ukarofi

12664 Posts
Sanata Yar’adua ya ba al’ummar mazaɓarsa haƙuri

Sanata Yar’adua ya ba al’ummar mazaɓarsa haƙuri

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina A wata sanarwa da mataimakin sa na musamman kan yaɗa labarai ya fitar ya ce sanatan ya saurari kowa kuma yana tabbatar masu zai yi nazari da kuma kawo gyara. Yar'adua ɗan Adam ne, duk ɗan Adam ajizine kuma ya san ƙauna tasa al'ummar sa basa son su ga wata matsala. "Saboda haka ina bada haƙuri.A bamu lokaci kaɗan mu ƙara nazari domin fidda hanyoyi da za a yi gyara,"Inji Yar'adua. Sanata Yar'adua ya yi godiya bisa shawarwari da masoyan ke badawa domin cigaba da wannan tafiya kuma domin tafiyar jam'iyyar su ta ƙara samun…
Read More
Ba macen da za ta rasa sana’ar yi daidai ita – Khadija Madaki

Ba macen da za ta rasa sana’ar yi daidai ita – Khadija Madaki

"Kusan duk wani ɗan kasuwa bashi ne babban ƙalubale a gare shi" Daga AISHA ASAS  Shafin Gimbiya na wannan makon ya zaga ya zagayo, inda ya yi wa masu karatu kamun wata 'yar ƙwalisa da ta ajiye aiki saboda dalilin kutsawa cikin harkar kasuwancin saye da sayarwa. A 'yar taƙaitacciyar tattaunawar da Manhaja ta yi da ita, za ku ji yadda ta ba sana'a matuƙar muhimmanci ga kowace 'ya mace, inda ta kwatanta duk macen da ba ta da sana'ar yi ko yaya take, to tamkar ba ta san ciwon kanta ba ne. Idan kun shirya, Aisha Asas ce tare…
Read More
Gwamna Raɗɗa ya ƙaddamar da ayyukan raya ƙasa da ƙaramar hukumar Katsina da aiwatar

Gwamna Raɗɗa ya ƙaddamar da ayyukan raya ƙasa da ƙaramar hukumar Katsina da aiwatar

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Ayyukan da shugaban ƙaramar hukumar Hon Ishaq Miƙidad AD Saudi ya aiwatar sun haɗa da gina sabuwar majalisar kansiloli ta ƙaramar hukumar Katsina da gina asibiti a Unguwar Yari Dake. Akwai samar da cibiyar sadarwa ta ICT domin inganta koyon zamani da gudanar da ayyukan gwamnati da sayen motoci ga wasu kansiloli don inganta gudanar da ayyukan su na majalisar ƙaramar hukumar. Gwamna Raɗɗa ya yaba wa shugaban ƙaramar hukumar, Hon. Isah Miqdad AD Saude, bisa jajircewarsa da kuma rawar gani da yake takawa wajen aiwatar da ayyukan raya ƙasa, yana mai cewa irin waɗannan…
Read More
Gwamna Raɗɗa ya ƙara jaddada ƙudirin inganta walwalar sarakuna

Gwamna Raɗɗa ya ƙara jaddada ƙudirin inganta walwalar sarakuna

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Gwamnan ya yi wannan bayani ne a ziyarar ban girma da ya kai fadar Mallamawan Katsina, Hakimin Ɓatagarawa, a ci gaba da rangadin da yake yi a ƙananan hukumomi 34 da ke jihar. Da yake magana da masu riƙe da sarautun gargajiya a ƙaramar hukumar ta Ɓatagarawa, Gwamna Dikko Raɗɗa ya bayyana sarakunan gargajiya a matsayin ginshiƙan zaman lafiya da shugabanci a al’umma. “Sarakunanmu ginshiƙai ne na zaman lafiya da haɗin kai a cikin al’ummominmu. Za mu ci gaba da tallafa musu da kayan aiki da muhimman abubuwan da suke buƙata domin gudanar da aikinsu,”…
Read More
BIDIYO: Yadda Shettima ya isa wajen taron inganta al’umma daga tushe da aka yi a Akwa-Ibom

BIDIYO: Yadda Shettima ya isa wajen taron inganta al’umma daga tushe da aka yi a Akwa-Ibom

Mataimakin Shugaban Ƙasar ya isa Cibiyar Inganta Al'umma ta Unyima Idem da ke mazaɓar Ukanafun/Oruk Anam a jihar domin bada caki ga mutane guda 1,000 da suak amfana da shirin Renewed Hope Initiative na Naira biliyan 1 da aka ware don tallafa wa magidanta Shettima, wanda ya wakilci Shugaba Bola Tinubu a taron ya samu tarba daga manyan jami'an gwamnatin jihar ƙarƙashin jagorancin Maitaimakin Gwamnan jihar, Sanata Akon Eyakenyi. An gudanar da taron ne da nufin tallafa wa magidanta guda 1,000 inda ake sa ran kowannensu zai samu jarin da zai faɗaɗa ko fara kasuwancinsa.
Read More
Juyin mulki 10 da suka girgiza Afirka tun 2020

