12
Dec
Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Mutane sun shiga firgici da ɗimuwa a safiyar jiya Alhamis, 11 ga Disamba, 2025, bayan hatsarin mota mai tsanani da ya yi ajalin ɗaliban Jami’ar Jos (UNIJOS) takwas tare da direban motarsu akan titin Zariya da yake cikin garin Jos, Babban Birnin Jihar Filato. Shaidu sun ce, hatsarin ya faru ne a lokacin da wata babbar mota ƙirar tirela, wacce ake zaton ta samu matsalar birki, ta ƙwace wa direban ta bugi ɗaya daga cikin motoci biyu da ɗaliban suka ɗauka, domin zuwa yawon dare. Sai bugun ya fasa motar gabaɗaya tare da jefa ta kai…
