya kan yaƙi da ta’addanci

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Nijeriya da Turkiyya sun sanya hannu kan sabbin yarjejeniyoyin tsaro domin yaƙi da ta’addanci. An sanya hannu kan yarjejeniyoyin har guda tara ne a Ankara, babban birnin Turkiyya tare da Shugaban kasar, Recep Tayyip Erdogan yayin ziyarar da Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu yake yi a kasar. Yarjejeniyoyin sun shafi haɗin gwiwa a fannoni kamar manufofin ’yan gudun hijira, yaɗa labarai, ilimin gaba da sakandare, cinikayyar halal, harkar soja, da diflomasiyya. Haka kuma, kasashen sun amince su kafa wani Kwamitin Haɗin Gwiwar Tattalin Arziki da Kasuwanci (JETCO) a tsakanin su. Erdogan ya yi alkawarin…
Read More