ukarofi

12654 Posts
RHISG ta naɗa Isah Kogi a matsayin jakadan zaman lafiya

RHISG ta naɗa Isah Kogi a matsayin jakadan zaman lafiya

DAGA JOHN WADA a Lafia Wata ƙungiya da ake kira Renewed Hope Support Group a turance ta naɗa shugaban al'umma a Karu jihar Nasarawa Alhaji Isah Kogi a matsayin Ambasadan zaman lafiya a shiyar Arewa ta tsakiya da birnin tarayya Abuja wato North Central Peace Ambassador a turance. Ƙungiyar ta Renewed Hope Independent Support Group Committee ta karrama basaraken da muƙamin ne a gidan gwamnatin jihar Nasarawa da ke Lafia babban birnin jihar a makon da ake ciki, inda abokan arziki da iyalai na kusa da basaraken da al'ummar ƙaramar hukumar ta Karu da sauran su suka halarta. Da yake…
Read More
Babu abin da aka sauya a cikin sabbin dokokin haraji — Akpabio 

Babu abin da aka sauya a cikin sabbin dokokin haraji — Akpabio 

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ya musanta iƙirarin cewa an sauya sabbin dokokin haraji bayan Majalisar Tarayya ta amince da su. Ya ce dokokin da Shugaba Bola Tinubu ya sanya wa hannu kuma aka wallafa a jaridar gwamnati su ne waɗanda ’yan majalisa suka amince da su. Akpabio, ya bayyana haka ne bayan wani ɗan Majalisar Tarayya, Abdussamad Dakuku, ya ce dokokin harajin da aka fitar sun bambanta da waɗanda majalisa ta amince da su. Sai dai Akpabio ya ce wannan iƙirari ba shi da tushe, inda ya jaddada cewa takardun da Majalisar Tarayya…
Read More
An kashe mutane 155 ta hanyar ɗaukar doka a hannu cikin shekaru 10 a Nijeriya – Amnesty

An kashe mutane 155 ta hanyar ɗaukar doka a hannu cikin shekaru 10 a Nijeriya – Amnesty

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  ƙungiyar kare haƙƙin bil'adama ta Amnesty International Nigeria ta nuna matuƙar damuwa kan yawaitar kashe-kashen jama’a ta hanyar ɗaukar doka a hannu a ƙasar nan, inda ta bayyana cewa ta tattara aƙalla mutane 155 cikin shekaru 10 da suka gabata aka kashe. Daraktan ƙasa na Amnesty International, Isa Sanusi, ne ya bayyana hakan yayin taron masu ruwa da tsaki da aka gudanar a Kano a ƙarƙashin gangamin Dakatar da Kisan Jama’a (End Mob ɓiolence Campaign). Sanusi ya ce bayanan da da aka tattara sun haɗa da kashe-kashe da suka samo asali daga zargin ɓatanci…
Read More
Sarki Sanusi ya naɗa Sarkin Zabarmawan Kano na farko

Sarki Sanusi ya naɗa Sarkin Zabarmawan Kano na farko

Daga MUHAMMADU MUJITABA a Kano Mai Martaba Sarkin Kano, Khalifa Malam Muhammadu Sanusi II, ya naɗa Barham Amadu Husaini Yahaya a matsayin Sarkin Zabarmawan Kano na farko a tarihin Zabarmawan Kano, waɗanda suka shafe fiye da shekaru 170 suna zaune a birnin Kano. Naɗin ya gudana ne a ranar Laraba da ta gabata a fadar Sarkin Kano, inda jama’a daga sassa daban-daban suka halarta domin shaida wannan muhimmin lamari na tarihi. Masana tarihi da shugabannin al’umma sun bayyana wannan naɗi a matsayin wata babbar alama ta haɗin kai da girmama kowane rukuni da ke zaune a Kano ba tare da…
Read More
APC ta ƙaddamar da rajistar katin mambobi ta intanet a Kano

APC ta ƙaddamar da rajistar katin mambobi ta intanet a Kano

Daga MUHAMMADU MUJITABA a Kano Jam’iyyar APC reshen Jihar Kano ta ƙaddamar da rijistar mambobinta ta zamani ta intanet, a wani taro da aka gudanar a dakin taro na Amani da ke Kano. Shugabannin jam’iyyar sun bayyana cewa sabon tsarin zai taimaka wajen sauƙaƙa rijistar mambobi tare da kawar da matsalolin da ke tattare da tsohon tsarin hannu. Shugaban jam’iyyar APC a jihar ya ce rijistar za ta ba da damar sanin sahihin yawan mambobin jam’iyyar a dukkan ƙananan hukumomi 44 na jihar. Ya ƙara da cewa tsarin zai taimaka wajen inganta tsare-tsaren jam’iyyar na zaɓe da kuma tallafa wa…
Read More
Rashin haɗin kai ke hana ci gaban malamai — Dakta Ahmad Gumi

