ukarofi

12654 Posts
An fitar da sanawar bayan taron Ranar Marubuta Hausa ta Duniya

An fitar da sanawar bayan taron Ranar Marubuta Hausa ta Duniya

Daga NASIR S. GWANGWAZO a Abuja Taron Ranar Marubuta Hausa ta Duniya ya gudana cikin nasara a ranar 31/12/2025 a garin Dutse Jihar Jigawa, inda ya haɗa marubuta, manazarta, malamai, ɗalibai, da wakilan gwamnatoci daga sassa daban-daban na Nijeriya da maƙwabtanta. Taron ya ƙara jaddada muhimmancin rubutun Hausa a ƙarni na 21, musamman a fuskokin tsaro, tattalin arziki, al’adu, da ci gaban al’umma. Muhimman abubuwan da taron ya tattauna: 1. ƙalubalen Tsaro da Al’adar Karatu: An jaddada cewa duk da ƙalubalen rashin tsaro, akwai babbar matsala ta raguwar al’adar karatu musamman a tsakanin matasa, wadda ke buƙatar tsayuwar daka. An…
Read More
Burina shine fito da daraja da mutuncin matan Arewa – Hajara Kabir

Burina shine fito da daraja da mutuncin matan Arewa – Hajara Kabir

Daga NASIR S. GWANGWAZO a Abuja Kamar yadda ya gabata a kundin farko (na shekarar 2010), wannan kundin na gaba ya ƙunshi jerin muƙaloli masu alaƙa da juna amma mabambanta, waɗanda ke bayani kan mata daga fannoni daban-daban na al’umma, tare da bambancin matakan nasara daga Arewacin Nijeriya. (Northern Women Development: A Historical and Contemporary Perspective on Northern Nigerian Women) yana nazartar rikitarwa da ke tattare da nasarorin da mata suka samu cikin yanayin al’adu da addini na Arewacin Nijeriya, na tarihi da na zamani. Lokacin da ƙwararrun marubuta mata, masana da ‘yan jarida irin su Hajara Muhammad Kabir suka raba…
Read More
Farfesa Abdullahi Yamma ya ƙalubalanci shugabanni su yi aiki da rantsuwa da suka ɗauka

Farfesa Abdullahi Yamma ya ƙalubalanci shugabanni su yi aiki da rantsuwa da suka ɗauka

DAGA JOHN WADA, a Lafia Prof. Abdullahi Mohammed Yamma na dandalin siyasar kafafen siyasa a babban jami'ar Jihar Nasarawa da ke birnin Keffi, ya buƙaci shugabanni a duka matakai da su yi kamar yadda suka yi alƙawari a lokacin da ake rantsar da su. Farfesan ya bayyana hakan ne a lokacin da yake gabatar da wata laccar jami'ar NSUK da ake yi a kowanne shekara, wadda aka gabatar a babban ɗakin taro na jami’ar ranar Laraba na mako da ake ciki mai taken "Layi na shugabanci mai daraja: Yin misali da ƙa’idoji na gudanar da tasirin Nijeriya". A cewar Prof.…
Read More
Yan bindiga sun kashe ‘yan sandan kwantar da tarzoma uku a Katsina

Yan bindiga sun kashe ‘yan sandan kwantar da tarzoma uku a Katsina

' Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Lamarin ya faru na a ƙauyen Guga da ke ƙaramar hukumar Bakori a lokacin da 'yan sandan ke gudanar da sintiri a ƙauyen. 'Yan bindigan ne suka buɗewa yan sandan wuta ba zato ba tsammani inda nan take suka kashe 'yan sandan uku tare da raunana biyu. Jami'in hulɗa da jama'a na rundunar 'yan sanda a Katsina DSP Abubakar Sadiq Aliyu ya tabbatar da faruwar lamarin. Ya bayyana cewa rundunar 'yan sanda na nan na bincike. Kofur Usman Musa ya bada sunayen 'yan sandan da aka kashe da yace akwai ASP Abubakar Abdullahi,Sifeto Umar…
Read More
Kallon fina-finan Hausa na taimaka wa yawaitar kashe-kashe – Shugaban Izala na Gombe

Kallon fina-finan Hausa na taimaka wa yawaitar kashe-kashe – Shugaban Izala na Gombe

Daga ABUBAKAR A. BOLARI a Gombe Yawaitar kashe-kashe da tashe-tashen hankula a cikin al’umma na da alaƙa da tasirin kallon wasu fina-finan Hausa da ke ɗauke da nuna tashin hankali, inji Shugaban ƙungiyar Jama’atu Izalatil Bid’ah Wa Iƙamatissunnah (Izala) a Jihar Gombe, Injiniya Salisu Muhammad Gombe. Ya bayyana hakan ne yayin taron bitar da ƙungiyar Izala ta shirya wa malamai da limamai sama da 750 domin shirin tafsirin watan Ramadan na shekarar 2026 a faɗin jihar.Salisu Gombe ya ce a wannan lokaci al’umma na buƙatar jagorancin malamai, saboda haka ya zama wajibi a shirya su yadda za su fuskanci jama’a…
Read More
Ƙungiyar tsangaya ta samar wa malaman tsangaya cigaba a ƙasa

