ukarofi

12664 Posts
Matakin da iyaye ya kamata su ɗauka ga ɗansu mai shaye-shaye

Matakin da iyaye ya kamata su ɗauka ga ɗansu mai shaye-shaye

Tare da BILKISU YUSUF ALI Gabatarwa Shaye-shaye (kamar amfani da tabar wiwi da ƙwayoyi da shisha da sauransu) ya zama barazana ga matasa a rayuwar yau. Wannan matsala ta zama ruwan dare a tsakanin matasa da yara ’yan shekara 13 zuwa 25. Lokacin da iyaye ko al’umma suka gano cewa, ɗansu ko wani yaro yana taɓa miyagun ƙwayoyi, da yawa su kan firgita, su yanke ƙauna ko su yi amfani da hukunci da duka da kyama da hantara da janye duk wani tallafi da suke ba shi, maimakon neman mafita mai kyau. To, me ya kamata iyali da al’umma su…
Read More
Sama da miliyan 100 za a raba wa ‘yan kasuwar Masaka da gobara ta shafa

Sama da miliyan 100 za a raba wa ‘yan kasuwar Masaka da gobara ta shafa

Daga JOHN D. WADA, a Lafiya Kwamitin da shugaban ƙaramar hukumar Karu a jihar Nasarawa barista Abubakar Aliyu Madaki ya kafa domin tantance lalacewa da kuma asarar dukiyoyi da aka yi sakamakon wata mummunar gobarar wuta da ta auku a kasuwar Masaka ta garin Karu din a bara ya gabatar da rahoton sa. Kwamitin wadda ke ƙarƙashin jagorancin shugabanta wato Cif Mark Auta a yayin zaman ya kuma ba da wasu shawarwari na musamman dangane da yadda za a aiwatar da matakan hana wuta a kasuwannin domin hana irin wannan abin gaggawa sake faruwa nan gaba da tabbatar da tsaro…
Read More
Zamfara: Matawalle bai taɓa taimaka wa Marafa a siyasance ba – Maikatako

Zamfara: Matawalle bai taɓa taimaka wa Marafa a siyasance ba – Maikatako

Daga SANUSI MUHAMMAD Gusau Shugaban ƙungiyar tallafawa siyasa ta Sanata Kabiru Garba Marafa, Hon. Surajo Garba Maikatako a jihar Zamfara, ya soki shugaban jam'iyyar APC ta jihar Hon. Tukur Umar Danfulani saboda abin da ya bayyana ƙaryar da ke cewa ministan tsaron, Bello Muhammad Matawalle, ya taimaka wa Sanata Kabiru Garba Marafa a siyasance. Hon. Maikatako ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ya fitar ga manema labarai a Gusau ranar Litinin. A cewarsa, sanarwar da Tukur ya yi kwanan nan ta ikirarin cewa shugabansa, Bello Matawalle, ya taimaka wa Sanata Kabiru Garba Marafa a siyasa, ƙarya ce…
Read More
An fara taron al’adu da wasannin gargajiya na ‘Muryar Matasa’ a Katsina

An fara taron al’adu da wasannin gargajiya na ‘Muryar Matasa’ a Katsina

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Ƙungiyar Muryar Matasa mai suna 'Matasa Initiative For Employment Development And Inclusion, ta shirya biki na al'adu da kuma wasanni daban-daban mai taken “Matasa, kasuwanci da Al'adu' a filin wasa na Muhammad Dikko, a garin Katsina. Wasannin da aka shirya ya gudana cikin tsari mai kyau da nishaɗantarwa, inda aka mayar da hankali kan bunƙasa kasuwancin matasa a fannoni uku: Kasuwanci, Al’adu da Wasanni. Shugabar taron Saratu Hamidu Samaila, ta ce sun shirya taron ne domin nuna ma jama'a cewa su ma mutāne masu buƙata ta musamman suna bada gudunmuwa da goyan baya wajen haɓaka…
Read More
Zuwa ga masu tuƙin ganganci

Zuwa ga masu tuƙin ganganci

– Duk wanda yake tuƙin ganganci ba jarumi ba ne, ba ƙwararre ba, bai fi kowa ba. A’a, mutum ne da ke wasa da rayuwarsa da ta wasu. Assalamu alaikum wa rahmatullahi wa barakatuh. Wannan wasiƙa an rubuta ta ne da zuciya ɗaya, da damuwa mai tsanani, da kuma fatan alheri. Ba da ƙiyayya ba, ba da tsinuwa ba, ba da zagi ba. Sai dai da ƙauna, nasiha, tunatarwa da kuma roƙo na gaskiya daga ɗan uwa zuwa ‘yan uwansa. Ina magana ne kai tsaye zuwa gare ku masu tuƙin ganganci – masu karya doka, masu sa rayuwar kansu da…
Read More
Pharmacist Ahmed Ibrahim Yakasai: Jagora mai gina al’umma ya cika shekaru 65