Juyin mulki 10 da suka girgiza Afirka tun 2020

Daga AISHA ASAS  Daga 2020 zuwa 2025, nahiyar Afirka ta sake shiga wani sabon zamani na rikice-rikicen siyasa, inda aƙalla juyin mulki 10 suka faru, musamman a yankin Yammacin Afirka da Sahel. Sabon juyin mulki a Guinea-Bissau a ranar 26 ga Nuwamba, 2025, ya cika jerin juyin mulki 10 da suka faru tun 2020, wanda ya haifar da matuƙar damuwa daga ECOWAS, Tarayyar Afirka da sauran ƙasashen duniya. Da wannan ne Blueprint Manhaja ta yi duba kan  jerin juyin mulkin da suka faru tun 2020 kawo wa yanzu, wanɗada za mu bayyana maku a wannan mako: 1. Mali – 2020…
Read More
Majalisar Amurka za ta tilasta ƙuri’a kan “War Powers” idan Shugaba Trump ya kai hari ga Venezuela

Majalisar Amurka za ta tilasta ƙuri’a kan “War Powers” idan Shugaba Trump ya kai hari ga Venezuela

A ranar 2 Disamba 2025, wasu sanannun ‘yan majalisar Amurka sun sanar da aniyyarsu ta gabatar da wani tsari mai taken 'War Powers Resolution' wanda zai tilasta a yi ƙuri’a a Majalisar Dokoki idan Shugaba Donald Trump ya yanke shawarar kai wani farmaki kan Venezuela ba tare da samun izinin majalisa ba. Wannan mataki ya fito ne bayan damuwar kan yiwuwar kai farmaki da kuma rahotannin cewa rundunonin Amurka sun aiwatar da wasu harbi a yankin Caribbean, har da wani abin da ake tuhuma ya kashe wasu mutane a wani farmaki na biyu.  Masu kirkiro wannan shiri sun ce manufarsu…
Read More
Rebeca Grynspan ta bayyana kanta a matsayin ‘yar takara don shugabancin Majalisar Dinkin Duniya

Rebeca Grynspan ta bayyana kanta a matsayin ‘yar takara don shugabancin Majalisar Dinkin Duniya

A ranar 3 Disamba 2025, Rebeca Grynspan, tsohuwar Mataimakiyar Shugaban Costa Rica kuma shugabar UNCTAD, ta bayyana cewa idan an yi amfani da ƙa’idojin daidaito da rashin bambanci, Majalisar ɗinkin Duniya za ta samu Sakataren-Janar mace a karo na farko. Grynspan, wacce ake ganin ta fi fitowa a matsayin jagora daga Latin Amurka da Caribbean, ta jaddada buƙatar gyare-gyare a UN da suka hada da bai wa Afirka da Latin Amurka ƙarin wakilci a kotun tsaro (Security Council).  Ta bayyana manufarta ta gyara tsarin, sake gina amincewar duniya da UN, da kuma mayar da hankali kan matsalolin duniya na yanzu…
Read More
Mutane 100,000 sun gudu garin Erati a Arewacin Mozambique saboda tsananin tashin hankali – UNHCR

Mutane 100,000 sun gudu garin Erati a Arewacin Mozambique saboda tsananin tashin hankali – UNHCR

A jawabin da aka gabatar a taron manema labarai na UN a Geneva a ranar 2 Disamba 2025, wakilin UNHCR a Mozambiƙue ya bayyana cewa a cikin makonni biyu da suka gabata, kusan 100,000 mutane sun isa birnin Erati a arewacin Mozambiƙue bayan tsanantawar hare-haren da ‘yan bindiga suka kai a yankuna daban-daban. Yawancin waɗanda suka tsere sun bar komai — ba takardu ba kayan abinci — kuma suna kwance a bude, suna fuskantar barazanar rashin lafiya. Rahotanni sun nuna cewa an sami kone-kone na gidaje, kisan farar hula, da kuma rahotannin tashin hankali kamar fyaɗe da cin zarafi, wanda…
Read More
Dalilin da ya sa ake banƙarewa budurwa leɓe a ƙabilar Kibishi

Dalilin da ya sa ake banƙarewa budurwa leɓe a ƙabilar Kibishi

Su dai waɗannan bayin Allah suna rayuwa ne a yammacin kogin ‘Omo’ da ke kudu-maso-yammacin Habasha, ana kiransu da ‘Kibishi’. Bincike ya nuna cewa su dai waɗannan mutane makiyayane, sannan a kan gane yawan dukiyar kowane gida ta hanyar la’akari da yawan dabbobin da suka mallaka. Addini: Waɗannan mutane suna da abin bauta wanda suke yi masa laƙabi da ‘Tuma’. Sun yi imani cewar shi dai wannan Tuma ya kasancene a cikin sararin samaniya, bugu da ƙari mutanen sun yi imani da al’matsutsai da kuma ifiritai, sun kuma yi imani da cewar su ɗin a karan kansu na iya sanya…
Read More