
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima ya ce gyare-gyaren da gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ke yi na samar da sakamakon da ake buƙata da dawo da yaƙinin amincewa da ƙasar daga ƙasashen waje.
A cewarsa, sabunta yardar ƙasashen waje ya ginu ne akan faɗaɗa shiga shirye-shirye da suka shafi ƙasashen da Nijeriya ke yi.
Shettima ya bayyana haka ne a jiya Alhamis, a taron ƙaddamar da shirin “Nigeria Procurement Certification Programme” da aka gudanar a ɗakin taro na Banquet da ke Fadar Shugaban Ƙasa a Abuja.
A wata sanrwa da Mai taimaka wa shugaban ƙasa akan harkokin yaɗa labarai na ofishin mataimakin shugaban ƙasa, Stanley Nkwocha ya fitar, ya ce Shettima ya samu wakilcin mataimakin shugaban ma’aikatan fadar shugaban ƙasa, Sanata Ibrahim Haɗejia.
Ya ce, samun yaƙinin daga waje ya sanya mutane da dama suke zaɓar yin kwasa-kwasan harkokin da suka shafi ƙwarewa a Nijeriya musamman shirye-shiryen takardun shaidar mallakar kadarorin gwamnati.
Ya bayyana cewa, ƙwarewa a fannin ga ƙasa kamar Nijeriya mai amfani da dabaru wajen gudanar da kadarorin gwamnati abu ne zai yi tasiri wajen aiwatar da ayyukan Sabunta Fata na gwamnatin Shugaba Bola Tinubu.
Ya ƙara da cewa, tsarin abu ne da zai iya inganta ƙarfin titina da layukan dogo, fannin kiwon lafiya, makaratu da jami’o’i da kuma amintuwar al’umma ga gwamnatinsu.