Ƙungiyar tsangaya ta samar wa malaman tsangaya cigaba a ƙasa

Ƙungiyar Tsangaya ta samar wa malaman tsangaya cigaba a ƙasa tare da Gwani Ibrahim Mai Bindiga Hadejia . Taron da aka gudanar da shi yau Talata 27 ga watan Janairu a ɗakin taron na Naicon Luxury Hotel dake Abuja ya samu halarta manya Shaihunnai da gwanenyen Al'qurani mai girma daga sassan daban-daban na faɗin kasar nan. Manya gwanayen da shaihunnai Al'qurani mai girma sun bayyana taron a matsayin wani babban cigaba a ƙungiyar tsangaya wanda naɗa Gwani Ibrahim Mai Bindiga zai samarwa Almajirai damar-maki a matakai daban-daban. Haka kuma gwanayen sun bayyana cewa ƙungiyar Tsangaya kullum burinta shine fafutikar nemawa…
Read More
Gwamnatin Kano ta jinjinawa Kashim Shettima kan tallafa wa mahaddata Alƙur’ani

Gwamnatin Kano ta jinjinawa Kashim Shettima kan tallafa wa mahaddata Alƙur’ani

Daga RABI'U SANUSI a Kano Gwamnatin Jihar Kano ta jinjinawa mataimakin shugaban ƙasa, Sanata Kashim Shettima, da Uwargidansa, Hajiya Nana Kashim Shettima, bisa irin gagarumar gudunmawar da suka bayar wajen tallafawa mahaddata Alƙur’ani. Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya bayyana hakan ne yayin bikin karrama mahaddata Alƙur’ani da suka wakilci ƙasa a wata gasa ta ƙasa da ƙasa, inda ya ce irin wannan tallafi na ƙarfafa addini da ilimi abin a yaba ne kuma ya dace shugabanni su yi koyi da shi. A yayin taron, gwamnan ya sanar da cewa za a ɗauki nauyin cigaba da karatun Hafsat…
Read More
Duk magoya bayana su bi Gwamnan Kano Abba – Sanata Barau Maliya

Duk magoya bayana su bi Gwamnan Kano Abba – Sanata Barau Maliya

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano Mataimakin shugaban Majalisar Dattijai ta Nijeriya Sanata Barau I Jibrin ya yi kira ga duk magoya bayansa su goyi bayan gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf a zaɓen 2027. Sanata Barau wanda shi ne ke wakiltar mazaɓar Kano ta Arewa a majalisar dattijan Nijeriya ya bayyana haka ne a ranar Litinin, yayin da yake jawabi a gidan gwamnatin Kano, lokacin da Gwamna Abba ya shiga jam'iyyar APC. Kalaman ɗan majlisar, wanda ya yi amfani da kalmar 4+4, ma'ana yin gwamna wa'adi biyu, na nufin cewa ya jingine buƙatarsa ta takarar gwamna a zaɓe mai zuwa. Barau…
Read More
Me ya janyo yaƙin duniya na ɗaya?

Me ya janyo yaƙin duniya na ɗaya?

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD A tarihi yaƙin duniya na farko wanda a Turance ake kira da ‘World War I’ ko ‘First World War’ wani yaƙi ne wanda manyan ƙasashen duniya, musamman na nahiyar Turai (Europe) irin su Ingila (Britain), France, Germany, Russia, Austria-Hungary, Russia, Daular Ottoman ta Turkiya (Ottoman Empire), da kuma Amurka suka fafata, a tsakanin shekarun 1914 zuwa 1919. A bisa tarihi, ya tabbata cewa zuwa shekarar 1900 wato farkon ƙarni na 21, ƙasashen yammacin Turai irin su Ingila, France, Germany, Spain, Portugal, Netherlands, da kuma Italy sun kai ga cikakken ci gaban tattalin arziki (economic development) da…
Read More
Muhimman hanyoyi 10 na kula da fata

Muhimman hanyoyi 10 na kula da fata

Daga AISHA ASAS Mai karatu barkanmu da sake kasancewa a wannan shafi na Kwalliya. Sannunku da jimirin bibiyar mu. A wannan karon shafin zai yi duba ne kan sha'anin fata wadda ta kasance uwa ga kwalliya, kyanta kan yi tasiri kan kowacce kwalliya, idan kuwa ba ta samu kulawar da ta dace ba ba ta yadda kwalliya zata yi armashi. Kula da fata ba kawai wanke ta da shafa mata mai ne kawai ba, za mu iya cewa wata cikakkiyar al'ada ce da ya kamata a mayar jiki, wadda ta haɗa da tsafatacce fata cikin hikima, tsaftar muhalli, da zaɓaɓɓun…
Read More