Daga RABIU SANUSI a Kano
Gwamnatin Jihar Kano ta yi watsi da wasu kalamai da ake dangantawa da Injiniya Buba Galadima game da makomar siyasar Gwamna Abba Kabir Yusuf, tana mai cewa maganganun ba su da tushe kuma suna nuna rashin fahimta kan tarihin siyasar Kano da al’adun dimokuraɗiyyarta.
A cikin wata sanarwa da Kwamishinan Yaɗa Labarai da Harkokin Cikin Gida, Kamarade Ibrahim Abdullahi Waiya, ya fitar a ranar Asabar, gwamnatin ta ce duk da cewa Sanata Rabiu Musa Kwankwaso babban jigo ne a siyasar jihar ba daidai ba ne a ɗaure makomar Kano da amincewa ko ikon mutum ɗaya.
Sanarwar ta jaddada cewa siyasar Kano ta samo asali ne daga shiga-tsakani da halartar jama’a, wayewar kan al’umma da shugabanci bisa aiki, inda ta nuna cewa nasarar zaɓe a jihar ba ta taɓa dogaro kacokan da tsarin “uban gida” ko naɗawa ba.
A cewar sanarwar, abin mamaki ne Injiniya Galadima ya faɗi irin waɗannan maganganu, duk da cewa ya ci gajiyar tsarin shugabanci mai haɗa kowa da kowa na Gwamna Abba Kabir Yusuf.
Ta ce gwamnan ya naɗa shi Shugaban Majalisar Gudanarwa ta Kano State Polytechnic, domin bunƙasa cibiyar, duk da kasancewarsa ba ɗan asalin jihar Kano ba.
Sanarwar ta ƙara da cewa ya kamata a auna shugabanci da sakamakon aiki, ba wai da yawan magana ko jita-jita ba, tare da cewa wa’adin da ake magana a kai bai haifar da sauye-sauye ko gagarumin ci gaba ba a cibiyar.
“Siyasar Kano ta bambanta. Ikon siyasa a nan yana hannun masu zaɓe, ba na masu ɗaura siyasa ba. Aminci ana samunsa ne ta hanyar aiki, nagarta da amincewar jama’a,” inji sanarwar.
Gwamnatin ta kawo misalan tarihi da suka haɗa da zaben Malam Ibrahim Shekarau a matsayin Gwamna a 2003, ba tare da goyon bayan uban gida ba, da kuma komawar Sanata Kwankwaso mulki a 2011 wanda ta ce al’ummar Kano ne suka ba shi dama bisa tantance ayyukansa na baya, ba wai saboda nadawa ba.
Sanarwar ta kuma jaddada cewa Gwamna Abba Kabir Yusuf ya hau mulki ne da sahihin zaɓen al’ummar Kano, ya kare nasararsa ta hanyoyin doka, sannan ya fara aiwatar da tsare-tsaren mulki da suka haɗa da gyaran harkar ilimi, sake gina cibiyoyi, da dawo da amincewar jama’a ga gwamnati.
Ta ƙara da cewa iƙirarin cewa jagorancin gwamnan na kan “aro tasiri” ba shi da tushe, domin ikon siyasa a Kano yana tasowa ne daga hidima, ƙwarewa da nagartaccen shugabanci, ba dogaro na dindindin da wasu mutane ba.
Dangane da sauye-sauyen siyasa na baya-bayan nan, Kwamishinan ya bayyana cewa shawarar gwamnan ta samo asali ne daga rikice-rikicen cikin gida na jam’iyyar NNPP, sabanin shugabanci, da kuma shari’o’in da ke gaban kotuna, waɗanda suka haifar da rarrabuwar kai da rashin tabbas a cikin jam’iyyar.
“An yanke wannan shawara ne cikin kyakkyawar niyya, ba tare da wata manufa ta gaba ko ƙiyayya ba, domin kare zaman lafiya, haɗin kai da dorewar ci gaban Jihar Kano,” inji sanarwar.
A ƙarshe, Kwamishinan ya bayyana ƙwarin gwiwa cewa Gwamna Abba Kabir Yusuf zai samu wa’adi na biyu, tare da cewa kwarewa da koyon darasi daga aiki na ƙara wa jagora basira da nagarta a shugabanci.
Sanarwar ta rufe da ambaton ayoyin Alƙur’ani da Hadisan Annabi (SAW), inda ta jaddada dogaro ga ƙaddarar Allah a matsayin tushen falsafar siyasa da tafiyar da mulki a Kano.
