ukarofi

12654 Posts
NELFUND ta ƙaryata rahotannin bogi kan fara karɓar bashin lamunin ɗalibai

NELFUND ta ƙaryata rahotannin bogi kan fara karɓar bashin lamunin ɗalibai

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Hukumar Ba da Lamunin Ilimi ta Nijeriya (NELFUND) ta fito ƙarara ta ƙaryata rahotannin da ke yawo a kafafen sada zumunta da wasu kafafen yaɗa labarai, waɗanda ke iƙirarin cewa an umurci zaliban da suka amfana da shirin lamunin ɗalibai da su fara biyan bashin. A cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Lahadi, wacce Daraktar Sadarwa ta Dabaru, Oseyemi Oluwatuyi ta sanya wa hannu, hukumar ta bayyana waɗannan rahotanni a matsayin ƙarya, ruɗani da kuma marasa tushe. Sanarwar ta ce, wannan bayani ya biyo bayan wata sanarwa da Shugaban Jami’ar Benin (UNIBEN), Farfesa Edoba…
Read More
Farashin ɗanyen mai ya tashi sakamakon rigingimun siyasa na duniya

Farashin ɗanyen mai ya tashi sakamakon rigingimun siyasa na duniya

Daga MAHDI MUSA MUHAMAMD Farashin mai ya ɗan ƙaru a kasuwar duniya a makon da ya gabata, inda alamun tashin hankali na siyasa, sauye-sauyen kasuwanci daga Amurka da ƙaruwar buƙatar mai daga ƙasar Chana suka ƙara ɗaure kasuwar. A ƙarshen mako, ɗanyen mai na Brent, ma’aunin farashin mai na duniy, ya tashi zuwa kusan dala 64.41 kowace ganga, ƙaruwa ta kusan kashi 1.3 idan aka kwatanta da makon da ya gabata. West Teɗas Intermediate (WTI) na Amurka ma ya yi ƙasa da ƙasa ya kai dala 60.31 kowace ganga, yana daidai da ƙaruwa ta kimanin kashi 1.8% a makon nan. …
Read More
Ba mu san abin da aka amince da shi a sabbin dokokin haraji ba – Makinde

Ba mu san abin da aka amince da shi a sabbin dokokin haraji ba – Makinde

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde, ya bayyana damuwa kan yadda aka tafiyar da sabbin dokokin haraji a Nijeriya, yana mai cewa har yanzu gwamnonin jihohi da ma jama’a ba su san takamaiman abin da Majalisar Tarayya ta amince da shi ko abin da aka rattaba wa hannu ya zama doka ba. Makinde ya bayyana hakan ne yayin wani taron jama’a inda ya ke jawabi ga tsohon Mataimakin Shugaban ƙasa, Yemi Osinbajo. A jawabinsa, gwamnan ya nuna rashin jin dadinsa kan yadda Osinbajo ya bar muƙami, yana mai cewa tsarin shugabanci na tattaunawa da sauraron juna da…
Read More
DSS ta daƙile yunƙurin ’yan fashin teku na sace jirgin ɗanyen mai a teku

DSS ta daƙile yunƙurin ’yan fashin teku na sace jirgin ɗanyen mai a teku

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS) ta kama wasu mutane biyu da ake zargi da kasancewa cikin ƙungiyar ’yan fashin teku a jihar Bayelsa, yayin da suke kammala shirinsu na sace wani jirgin ruwa ɗauke da ɗanyen mai a yankin Tekun Guinea. Majiyoyin tsaro sun bayyana cewa an cafke mutanen ne a wani otel da ke Titin Tenacious a unguwar Edepie da ke Yenagoa, babban birnin jihar Bayelsa. An bayyana sunayensu da Geoffrey Atizara mai shekaru 38 daga Aleibiri a ƙaramar hukumar Ekeremor ta jihar Bayelsa, da kuma Divine Kelechi Unueze mai shekaru 42 daga Nekede…
Read More
Ba za mu aminta da zaɓen da Amupitan zai jagoranta ba — Majalisar Shari’a

Ba za mu aminta da zaɓen da Amupitan zai jagoranta ba — Majalisar Shari’a

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Majalisar Shari’a ta Nijeriya (SCSN), ta bayyana cewa Musulmi ba za su aminta da kowane irin zaɓe da Hukumar Zaɓe ta ƙasa (INEC) za ta gudanar ƙarƙashin shugabanta, Farfesa Joash Amupitan ba. Majalisar ta bayyana haka ne yayin laccar shekara-shekara gabanin watan azumin Ramadan a Abuja, inda ta nemi a sauke Amupitan saboda rashin amincewa da adalci da gaskiyarsa. Shugaban majalisar, Sheikh Bashir Aliyu Umar, ya ce rashin amincewar ya samo asali ne, sakamakon zargin da Amupitan ya yi cewa ana yi wa Kiristoci kisan ƙare dangi a Nijeriya. “Muna buƙatar a sauke shugaban…
Read More
Kashi 11 ne kawai na makarantun Nijeriya ke da ruwa da banɗaki — UNICEF

