Kano: Hukumar KSCHCMA ta ta ƙaddamar da gangamin wayar da kai a kasuwannin Wudil da Getso

Spread the love

Daga SULEIMAN HUSSAINI D/KUDU a Kano

A ƙoƙarinta na tabbatar da samun ingantaccen kiwon lafiya ga al’ummar Jihar Kano, Hukumar Kula da Tsarin Taimakon Kiwon Lafiya ta Jihar Kano (Kano State Contributory Health Care Management Agency (KSCHCMA) ta kaddamar da gangamin wayar da kai a kasuwannin Wudil da Getso, domin faɗaɗa shirin zuwa ga ‘yan kasuwa da sauran al’umma masu zaman kansu.

Gangamin na daga cikin matakan da gwamnatin jihar Kano karkashin jagorancin Gwamna Alhaji Abba Kabir Yusuf ke dauka na ganin cewa kowane mazaunin jihar ya amfana da shirin taimakon kiwon lafiya, ba tare da la’akari da matsayin aikinsa ba.

Tun asali, tsohuwar gwamnatin Dr. Abdullahi Umar Ganduje ce ta assasa shirin taimakon kiwon lafiya, wanda aka fi mayar da hankali kan ma’aikatan gwamnati, inda ake cire wani kaso daga albashinsu domin samun saukin kudin magani. A ƙarƙashin tsarin, mai rijista zai biya kashi goma cikin dari na kuɗin magani, yayin da gwamnati ke daukar nauyin kashi casa’in.

Sai dai, ganin muhimmancin shirin da kuma irin ribar da yake da ita ga al’umma, Gwamna Abba Kabir Yusuf ya bayar da umarnin fadada shirin domin ya haɗa da ‘yan kasuwa, ma’aikatan kamfanoni masu zaman kansu da sauran al’ummar jihar.

A wannan dalili ne Hukumar, ƙarƙashin jagorancin Babbar Sakatare a Ma’aikatar Lafiya, Dakta Rahila Aliyu Mukhtar, ta ɓullo da sabon tsari na shiga lungu da saƙo da kasuwanni domin wayar da kan jama’a kai tsaye.

Gangamin ya fara ne a Kasuwar Shanu ta Wudil a ranar Juma’a, sannan ya wuce zuwa Kasuwar Shanu ta Getso da ke Karamar Hukumar Gwarzo. A yayin ziyarar, Dakta Rahila ta kai ziyara ta girmamawa ga Hakimin Wudil, Makaman Kano, wanda Dan Ruwatan Makaman Wudil, Alhaji Sarki Ibrahim, ya wakilta, da kuma Sarkin Getso, Alhaji Bello Ibrahim, domin neman albarka da hadin kai.

Ta bayyana cewa duk da kokarin da hukumar ke yi ta kafafen sadarwa na zamani, an ga dacewar sauka kasa domin isar da sakon shirin kai tsaye ga al’umma, musamman ‘yan kasuwa da masu karamin karfi.

Dakta Rahila ta jaddada cewa shirin ba na ma’aikatan gwamnati kadai ba ne, kowane mazaunin jihar Kano na da damar shiga shirin, ta hanyar yin rijista da hukumar da zaben asibitin da ya fi dacewa da shi, na gwamnati ko mai zaman kansa.

A nasu jawaban, Dan Ruwatan Makaman Wudil da Sarkin Getso sun tabbatar da cikakken goyon bayansu ga shirin, tare da alkawarin amfani da dukkan hanyoyin da suke da su domin sanar da jama’arsu amfanin shirin.

Haka kuma shugabannin kasuwannin Wudil da Getso sun yaba da wannan shiri, inda suka bayyana shi a matsayin gagarumin ci gaba ga walwalar ‘yan kasuwa.

By ukarofi