ukarofi

12664 Posts
Yadda ‘yan kasuwar Mile-12 a Legas suka gudanar da addu’o’in nema wa Nijeriya zaman lafiya 

Yadda ‘yan kasuwar Mile-12 a Legas suka gudanar da addu’o’in nema wa Nijeriya zaman lafiya 

Daga DAUDA USMAN a Legas A Legas, an gudanar da taron addu’o’i na musamman a kasuwar Mile 12 International Market ƙarƙashin jagorancin tsohon shugaban kasuwar, Alhaji Isa Muhammad Mai Shinkafa, tare da babban sakataren kasuwar, Alhaji Balarabe Idris. Taron ya mayar da hankali ne kan neman zaman lafiya da bunƙasar Nijeriya. Taron, wanda ya samu halartar manyan malamai magada Annabaw daga sassa daban-daban na Legas, ya gudana cikin natsuwa da tsari. A farkon taron an raba malaman gida uku, inda kashi na farko suka karanta ayoyi masu tsarki na Al-Kur’ani, kashi na biyu suka gudanar da addu’o’i na musamman, yayin…
Read More
Kungiyar ɗakunan karatu ta buƙaci gwamnati ta ƙarfafa ta

Kungiyar ɗakunan karatu ta buƙaci gwamnati ta ƙarfafa ta

Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano An yi kira ga gwamnati ta bayar da kulawa wurin gudnar da ayyuka da dokar ƙasa ta tanada na kyautata ɗakunan karatu saboda gudanar da ɗakunan karatu a Nijeriya haƙƙi ne da ya dogara ga Gwamnatin Tarayya da na jihohi da na ƙananan hukumomi. Dakta Lawan Umar Shugaban ƙungiyar masu kula da ɗakunan karatu na ƙasa ne ya yi kiran a yayin taron shekara da ƙungiyar reshen jihar Kano suka gudanar a jami'ar Khalifa Isyaku Rabiu a ranar Talata. Ya ce, idan za a inganta ɗakunan karatu su mayar da wurin mai kyakkyawan yanayi da…
Read More
Kungiyar masana zane-zane ta koka kan gobarar da ta laƙume Herwa Heart of Art Gallery

Kungiyar masana zane-zane ta koka kan gobarar da ta laƙume Herwa Heart of Art Gallery

Daga WAKILINMU Sanannen wajen koyar da fasaha na Herwa Heart of Art Gallery, wacce ta shahara a matsayin babban cibiyar ƙirƙira kuma ta samu lambar yabo ta Outstanding Gallery Award daga ƙungiyar ɗaliban Zane-Zane ta Nijeriya (SNA), ta ƙone ƙurmus a ranar Juma’ar da ta gabata sakamakon abin da shaidun gani da ido suka bayyana a matsayin fashewar hasken rana kwatsam. Wannan lamari ya tayar da hankulan maƙota da ke yankin. Akan haka ne ƙungiyar SNA ta bayyana al’amarin a matsayin babban rashi ba ga 'yan ƙungiyar ba kaɗai har ma ga ɗalibai masu tasowa, asarar a matsayin babbar rashi…
Read More
Malami ya ƙaryata zargin hannu a ta’addanci

Malami ya ƙaryata zargin hannu a ta’addanci

Daga JAMIL GULMA a Kebbi Da safiyar Asabar ɗin nan maigirma tsohon ministan shari'a kuma ɗan takarar gwamnan Jihar Kebbi a zaɓe mai zuwa Alhaji Abubakar Chika Malami ya ƙaryata zargin sa da hannu a cikin harkokin ta'addaci da wata jaridar Daily Trust ta wallafa a shafin ta na sada zumunta kwanan nan kamar haka "Binciken Operation Service Wide (OSW) – wanda Buhari ya shirya tun 2021 – ya gano alaƙar wasu manya da B0k0 Háram, ciki har da waɗanda ake zargi suna tallafawa ta’addanci." inda aka alaƙanta waɗansu mutane guda biyu da ba a bayyana sunayen su ba da…
Read More
Taron HIBAF na bana zai tattauna kan rumbunan ilmi – Sada Malumfashi

Taron HIBAF na bana zai tattauna kan rumbunan ilmi – Sada Malumfashi

Daga USMAN KAROFI a Abuja Gidauniyar Open Arts wadda ke gudanar da Bikin Baje Kolin Littattafai da Fasahohin Hausa (HIBAF 2025) ta bayyana taken bikin wannan shekara da sunan "Rumbunan Ilimi. Wannan ya fito daga bakin shugaban gidauniyar Open Arts Foundation Sada Malumfashi a wani taron manema labarai da ya gudana, wanda wakilin Blueprint Manhaja ya halarta. ”Taken bikin na bana zai mayar da hankali ne kan muhimmancin adana ilimi da tarihin al’ummar Hausa, tare da amfani da zamani da fasahohin zamani wajen kiyaye su. Hakan na nufin tabbatar da cewa ilimin gargajiya da na zamani ba su lalace ba,…
Read More
Gwamnatin Katsina za ta faɗaɗa asibitin garin Jibia