Rashin haɗin kai ke hana ci gaban malamai — Dakta Ahmad Gumi

Daga MUHAMMADU MUJITABA a Kano Fitaccen malamin addinin Musulunci, Dakta Ahmad Mahmud Gumi, ya bayyana cewa rashin haɗin kai da ƙarancin fahimtar al’amuran zamani na daga cikin manyan dalilan da ke hana malamai taka rawar gani wajen ci gaban al’umma. Dakta Gumi ya bayyana hakan ne yayin wani taron nazari da Jami’ar Bayero Kano ta shirya domin tunawa da rayuwa da koyarwar marigayi Sheikh Abubakar Mahmud Gumi. Ya ce malamai na da rawar da za su taka wajen gyaran al’umma idan har suka haɗa kai suka rungumi ilimin zamani tare da na addini. Malamin ya jaddada cewa rarrabuwar kai a…
Read More
Kano: Hukumar KSCHCMA ta ta ƙaddamar da gangamin wayar da kai a kasuwannin Wudil da Getso

Kano: Hukumar KSCHCMA ta ta ƙaddamar da gangamin wayar da kai a kasuwannin Wudil da Getso

Daga SULEIMAN HUSSAINI D/KUDU a Kano A ƙoƙarinta na tabbatar da samun ingantaccen kiwon lafiya ga al’ummar Jihar Kano, Hukumar Kula da Tsarin Taimakon Kiwon Lafiya ta Jihar Kano (Kano State Contributory Health Care Management Agency (KSCHCMA) ta kaddamar da gangamin wayar da kai a kasuwannin Wudil da Getso, domin faɗaɗa shirin zuwa ga ‘yan kasuwa da sauran al’umma masu zaman kansu. Gangamin na daga cikin matakan da gwamnatin jihar Kano karkashin jagorancin Gwamna Alhaji Abba Kabir Yusuf ke dauka na ganin cewa kowane mazaunin jihar ya amfana da shirin taimakon kiwon lafiya, ba tare da la’akari da matsayin aikinsa…
Read More
Turji da yaransa sun kama ɗan bindigar da jagoranci yin sulhu a Katsina

Turji da yaransa sun kama ɗan bindigar da jagoranci yin sulhu a Katsina

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Kasurgumin ɗan bindigar nan, Bello Turji da yaransa sun kama Abdu Lankai, ɗan fashin dajin da taimaka wajen kawo zaman lafiya a ƙaramar Hukumar Jibiya, a Jihar Katsina. Sun kashe yaran Lankai bakwai sakamakon saɓani da ya ɓarke a tsakaninsu. Ba za mu aminta da zaɓen da Amupitan zai jagoranta ba — Majalisar Shari’a Kashi 11 ne kawai na makarantun Nijeriya ke da ruwa da banɗaki — UNICEF Wasu majiyoyi sun ce wasu daga mabiya Lankai sun jikkata, biyu kuma suna cikin mawuyacin hali a asibiti a Katsina. Lankai ya yi ƙaurin suna a…
Read More
Yadda Jonathan ya kore ni a matsayin Ministan Wasanni bisa ƙin sukar Saraki – Bolaji Abdullahi

Yadda Jonathan ya kore ni a matsayin Ministan Wasanni bisa ƙin sukar Saraki – Bolaji Abdullahi

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Tsohon Ministan Wasanni da Ci Gaban Matasa, Bolaji Abdullahi, ya bayyana yanayin da ya faru game da cire shi daga majalisar ministocin tsohon Shugaban ƙasa Goodluck Jonathan a shekarar 2014, yana mai cewa ƙin amincewa da ƙalubalantar tsohon Shugaban Majalisar Dattawa Bukola Saraki a bainar jama'a ya sa shi rasa aikinsa. Manhaja ya ruwaito cewa Abdullahi, wanda ya yi aiki a matsayin memba na Majalisar Zartarwa ta Tarayya da ke wakiltar Jihar Kwara a lokacin gwamnatin Jonathan, an sauke shi daga muƙaminsa a watan Maris na 2014 a lokacin da aka samu sauyin siyasa…
Read More
An kama abubuwan fashewa 954 da ake shirin kai wa ’yan ta’adda a Zamfara

An kama abubuwan fashewa 954 da ake shirin kai wa ’yan ta’adda a Zamfara

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Rundunar ’Yan Sandan Jihar Zamfara ta kama mota da ke ɗauke da abubuwan fashewa guda 954 da ake zargin ana shirin kai su ga ’yan ta’adda da ke jihar don haɗa boma-bomai. Mai magana da yawun rundunar a jihar, Yazid Abubakar, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa a ranar Laraba, inda ya ce an kuma kama direban motar mai suna Mustapha Mohammad. Abubakar ya ce jami’an rundunar na musamman kan yaƙi da haƙar ma’adinai ba bisa ƙa’ida ba ne suka gudanar da wannan samame bayan samun sahihan bayanan sirri. A cewarsa: “A ranar…
Read More