ukarofi

12654 Posts
Makomar siyasa ba ta ta’allaƙa a hannun mutum ɗaya kacal – Gwamnatin Kano

Makomar siyasa ba ta ta’allaƙa a hannun mutum ɗaya kacal – Gwamnatin Kano

Daga RABIU SANUSI a Kano Gwamnatin Jihar Kano ta yi watsi da wasu kalamai da ake dangantawa da Injiniya Buba Galadima game da makomar siyasar Gwamna Abba Kabir Yusuf, tana mai cewa maganganun ba su da tushe kuma suna nuna rashin fahimta kan tarihin siyasar Kano da al’adun dimokuraɗiyyarta. A cikin wata sanarwa da Kwamishinan Yaɗa Labarai da Harkokin Cikin Gida, Kamarade Ibrahim Abdullahi Waiya, ya fitar a ranar Asabar, gwamnatin ta ce duk da cewa Sanata Rabiu Musa Kwankwaso babban jigo ne a siyasar jihar ba daidai ba ne a ɗaure makomar Kano da amincewa ko ikon mutum ɗaya.…
Read More
2026: Za a gudanar da bikin al’adu na ‘Rigata’ a Yawuri ranakun 4-7 ga watan Fabrairu

2026: Za a gudanar da bikin al’adu na ‘Rigata’ a Yawuri ranakun 4-7 ga watan Fabrairu

Daga JAMIL GULMA a Kebbi  Sakataren Gwamnatin Jihar Kebbi kuma shugaban kwamitin shirye-shiryen bikin al'adun da suka shafi tu'ammali da ruwa na  RIGATA da a ke yi shekara-shekara a garin Yawuri, Alhaji Yakubu Bala (Tafidan Yawuri, ya bayyana cewa gwamnatin jihar Kebbi ta ayyana ranakun 4 zuwa 7 ga watan Fabrairun wannan shekarar a matsayin ranakun gudanar da wannan bikin. Da yake jawabi, sakataren Gwamnatin ya bayyana cewar bikin al'adun gargajiyar Rigata daɗaɗɗen biki ne mai cike da tarihi a masarautar ta Yawuri dake jihar Kebbi. Haka kuma ya bayyana cewa bikin wani sashe ne na nuna irin al'adun gargajiyar…
Read More
Za mu bai wa Gwamna Abba goyon baya don haɓaka ci gaban Jihar Kano – Hon. Ado Tati

Za mu bai wa Gwamna Abba goyon baya don haɓaka ci gaban Jihar Kano – Hon. Ado Tati

Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano Shugaban Jami'ar Siyasa Gangariya na ƙasa, Hon. Ado Tati. Jugo a Jam'iyyar APC ya nuna mutuƙar jin daɗi da farin cikinsa tare da yi wa Allah godiya da ya nuna musu ranar da suka sake haɗuwa a tafiya ɗaya ta siyasa da Gwamnan jihar Kano a ƙarƙashin jam'iyyarsu ta APC. Ya bayyana haka ne da yake zantawa da 'yan jarida jim kaɗan bayan karɓar Gwamnan jihar Kano Injniya Abba Kabir Yusuf da jagororin  jam'iyyar suka yi a ranar Litinin bayan canza sheƙa da yayi daga NNPP zuwa cikinta.  Hon Ado Tati ya ƙara da cewa…
Read More
Ya kamata sojoji su ba ’yan Nijeriya haƙuri kan musanta yunƙurin juyin mulki – Falana

Ya kamata sojoji su ba ’yan Nijeriya haƙuri kan musanta yunƙurin juyin mulki – Falana

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Femi Falana, babban lauya mai kare haƙƙin ɗan adam, ya ce rundunar sojin Nijeriya ta ruɗi jama’a ta hanyar musanta zargin yunƙurin juyin mulki a baya, yana mai cewa ya dace su ba ’yan Nijeriya haƙuri. Falana ya bayyana hakan ne bayan da hedikwatar tsaro  ta tabbatar cewa akwai shirin kifar da gwamnatin Shugaba Bola Tinubu, tare da sanar da cewa za a gurfanar da wasu jami’an soji a gaban kwamitocin shari’a na soji. A watan Oktoban 2025 ne gwamnatin tarayya ta soke bikin faretin ranar ’yancin kai, lamarin da daga baya aka danganta…
Read More
Hukumar NHRC ta saurari ƙararrakin cin zarafi miliyan 3.7 a Nijeriya a 2025

Hukumar NHRC ta saurari ƙararrakin cin zarafi miliyan 3.7 a Nijeriya a 2025

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Hukumar kare haƙƙin bil’adama ta ƙasa NHRC ta bayyana cewa ta saurari ƙararrakin cin zarafi miliyan 3.7 a jihohi 36 da Babban Birnin Tarayya Abuja a shekarar 2025. Shugaban Hukumar Tony Ojukwu ya sanar da haka yayin sa yake gabatar da ayyukan da hukumar ta yi daga Janairu zuwa Disamba ta 2025. Ya ce kaso kaɗan ne daga cikin wanda hukumar ta saurara ne ta iya gudanar da bincike a kansu. Wani babban mashawarci kan illar cin zarafin mutane na Hukumar Hiliary Ogbonna a ranar Talata ya ce Hukumar ta kammala gudanar da bincike…
Read More
Kotu ta yi watsi da buƙatar sauya wa Kanu gidan yari

