30
Jan
Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Sanata Abdul Ahmed Ningi, mai wakiltar Bauchi ta Tsakiya, ya bayyana damuwa kan yadda Amurka ta kai hare-haren sama kan wuraren ‘yan ta’adda a Jihar Sokoto ba tare da neman izini ko tuntuɓar majalisar dokokin ƙasar ba kafin ta kai harin. Sanatan ya ce "hakan ya saɓa wa ikon ƙasar tare da karya tsarin sa ido na majalisa kan al’amuran tsaro." Sanata Ningi ya tayar da batun ne a zauren majalisar dattawa inda ya ce "majalisar dokoki na da rawar da doka ta tanada a harkokin tsaro da kuma shigar sojojin ƙasashen waje, amma…
