ukarofi

12664 Posts
Iya sojojin da ke tsaron Seyi Tinubu sun isa su samar da tsaro a Benin – Soyinka

Iya sojojin da ke tsaron Seyi Tinubu sun isa su samar da tsaro a Benin – Soyinka

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Marubuci kuma mai lambar yabo ta Nobel, Wole Soyinka, ya ce kamata ya yi Shugaban ƙasa Bola Tinubu ya tura ɗansa, Seyi Tinubu, zuwa Jamhuriyar Benin domin “kwantar da” yunƙurin juyin mulki da bai yi nasara ba. Soyinka ya soki matakin Tinubu na tura dakarun rundunar Sojojin Sama ta Nijeriya zuwa Jamhuriyar Benin bayan yunƙurin juyin mulki da aka yi domin kifar da Shugaba Patrice Talon daga mulki. Ya yi wannan jawabi ne a bikin bayar da kyaututtuka na shekara karo na 20 da Cibiyar Binciken Kwakwaf ta Wole Soyinka (WSCIJ) ta shirya a…
Read More
Rashin Tsaro: Gwamnatin Tarayya ta gaza — Kwankwaso

Rashin Tsaro: Gwamnatin Tarayya ta gaza — Kwankwaso

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Tsohon Gwamnan Jihar Kano kuma dan takarar shugaban ƙasa na Jam’iyyar NNPP, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya ce Gwamnatin Tarayya ta gaza wajen shawo kan matsalar tsaro da ke ƙara ta’azzara a faɗin kasar nan, lamarin da ya ce yana barazana ga haɗin kan ƙasa da zaman lafiya. Kwankwaso, wanda ya taɓa zama Ministan Tsaro, ya bayyana a shafinsa na Facebook cewa yana da “damuwa ta musamman” kan yadda gwamnati ta kasa daƙile ayyukan ’yan ta’adda, ’yan bindiga, rikice-rikicen ƙabilanci da kuma yaɗuwar makamai ba tare da kulawa ba. Ya ce abin da ya…
Read More
Yadda Gwamnonin Arewa suka kafa asusun magance matsalar tsaron yankin

Yadda Gwamnonin Arewa suka kafa asusun magance matsalar tsaron yankin

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Kungiyar Gwamnonin Arewa ta kafa asusun magance matsalar tsaro tare da tsara kowacce jiha za ta riƙa ba da Naira biliyan 1 a kowanne wata kamar yadda Blueprint Manhaja ta rawaito. Gwamnan Nassarawa kuma shugaban kungiyar gwamnonin yankin Arewa ta tsakiya, Abdullahi Sule, ne ya bayyana haka a yayin zaman majalisar zartarwa ta jihar a Lafiya. A cewar Gwamna Sule, an ɗauki wannan mataki ne a zaman da ƙungiyar gwamnonin Arewa ta yi na ƙarshe a Kaduna. Ya ce, za a yi amfani da kuɗi ne wajen sayen manyan makamai Ga jami’an tsaro da…
Read More
Yadda aka kammala taron bajekolin Kano karo na 46 cikin nasara 

Yadda aka kammala taron bajekolin Kano karo na 46 cikin nasara 

Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano  An gudanar da bikin rufe bajekoli na duniya Karo na 46 da Cibiyar Kasuwanci da Masana'antu ta Jihar Kano ƙarƙashin jagorancin Ambassada Usman Darma suka gudanar. A yayin  taron rufe bajekolin da aka gudanar a yammacin ranar Asabar ya samu halartar Sanatan Kano ta tsakiya Hon. Rufa'i Sani Hanga da Kwamishinan kasuwanci na jihar Kano Wada Sagagi. Haka kuma wakilai daga masarautun Kano da shugabannin cibiyoyin kasuwanci na jihohin  Kaduna, Zamfara da Gombe da sauran hukumomin gwamnati da 'yan kasuwa. Da yake jawabi a yayin rufe taron shugaban cibiyar Kasuwanci da masana'antu na jihar Kano,…
Read More
Nijeriya da Saudiyya sun ƙulla yarjejeniyar tsaro domin ƙarfafa haɗin gwiwar soja

Nijeriya da Saudiyya sun ƙulla yarjejeniyar tsaro domin ƙarfafa haɗin gwiwar soja

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Nijeriya da Saudiyya sun rattaɓa hannu kan muhimmin yarjejeniya a ranar Talata domin zurfafa haɗin gwiwar tsaro da soja tsakanin ƙasashen biyu. Wannan mataki na zuwa ne a lokacin da Nijeriya ke fama da ƙalubalen tsaro iri-iri, tana kuma neman ƙarin goyon bayan ƙasashen duniya don farfaɗo da ƙarfinta na soja. Ministan ƙaramin Harkokin Tsaro na Nijeriya, Bello Matawalle, da Mataimakin Ministan Tsaron Saudiyya mai kula da Harkokin Gudanarwa, Dr Khaled Al-Biyari, su ne suka sanya hannu kan yarjejeniyar a Abuja. A cewar sanarwar da Blueprint Manhaja ta gani, wacce Jami’ar Hulɗa da Jama’a…
Read More
IBB ga shugabannin Arewa: Ku yi koyi da hangen nesan Hassan Katsina na son zaman lafiya haɗin kai