Pharmacist Ahmed Ibrahim Yakasai: Jagora mai gina al’umma ya cika shekaru 65

Daga KABIR SAIDU DANLADI FUNTUA A cikin duniyar da ake buƙatar shugabanni masu hangen nesa, ɗabi’a, da kishin mutane, akwai wasu mutane da fitilarsu ba ta gushewa. A Najeriya musamman a fannin kiwon lafiya, irin wannan haske ya bayyana ta fuskar Pharmacist Ahmed Ibrahim Yakasai — Wanda taimako da tallafinsa sun haɗa fannoni da yawa tun daga ilimi, jagoranci, alheri, kasuwanci, da bauta wa al’umma. An haife shi a 1 Ga watan Disamba, 1960, kuma tun Yana dan karami ya fara karatun Allo, Islamiyya da karatun zamani. daga wannan lokacin ya fara tafiyar da ta zamo ginshiƙi ga dubban mutane.…
Read More
Sheikh Dahiru Bauchi: Ya kwanta dama bayan shekaru 101 masu albarka (1346AH – 1447AH)

Sheikh Dahiru Bauchi: Ya kwanta dama bayan shekaru 101 masu albarka (1346AH – 1447AH)

Daga ALI ABUBAKAR SADIQ Cikin mutane sama da biliyan takwas da suke raye a wannan duniya tamu a yau, kimanin mutane 722,000 a cikinmu sun sami tsawon rai na kai wa shekaru 100 cif. To idan zan yi la’akari da wannan ma’aunin kawai, zan iya cewa hakika Marigayi Sheikh Dahiru Bauchi, na daya daga cikin mutane da Allah ya yi wa wata kebabbiyar baiwa kasancewar ya shiga cikin jerin wadannan mutane da su ka rayu tsawon shekaru dari a duniya. Na tabbatar kuma idan za’a sake wata kididdigar a cikin wadancan mutane masu shekaru dari a duniya, Shehin dai, zai…
Read More
Meye ribar masu aibata Shehu Mujaddadi?

Meye ribar masu aibata Shehu Mujaddadi?

Daga NASIRU ADAMU EL-HIKAYA Kamar yadda wasu magoya bayan Isra’ila a Najeriya ke kawar da kai kan kisan gillar da ake yi wa Musulmi da Kiristoci a Gaza don a wajen su Isra’ila ba ta laifi, haka ne karara ‘yan ikirarin Hausa zalla su ka kau da kai ga mulkin mallakar Turawa da bautar da kakakanni da su ka yi, su ka dukufa haikan wajen zagin Mujaddadi Shehu ɗanfodiyo. Mujaddadi na Musulunci ma ya koma ga Allah kimanin shekaru 86 kafin ‘yan mulkin mallaka su zo don haka shi bai ma gamu da ko ɗaya daga masu jajayen kunne da…
Read More
Satar ɗalibai: Mu taimaka a samar da tsaro a makarantun ’ya’yan mu

Satar ɗalibai: Mu taimaka a samar da tsaro a makarantun ’ya’yan mu

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU Yayin da nake wannan rubutu, har yanzu ɗalibai kimanin fiye da 300 na makarantar firamare da sakandire ta St. Mary's Catholic dake Papiri a Jihar Neja da suka haɗa maza da mata, suna can hannun 'yan ta'adda masu ɗauke da makamai a cikin daji, tun bayan da aka sace su kuma aka yi garkuwa da su a makarantar da suke neman ilimi a ranar 12 ga watan Nuwamba. Wannan ya biyo bayan garkuwa da ɗaliban makarantar 'yan mata ta Maga su 25 da wasu 'yan ta'adda suka yi, waɗanda daga baya suka samu 'yancin kansu, yayin…
Read More
Gidauniyar Mangal ta kashe Naira milliyan 257 domin kula da marasa galihu

Gidauniyar Mangal ta kashe Naira milliyan 257 domin kula da marasa galihu

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Wani mai taimakon al’umma, Alhaji Dahiru Mangal, ya biya kuɗaɗen magani dana aiki da suka haura naira miliyan 257 ga kusan marasa lafiya 21,000 masu rauni a Jihar Katsina, daga 2016 zuwa yanzu. Wani mamba na kwamitin amintattu na Gidauniyar Mangal, Alhaji Hassan Kabir, ne ya bayyana haka a ranar Asabar a Katsina, yayin tantance marasa lafiya masu matsalolin ido. Kabir ya bayyana cewa a cikin wannan lokaci, gidauniyar ta ɗauki nauyin jinyar kusan marasa lafiya 3,000 masu cututtukxan fitsari (urology), da kuɗin da ya haura N140 miliyan. Bugu da ƙari, Kabir ya ce fiye…
Read More