Kashi 11 ne kawai na makarantun Nijeriya ke da ruwa da banɗaki — UNICEF

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Asusun Kula da ƙananan Yara na Majalisar ɗinkin Duniya (UNICEF), ya ce Nijeriya na fuskantar babbar barazana ga lafiyar jama’a da harkar ilimi, sakamakon kashi 11 cikin 100 ne kawai na makarantu a faɗin ƙasar da ke da ruwa da banɗaki mai tsafta. Babban jami’in UNICEF, Rahamah Farrah ne, ya bayyana haka yayin wani taron tattaunawa da kafafen yaɗa labarai da aka gudanar a Kano a ranar Laraba. Ya ce rashin samun tsaftataccen ruwa da banɗaki a makarantu da cibiyoyin lafiya na janyo ɗalibai, musamman ’yan mata rashin zuwa makaranta, tare da jefa miliyoyin…
Read More
KAZTA ta karɓi jakadun zaman lafiya daga WACORPAI

KAZTA ta karɓi jakadun zaman lafiya daga WACORPAI

Daga MUHAMMADU MUJITABA a Kano Kungiyar ’Yan Kasuwar ƙaramar Hukumar Kabo mazauna waje, wadda aka fi sani da Kabo Zone Traders Association (KAZTA), ta karɓi jakadun zaman lafiya daga cibiyar Wazobia Conflict Resolution and Peace Advocacy Initiative (WACORPAI), ƙarƙashin jagorancin Dakta Garba Sulaiman Marafa. An miƙa lambar yabo ne a wani babban taro da ƙungiyar KAZTA ta shirya a garin Kabo, Jihar Kano, a ranar Asabar da ta gabata, wanda ya samu halartar manyan baki daga sassa daban-daban na jihar. Daga cikin waɗanda aka karrama akwai Shugaban ƙaramar Hukumar Kabo, Hon. Lawan Najume; Sarkin Fulani Masanawa, Alhaji Yusuf Khan Umma;…
Read More
Kwamishinoni biyar da manyan jami’an gwamnatin Kano 10 sun ajiye muƙamansu

Kwamishinoni biyar da manyan jami’an gwamnatin Kano 10 sun ajiye muƙamansu

Daga SULEIMAN HUSSAINI D/KUDU a Kano Kwamishinoni biyar da wasu manyan jami’an gwamnatin Jihar Kano goma sun ajiye mukamansu, tare da jaddada mubaya’a da biyayya ga Jagoran Kwankwasiyya, Injiniya Rabiu Musa Kwankwaso, a yayin da rikicin siyasa ke kara daukar zafi tsakanin sa da Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf. Binciken da Manhaja ta gudanar ya nuna cewa daga cikin kwamishinonin da suka yi murabus akwai Mustapha Rabiu Kwankwaso, Kwamishinan Matasa da Wasanni; Dakta Yusuf Kofar Mata, Kwamishinan Kimiyya da Fasaha; Nasiru Sule Garo, Kwamishinan Ayyuka na Musamman; Adamu Kibiya, Kwamishinan Jinkai; da AVM Ibrahim Umar (mai ritaya), Kwamishinan…
Read More
Jam’iyyu 10 ne za su fafata a zaɓen cike gurbi a Kano — INEC

Jam’iyyu 10 ne za su fafata a zaɓen cike gurbi a Kano — INEC

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano  Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta ƙasa (INEC), ta sanar da cewa jam’iyyun siyasa guda 10 ne za su shiga zaɓen cike gurbi na Majalisar Dokokin Jihar Kano da za a gudanar a ranar 21 ga watan Fabrairu. Kwamishinan Zaɓe na Jihar Kano (REC), Ambasada Abdu Zango ne, ya bayyana hakan yayin taron masu ruwa da tsaki da aka gudanar a Kano. Ya ce hukumar ta karɓi sunayen ’yan takara daga jam’iyyu 10 domin zaɓen da za a yi a ƙananan hukumomin Birni da Ungogo. Jam’iyyun sun haɗa da APC, ADP, AAC, PRP, Dennis Labour…
Read More
Babu Kobon gwamnatu a shirin gina gidaje 3750 a Katsina – Falalu Bawale

Babu Kobon gwamnatu a shirin gina gidaje 3750 a Katsina – Falalu Bawale

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Shugaban ma'aikatan jihar Katsina, Malam Falalu Bawale ya faɗi haka ga manema labarai a Katsina. Ya bayyana cewa shi wannan shirin gina gidaje tare da haɗa su da harkokin noma da kiwo (aquaculture) babu kobon gwamnatin Katsina a ciki. Alhaji Bawale ya ce gwamnati ta rattaba hannu ne kan yarjejeniyar fahimta (MoU), da Cosmos Investment Nigeria Limited, tare da haɗin gwiwar ma’aikatar gidaje ta tarayya, gwamnatin Jihar Katsina da CESA Investment Limited, domin gina kusan gidaje 3750 a garuruwan kankiya da Raɗɗa domin shirin noma da kiwo. Ya ce, waɗannan kamfanoni da ke zaune a…
Read More