Kotu ta yi watsi da buƙatar sauya wa Kanu gidan yari

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Kotun ƙolin Tarayya da ke Abuja ta yi watsi da buƙatar da shugaban ƙungiyar ’yan awaren Biyafara (IPOB), Nnamdi Kanu, ya shigar na neman a sauya masa gidan yari daga Sakkwato. A zaman kotu da aka gudanar a ranar Talata, Mai Shari’a Omotosho ya ce tun a ranar 8 ga Disamba ya umurci Kanu da ya sanar da dukkan ɓangarorin da shari’ar ta shafa, wato Gwamnatin Tarayya da Hukumar Gyaran Hali, game da wannan buƙata. Alƙalin ya ce, “Na umurce ka da ka tabbatar an sanar da waɗanda shari’ar ta shafa, amma babu wata…
Read More
Gwamnatin Borno ta dawo da ’yan gudun hijira 3,000 daga Kamaru

Gwamnatin Borno ta dawo da ’yan gudun hijira 3,000 daga Kamaru

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Gwamnatin Jihar Borno ta fara dawo da ‘yan gudun hijira sama da 3,000 da suka tsallaka Kamaru tsawon shekaru fiye da 11 da suka gabata, a wani muhimmin mataki na ƙoƙarin dawo da rayuwar al’umma bayan rikicin da ya daɗe yana addabar yankin. Matakin na zuwa ne biyo bayan alƙawarin da Gwamnan Borno, Babagana Umara Zulum, ya yi a ranar 8 ga Disamba, 2025, kamar yadda Shugaban Kwamitin Kula da ’Yan Gudun Hijira na Jihar Borno, Injiniya Lawan Abba Wakilbe, ya bayyana. Wakilbe, wanda ya jagoranci tawagar gwamnatin jihar zuwa Kamaru, ya ce sun…
Read More
2027: APC za ta iya rasa kujerar gwamnan Nasarawa idan ta hana IGP Abubakar tikiti

2027: APC za ta iya rasa kujerar gwamnan Nasarawa idan ta hana IGP Abubakar tikiti

DAGA JOHN WADA a Lafia Wata ƙungiyar siyasa da aka fi sani da Nasarawa North Peace Assembly a turance da ke jihar Nasarawa ta buƙaci jam'iyar APC mai ci a jihar ta tabbatar ta bar zaɓen fitar da gwanin ta na kujerar gwamnan jihar na shekarar 2027 a bude ga duk wanda ya cancanta ba tare da yin la'kari da shiyar da ya fito ba. Ƙungiyar ta bayyana haka ne ta bakin shugaban ta Hon. Isah Nathaniel JP a lokacin wani gangamin wayar da kai na musamman da ta shirya wa ɗan takarar gwamnan jihar a inuwar jam'iyyar APC a…
Read More
Yara fiye da 1000 gidauniyar Gwagware ta ɗauki nauyin yi masu kaciya

Yara fiye da 1000 gidauniyar Gwagware ta ɗauki nauyin yi masu kaciya

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Shugaban ƙungiyar kwamred Mannir Suleiman ya faɗi haka a lokacin da yake duba gyaran sabon ofishin gidauniyar a Katsina. Ya ce nan bada jimawa ba gidauniyar za ta fara raba kayan yaran makarantun firamare a ƙananan hukumomi 34 da ke jihar. Kayan sun haɗa da rigunan makaranta, littafin rubutu da alli na rubuta da za su zagaya da kansu zuwa ƙananan hukumomin domin raba wa yara marasa ƙarfi da masu buƙata ta musamman inji Mannir. "Duk waɗannan ayyuka da Gidauniyar Musa Adamu Funtua ke yi daga ajihummu muke,"kwamred ya ce . Ya ce suna wannan…
Read More
Tinubu ya amince da fara haƙo ɗanyen mai a Ogun

Tinubu ya amince da fara haƙo ɗanyen mai a Ogun

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Jihar Ogun na daf da shiga sahun jerin jihohin da ke samar da danyen mai a Nijeriya bayan da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya amince da fara haƙo mai na kasuwanci a yankin Eba da ke ƙaramar Hukumar Ogun Waterside. Gwamnan jihar, Dapo Abiodun, ne ya bayyana hakan a ranar Alhamis yayin da yake karɓar baƙuncin Babban Kwamandan Rundunar Sojin Ruwa na Yankin Yamma, Rear Admiral Abubakar Abdullahi Mustapha, tare da manyan jami’ansa, a ofishinsa da ke Oke-Mosan a Abeokuta. Gwamnan ya kuma sanar da cewa Shugaba Tinubu ya bayar da umarnin gaggauta fara aikin gina…
Read More