ukarofi

12664 Posts
Ƙudurin sake fasalin dokokin haraji

Ƙudurin sake fasalin dokokin haraji

A wani lokaci da tattalin arzikin ƙasa ke buƙatar daidaito, gaskiya da tsarin da ya dace, gwamnatin Shugaba Bola Ahmad Tinubu ta ɗauki mataki mai nisa wajen sake fasalin dokokin haraji domin farfaɗo da tattalin arziki da kuma dawo da amincewar jama’a ga yadda ake gudanar da haraji a Nijeriya. Wannan sabon tsarin, wanda zai fara aiki a 2026, wani babban lamari ne da ya tsaya kan gaskiya, sauƙi da kare al’ummar ƙasa — musamman masu ƙaramin ƙarfi. A karin gaskiya, tsarin haraji a baya ya yi nauyi ga ‘yan kasuwa, ya ƙara ruɗani ga zuba jari, ya hana yawancin…
Read More
Tana ƙasa tana dabo kan rikicin cikin gidan APC a Kebbi 

Tana ƙasa tana dabo kan rikicin cikin gidan APC a Kebbi 

Daga JAMIL GULMA a Kebbi  A duk lokacin da mutane biyu ko fiye da haka suke neman abu ɗaya kuma ba za a iya raba shi ba, to ba shakka kowane cikionsu yana iya yin duk yadda zai yi ya kai gaci, don haka ba shakka akwai gumurzu. Jam'iyyar APC mai mulki a Jihar Kebbi tana kusa  tsunduma cikin rikicin cikin gida da ke iya kai ta ga rugujewa, saboda a kullum ’yan takarar neman makamai daban-daban tun kama daga majalisar dokoki ta jiha zuwa Majalisar Wakilai ta Tarayya sai bayyana su ke yi daga sassa daban-daban na jihar, inda…
Read More
Tsarin siyasa ne ya lalata makomar Nijeriya, inji Sarki Sanusi

Tsarin siyasa ne ya lalata makomar Nijeriya, inji Sarki Sanusi

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano  Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, ya zargi manyan 'yan siyasar Nijeriya da gaza yi wa ƙasa aiki, yana mai cewa suna naushin cigaban al’umma ta hanyar fifita kansu a kan buƙatun jama’a. Sarkin na wannan jawabi ne a bikin cika shekaru 15 da kafuwar Enough is Enough (EiE) Nigeria a Lagos, ranar Laraba, Sanusi ya bayyana cewa Nijeriya na ci gaba da rasa muhimman damar bunkasuwa saboda yadda wasu ke ɗaukar muƙaman gwamnati a matsayin “gadon gidansu"  amanar al’umma ba. A cewarsa, yawancin shugabannin siyasa suna sa buƙatunsu da na iyalansu a gaba fiye da…
Read More
Ba mu yarda da kafa sabuwar hukumar Hisba a Kano ba – Farfesa Mai-Bushira 

Ba mu yarda da kafa sabuwar hukumar Hisba a Kano ba – Farfesa Mai-Bushira 

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano  Tsofaffin shugabannin Hukumar Hisbah ta Jihar Kano sun bayyana matsayinsu kan batun kafa wata sabuwar hukumar Hisbah mai zaman kanta, inda suka nuna cewa ba za su amince da hakan ba, tare da gargaɗin cewa bai kamata a siyasantar da hukumar ba. Sun bayyana wannan matsaya ne yayin wani taron manema labarai da aka gudanar a ɗakin taron Cibiyar ‘Yan Jarida ta Jihar Kano ranar Alhamis. Da yake jawabi a madadinsu, Farfesa Mai Bushira, ya ce an samu rahotannin cewa an sallami wasu jami’an Hisbah ba tare da bin ƙa’ida ba, lamarin da ya haifar…
Read More
Gwamna Lawal ya ƙaddamar da Tsarin Bunƙasa Zamfara na shekaru 10

Gwamna Lawal ya ƙaddamar da Tsarin Bunƙasa Zamfara na shekaru 10

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Gwamna Dauda Lawal ya ƙaddamar da sabon Tsarin Bunƙasa Jihar Zamfara na 2025 zuwa 2034, wani tsari mai dogon zango da aka gina bisa bincike, bayanai, da tattaunawa da ƙwararru domin sake fasalin jihar a shekaru goma masu zuwa. An gabatar da shirin ne a sakateriyar JB Yakubu da ke Gusau a ranar Juma’a, a wani taron da ya tattaro manyan jami’an gwamnati, shugabannin gargajiya da na addini, da ƙwararrun masana a fannin bunƙasar tattalin arziki. A cewar mai magana da yawun gwamnan, Sulaiman Bala Idris, gwamnatin jihar ta ɗauki kwamitin KPMG a matsayin babban mai…
Read More
Nijeriya ta fara kai-komon karɓo sojoji da jirginta da ke tsare a Burkina Faso

