ukarofi

12664 Posts
Matatar Dangote za ta riƙa samar da lita biliyan 1.5 duk wata a Nijeriya

Matatar Dangote za ta riƙa samar da lita biliyan 1.5 duk wata a Nijeriya

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Matatar man fetur ta Dangote ta sanar da shirin riƙa samar da litar fetur biliyan 1.5 kowane wata ga kasuwar Nijeriya daga watan Disamba 2025 zuwa Janairu 2026, domin tabbatar da wadataccen mai ba tare da tangarɗa ba a lokacin bukukuwan Kirsimeti da shiga sabuwar shekara. Shugaban rukunin kamfanin Dangote kuma Shugaba na Matatar Dangote, Alhaji Aliko Dangote ne ya bayyana wannan shiri a ƙarshen mako. Ya ce, matatar za ta fara sakin litar fetur miliyan 50 a kullum tun daga ranar 1 ga Disamba. A cewarsa, wannan shiri na samar da biliyan 1.5 na fetur…
Read More
Manoman shinkafa sun hango ƙarin faɗuwar farashi a Legas

Manoman shinkafa sun hango ƙarin faɗuwar farashi a Legas

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Kungiyoyin manoman shinkafa a Jihar Legas sun yi hasashen cewa farashin shinkafa zai ƙara sauƙa a kasuwa gabanin bukukuwan Kirsimeti da sabuwar shekara, bayan matakin da Gwamnatin jihar ta ɗauka na rage farashin shinkafar Legas daga N64,000 zuwa N57,000 a kan kowanne buhu. Manoman sun bayyana haka ne a hirarraki daban-daban da suka yi da wakilan Kamfanin Dillancin Labaran Nijeriya a ranar Lahadi a Legas. Rahoton ya nuna cewa gwamnatin Jihar Legas, ƙarƙashin jagorancin Gwamna Babajide Sanwo-Olu, ta yanke wannan mataki ne domin rage raɗaɗin tsadar rayuwa da kuma tallafa wa al’umma a daidai lokacin bukukuwa.…
Read More
Gwamna Abba ya yaba wa Kwastom kan tara biliyan N93.9 a Kano da Jigawa cikin wata 10

Gwamna Abba ya yaba wa Kwastom kan tara biliyan N93.9 a Kano da Jigawa cikin wata 10

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya yaba wa hedikwatar Kano da Jigawa ta Hukumar Kwastom ta Nijeriya kan rawar da ta taka wajen ƙara kuɗaɗen shiga da kashi 10.1 cikin ɗari daga watan Janairu zuwa Oktoban 2025. A cewar bayanan da aka gabatar, sashen ya tara kuɗin shiga har Naira Biliyan 93.9 a cikin wa’adin, idan aka kwatanta da Naira Biliyan 85.3 da aka tara a shekarar 2024. Hakazalika, kuɗazen shiga daga Yankin Ciniki ‘Yantacce na Kano sun tashi daga Naira biliyan 2.6 a 2024 zuwa Naira biliyan 17.7 a 2025, abin da ke nuna…
Read More
Arzikin Nijeriya ya bunƙasa da kashi 3.98 a rubu’i na uku na 2025 – NBS

Arzikin Nijeriya ya bunƙasa da kashi 3.98 a rubu’i na uku na 2025 – NBS

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Hukumar ƙididdiga ta Nijeriya, NBS ta ce arzikin da Nujeriya ke samarwa a cikin gida (GDP) ya ara da kashi 3.98 cikin 100 a rubu'i na uku na shekarar 2025. Cikin rahoton da ta fitar, NBS arzikin cikin gida da Nijeriya ta samu a watannin rubu'i na uku na shekarar ya zarta wanda ta samu a daidai wannan lokacin na shekarar 2024. NBS ta ce, fannin noma ne kan gaba a samar da arzikin da kashi 3.79 sai harkar masana'antu da ya aru da kashi 3.77. A baya-bayan nan dai ana samun raguwar hauhawar farashin kayayyaki…
Read More
Ganduje na tsaka mai wuya a yayin da rikicin APC ke ƙara ƙamari tsakaninsa da ‘yan siyasa

Ganduje na tsaka mai wuya a yayin da rikicin APC ke ƙara ƙamari tsakaninsa da ‘yan siyasa

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Sabon rikici ya ɓarke a jam’iyyar APC bayan da tsohon ɗan majalisa, Sha’aban Sharaɗa, ya yi watsi da shawarar tsohon gwamnan Kano, Abdullahi Ganduje, na mara wa ɗan majalisar wakilai, Sagir Koki, takara. Sharaɗa, wanda ya taɓa zama ɗan majalisar wakilai a shekarar 2019 zuwa 2023, ya shaida wa gidan rediyon Lumana Radio International a ranar Lahadi cewa, ba zai iya mara wa wani ɗan takara baya ba saboda daga mazaɓarsa ba matuƙar ba a bi tsarin da dimokraɗiyya ta tanada ba a lokacin da ake watsi da sauran ‘ya’yan jam’iyya. Rahotanni sun nuna…
Read More
Olisa Metuh ya sauya sheƙa daga PDP zuwa APC