Gwamnatin Katsina za ta faɗaɗa asibitin garin Jibia

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Gwamnan Jihar Katsina,Dikko Umaru Raɗɗa ya faɗi haka a garin Jibiya lokacin da ya kai ziyarar aiki a ƙaramar hukumar Jibiya. Ya bayyana ƙudirin gwamnatinsa na faɗaɗa da sake gina asibitin Jibia gaba ɗaya, domin rage cunkoso na marasa lafiya da ke dogaro da cibiyar wajen samun kulawar lafiya. Gwamna Raɗɗa ya ce gwamnati ta ɗauki matakin faɗaɗa asibitin ne bayan wani buƙatu da ɗan madamin Katsina kuma Hakimin Daddara, Alhaji Usman Usman Nagoggo, ya gabatar, inda ya roƙi a faɗaɗa gina muhimman gine-ginen gwamnati da ’yan bindiga suka lalata. Ya tabbatar wa shugabannin gargajiya…
Read More
Gwamnatin Tarayya ta ware Naira biliyan ɗaya domin kammala aikin madatsar ruwan Kaita

Gwamnatin Tarayya ta ware Naira biliyan ɗaya domin kammala aikin madatsar ruwan Kaita

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Gwamna Dikko Raɗɗa ya faɗi haka a ƙaramar hukumar Kaita lokacin da ya kai ziyarar aiki a yankin. Ya bayyana cewa Gwamnatin Tarayya ta ware wannan kuɗi a cikin kasafin kuɗin ƙasa na 2026 domin kammala aikin madatsar ruwan na Kaita da aikin ya tsaya cak. Gwamna Raɗɗa ya ce wannan tallafi babban ci gaba ne ga al’ummar yankin da suka shafe shekaru suna jiran farfaɗo da aikin da aka bari kuma da zaran an kammala aikin zai taimaka wa manoman noman rani ,ya kuma samar da wadataccen ruwan sha a ƙaramar hukumar ta kaita.…
Read More
Gwamnatin Katsina za ta kafa masana’antar sarrafa garin kwaki a Batsari

Gwamnatin Katsina za ta kafa masana’antar sarrafa garin kwaki a Batsari

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Gwamna Dikko Raɗɗa ya faɗi haka a sakatariyar ƙaramar hukumar Batsari a cigaba da ziyarar aiki da yake kaiwa a ƙananan hukumomi 34 da ke jihar. Ya ce gwamnati ta ɗauki wannan matakin ne ganin yadda garin Wajibi da babu wanda yafi su noman rogo a jihar suna shanya rogon a bakin hanya. Garin Wajibi shima mafi girma a ƙaramar hukumar Batsari bayan garin na Batsari. Haka kuma gwamnan yace gwamnatin jihar za ta gina makarantun ƙanana da manyan sakandire guda biyar a jihar. Dikko Raɗɗa ya ce zuwan su Batsari ya tabbatar da zaman…
Read More
An yi garkuwa da manoma 11 a Kudancin Kaduna

An yi garkuwa da manoma 11 a Kudancin Kaduna

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Fargaba ta lulluɓe al’ummar Ungwan Nungu da ke gundumar Bokana a ƙaramar Hukumar Sanga ta Jihar Kaduna, bayan wasu ’yan bindiga sun yi garkuwa da mazauna yankin 11 a ranar Asabar yayin da suke dawowa daga gonakinsu. Mazauna yankin sun ce an tare mutanen ne a wata hanyar daji da ke kusa da unguwar da yamma, inda aka tafi da su zuwa wani wuri da ba a sani ba. Lamarin ya tayar da hankula a ƙauyukan da ke kewaye, inda iyalai da dama suka kwana cikin fargaba. Wani mazaunin yankin da ya nemi a…
Read More
Zargin ɓatanci: Kotu ta amince da ɗage shari’ar Sanata Natasha zuwa Fabarairu

Zargin ɓatanci: Kotu ta amince da ɗage shari’ar Sanata Natasha zuwa Fabarairu

Daga USMAN KAROFI a Abuja Wata Babbar Kotu da ke zaune a Maitama na Birnin Tarayya Abuja, ta amince da buƙatar Gwamnatin Tarayya, inda ta ɗage cigaba da sauraron ƙarar da ta shigar akan Sanata mai wakiltar Kogi ta Tsakiya, Natasha Akpoti-Uduaghan, kan zargin ɓata suna. Alƙalin Kotu, Mai Shari’a Chizoba Orji, ya ɗage sauraron ƙarar, wadda ofishin Antoni Janar na ƙasa ya shigar zuwa ranar 23 ga Fabrairu, 2026, domin cigaba da shari’ar. A baya, Gwamnatin Tarayya ta gurfanar da Sanata Natasha ne bisa zargin yin furuci da ke ɓatanci da keta doka, wanda hakan ke zama cin mutunci…
Read More