Nijeriya ta fara kai-komon karɓo sojoji da jirginta da ke tsare a Burkina Faso

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Gwamnatin Tarayya ta shiga tattaunawar diflomasiyya ta matakai mafi girma domin ganin an saki jirgin saman rundunar sojin sama ta NIjeriya, NAF C-130, da kuma sojoji 11 da gwamnatin sojin Burkina Faso ta tsare har tsawon kwana uku a jere. Rahotanni sun nuna cewa an tsare jirgin ne bayan ya shiga sararin samaniyar Burkina Faso ba tare da izini ba, lamarin da ya haddasa ɗaurewar girar juna tsakanin ƙasashen biyu. Majiyoyin tsaro sun tabbatar cewa batun ya wuce hannun rundunar sojin sama, yanzu kuma Ma’aikatar Harkokin Waje ce ke jagorantar tattaunawar. Wata majiya ta soji ta…
Read More
Majalisar Dattawa ta tantance Fani-Kayode da Omokri a matsayin jakadu

Majalisar Dattawa ta tantance Fani-Kayode da Omokri a matsayin jakadu

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Kwamitin Majalisar Dattawa kan Harkokin ƙasashen Waje ya tantance waɗanda aka naɗa a matsayin jakadu, tsohon Ministan Sufurin Jiragen Sama, Femi Fani-Kayode. An wanke Fani-Kayode bayan ya bayyana a gaban Majalisar Dattawa. Fani-Kayode, wanda kuma tsohon Ministan Al'adu ne, an ba shi damar 'yin gaisuwar majalisa'. An kuma nemi tsohon Ministan Harkokin Cikin Gida kuma Janar na Soja mai ritaya, Abdulrahman Dambazau, ya "yi ruku'u ya tafi" a lokacin tantancewar jakadu a ranar Alhamis. An tattaro cewa a lokacin tantancewar, bayan an gabatar da ɗan gajeren lokaci, an nemi tsoffin ministoci, jakadu da 'yan…
Read More
Za a kuɓutar da sauran ɗaliban Neja lafiya, inji Idris

Za a kuɓutar da sauran ɗaliban Neja lafiya, inji Idris

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Gwamnatin Tarayya ta tabbatar wa al’umma cewa sauran ɗalibai da malaman makarantar St. Mary’s Catholic, Papiri, da aka yi garkuwa da su a ƙaramar hukumar Agwara, Jihar Neja, za a kuɓutar da su cikin ƙanƙanin lokaci tare da mayar da su hannun iyalansu lafiya. Wannan tabbaci ya fito ne daga bakin Ministan Yaɗa Labarai, Mohammed Idris, yayin da ya ziyarci Gwamnan Jihar Neja, Umar Bago, a Minna ranar Laraba domin jajanta wa jihar bisa harin. Tun farko, an riga an ceto ɗalibai 100 daga cikin 259 da aka sace, inda Gwamna Bago ya karɓe su a…
Read More
Kisan Zariya: Za mu haɗu da Buhari ranar lahira – El-Zakzaky

Kisan Zariya: Za mu haɗu da Buhari ranar lahira – El-Zakzaky

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Jagoran Harkar Musulunci a Nijeriya, waɗanda aka fi sani da 'Yan Shi'a, Sheikh Ibrahim El-Zakzaky, ya bayyana cewa tsohon Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari zai fuskanci tambayoyi a gaban Allah Ranar ƙiyama kan kisan 2015 da aka yi wa mambobin harkar a Zariya, wanda ya yi sanadin mutuwar ɗaruruwan mabiyansa. Yayin taron manema labarai da aka yi a Abuja ranar Laraba, El-Zakzaky ya kuma zargi gwamnatin yanzu da karya alƙawarin da ta yi tun kafin ta hau mulki — wanda ya haɗa da biyan diyyar asarar rayuka da dukiyoyi, da kuma fayyace matsayar gwamnati kan harin. Da…
Read More
’Yan sandan Katsina sun kama Sahabi Rabi’u kan zargin kashe mace da jaririyarta

’Yan sandan Katsina sun kama Sahabi Rabi’u kan zargin kashe mace da jaririyarta

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina ’Yan sanda a Jihar Katsina sun kama wani mai suna Sahabi Rabi'u da zargin kashe wata mata da jaririyarta. Jami'in hulɗa da jama'a na rundunar 'yan sanda a Katsina DSP Abubakar Sadiƙ Aliyu ya sanar da haka a wata takardar sanarwa. Ya bayyana cewa, lamarin ya faru ne a garin Sheme da ke ƙaramar Hukumar Faskari, inda ake zargin Sahabi da abokinsa da ake nema ruwa a jallo suka kai matar wajen garin Sheme, inda suka kashe ita da jaririyarta. Kamar yadda DSP ya ce tuni wanda ake zargi ya amsa laifinsa ya kuma tabbatar…
Read More