IBB ga shugabannin Arewa: Ku yi koyi da hangen nesan Hassan Katsina na son zaman lafiya haɗin kai

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Tsohon shugaban mulkin soja, Janar Ibrahim Babangida, ya yi kira ga shugabannin Arewa da su rungumi hangen nesa na Marigayi Janar Hassan Usman Katsina na zaman lafiya, haɗin kai da kuma dogaro da kai. Babangida ya yi wannan kira ne a lokacin taron tunawa da Marigayi Janar Hassan Usman Katsina karo na biyu wanda aka shirya a Kaduna wanda New ɓision Deɓelopment Initiatiɓe, NEɓDI, ta shirya. A cewarsa, yin tunani kan sadaukarwar shugabanni kamar Janar Usman Katsina ya dace, musamman ganin yadda Nijeriya ke ci gaba da fama da ƙalubale da dama na zamantakewa…
Read More
Ganduje ne ya sa aka kamani saboda bincikensa – Muhuyi

Ganduje ne ya sa aka kamani saboda bincikensa – Muhuyi

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Tsohon shugaban Hukumar ƙorafe-ƙorafen Jama'a da Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa ta Jihar Kano, PCACC, Muhuyi Magaji Rimin Gado, ya yi zargin cewa tsohon gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ne ya yi sanadiyyar kama shi da aka yi ranar Juma'a da jami'an 'yan sandan Nijeriya suka yi. 'Yan sanda ɗauke da makamai sun kama Magaji a ofishinsa na Kano, inda suka shaida masa cewa suna aiki bisa umarnin Sufeto Janar na 'Yan sandan. Da yake magana da DCL Hausa jim kaɗan bayan an sake shi a ranar Asabar, tsohon shugaban PCACC ya…
Read More
Fulani na zargin ‘yan sa-kai da cin zali a Zamfara

Fulani na zargin ‘yan sa-kai da cin zali a Zamfara

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Kungiyoyin Fulani a yankin arewacin Nijeriya na nuna damuwa game da abin da suka kira jama'u da ake yi wa al'ummarsu sanadiyyar matsalar tsaro da ake fama da ita a yankin. Suna zargin cewa ana zaluntar 'yan ƙabilar ta Fulani wadanda ba su, ba su gani ba ta hanyar cin mutuncinsu da kona masu rugage da kwashewa ko ma karkashe masu dabbobi, baya ga kisan gilla da ake yi masu a wurare da dama. Hakan kuwa yana hana su walwala da shiga garuruwa, da kasuwanni da cudanya da sauran jama'a. ƙorafi na baya-baya nan…
Read More
Yadda wani gurgu ya ƙera mota a Kano

Yadda wani gurgu ya ƙera mota a Kano

Daga SULAIMAN HUSSAINI D/KUDU a Kano Wani matashin gurgu daga Unguwar Rijiyar Lemo a ƙaramar Hukumar Dala, Ibrahim Abubakar mai shekaru kimanin 32, ya nuna bajintarsa a bikin rufe bajekolin bana ta hanyar gabatar da wata mota da ya ƙera da hannunsa wacce ke ɗaukar mutum huɗu. Ibrahim ya ce tun yana makaranta yake sha’awar zama injiniya, amma bai samu damar ci gaba da karatu ba bayan kammala sakandare. Ya fara ƙere-ƙere ne tun yana ƙarami, inda yakan gyara kekensa na zuwa makaranta har ya koyi amfani da ƙarafuna da walda. A cewarsa, motar da ya ƙera tana ɗauke da…
Read More
Jihar Kano ta ƙulla alaƙar cinikayya da wasu ƙasashen duniya – Darma

Jihar Kano ta ƙulla alaƙar cinikayya da wasu ƙasashen duniya – Darma

Daga SULAIMAN HUSSAINI D/KUDU a Kano A ƙoƙarinta na bunƙasa tattalin arzikinta da faɗaɗa hanyoyin samun kuɗaɗen shiga, gwamnatin Jihar Kano ta ƙulla sabuwar yarjejeniyar kasuwanci da wasu ƙasashen duniya, domin ƙara danƙon zumuncin cinikayya da masana’antu.  ƙasashen da suka shiga cikin yarjejeniyar sun haɗa da Bangladesh, Rwanda, Ghana da wasu manyan ƙasashen duniya masu ƙarfin tattalin arzikin masana’antu. Shugaban Cibiyar Kasuwanci, Ma’adanai, Masana’antu da Aikin Noma ta Jihar Kano, Ambassador Usman Hassan Darma ne ya bayyana haka yayin ganawarsa da manema labarai bayan rufe bikin bajekolin bana karo na 47. Darma ya ce wannan shekarar ta samu gagarumar nasara…
Read More