Olisa Metuh ya sauya sheƙa daga PDP zuwa APC

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Tsohon mai magana da yawun jam’iyyar PDP na ƙasa, Olisa Metuh, ya sauya sheƙa zuwa jam’iyyar APC mai mulki. Ya ce ya yanke wannan shawara ne saboda PDP ta kasa goyon bayansa lokacin da yake cikin matsaloli. Metuh, ya daina shiga harkokin siyasa kusan shekaru uku da suka wuce, ya amma ya dawo siyasa ne ta hanyar sauya sheƙa zuwa jam’iyya mai mulki. Ya bayyana hakan ne a lokacin bikin cikarsa shekaru 60 a duniya, wanda ya gudana a Abuja. Manyan ’yan siyasa da dama sun halarci taron, ciki har da gwamnan Jihar Imo,…
Read More
Burina Gwamna Abba ya yi shekara takwas, mataimakinsa ya gaje shi – Hon. Masu

Burina Gwamna Abba ya yi shekara takwas, mataimakinsa ya gaje shi – Hon. Masu

Daga MUHAMMADU MUJITTABA a Kano Shugaban ƙaramar Hukumar Fagge, Hon. Salisu Masu, ya bayyana cewa burinsa shi ne idan Gwamna Alhaji Abba Kabir Yusuf ya samu damar yin wa’adi na biyu ya kammala shekaru takwas a kan mulki, mataimakinsa, Comrade Aminu Abdulsalam Gwarzo, ya gaje shi a matsayin Gwamnan Kano. Hon. Masu ya ce wannan ra’ayi nasa ya samo asali ne daga ganin cewa Gwarzo mutum ne mai gogewa, jajircewa, da kuma cikakkiyar fahimtar akidar madugun Kwankwasiyya, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso. Ya bayyana haka ne a wajen taron raba tallafin jari ga mata 200 na ƙaramar hukumar, wanda aka gudanar…
Read More
ADC ta gama shirin kayar da Tinubu a zaɓen 2027 – Hon. Ungoggo

ADC ta gama shirin kayar da Tinubu a zaɓen 2027 – Hon. Ungoggo

Daga MUHAMMADU MUJITTABA a Kano Shugaban Jam’iyyar ADC na Jihar Kano, Hon. Musa Shuaibu Ungoggo, ya bayyana cewa jam’iyyarsu ta gama shiri tsaf domin fafatawa da karbar mulki daga jam’iyyar APC a zaɓen 2027, kasancewar gwamnatin Shugaba Bola Ahmad Tinubu ta nuna gazawa a fannoni daban-daban na rayuwa. Hon. Ungoggo ya yi wannan bayani ne a wajen taron shugabannin jam’iyyar ADC daga ƙananan hukumomi 44 na Kano, wanda aka gudanar a gidan tunawa da marigayi Malam Aminu Kano (Mambayya House) a makon da ya gabata. Ya ce taɓarɓarewar tsaro a ƙasar nan ya kai wani mawuyacin matsayi, inda ya bayyana…
Read More
Ba za a taɓa haɗa gwamnatin Abba da ta baya ba wajen gudanar da ayyukan cigaba a Jihar Kano – Bello Sumaila

Ba za a taɓa haɗa gwamnatin Abba da ta baya ba wajen gudanar da ayyukan cigaba a Jihar Kano – Bello Sumaila

Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano Jigo a siyasar yankin Sumaila da ke Kudancin Jihar Kano, Hon. Bello Musa ɗan Jam'iyyar NNPP ya bayyana cewa yanayin ayyukan raya ƙasa da gwamnatin Abba Kabir Yusuf take masu kyau da inganci, ba za a kwatanta da gwamnatin APC ta Dakta Abdullahi Umar Ganduje ba. A lokacin da yake zantawa da manema labarai a Kano, Hon. Bello Musa ya ce, “Har ga Allah muna ganin bambanci sosai a wannan gwamnatin idan aka kwatanta ta da ta baya. Ayyuka ga su nan ana ta yi i babu dare, ba rana a ko’ina ga hanyoyi ta…
Read More
Yadda matasan Hausawa na Kuje Amuwo Odofin a Legas suka nuna wasannin gargajiya

Yadda matasan Hausawa na Kuje Amuwo Odofin a Legas suka nuna wasannin gargajiya

Daga DAUDA USMAN a Legas A Legas, kwamitin majalisar matasan Hausawa na unguwar F-Shor da ke ƙaramar hukumar Kuje Amuwo Odofin, ƙarƙashin jagorancin Sarkin Samari Alhaji Tijjani Abdulrahman, ya gudanar da gagarumin taron nuna wasannin gargajiya, domin farfaɗo da al’adun Bahaushe tare da wayar da kan matasa mazauna yankin. Taron, wanda aka gudanar a makon da ya gabata, ya haɗa matasa daga sassa daban-daban na unguwar F-Shor, tare da halartar ’yan kabilu iri-iri. An gudanar da fitattun wasannin gargajiya irinsu damben gargajiya, kokowa, wasan kwai-kwayo, langa da sauran su — duk a matsayin nuni ga al’adun Hausawa na Arewa. Da…
Read More