12
Dec
Daga SULAIMAN HUSSAINI D/KUDU a Kano An yaba wa Gwamnan Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, bisa ɗaukar fannin ilimi da muhimmanci ta hanyar gyaran makarantu, samar da kayan koyo da koyarwa da sauran muhimman abubuwan ci gaban ilimi. Hajiya Rabiya Ahmad Muhammad, Darakta mai kula da ingancin ilimi ta hukumar kula da manyan makarantun sakandare ta kasa, ta bayyana haka yayin rangadin makarantu biyar da hukumar ta gudanar a Kano. Makarantun sun haɗa da: FGC Kano da GGC Dala da WTC Fanfo da KTC Sabon Gari da Makarantar Al-Azahar (mai zaman kanta) Ta ce sun duba kayayyakin koyarwa, adadin malamai,…
