13
Dec
Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Raɗɗa ya ƙaddamar da sabon tsarin Gwamnati a yanar gizo (E-Governance) ga manyan sakatarori da daraktoci a ma’aikatun gwamnati (MDAs), a mataki na inganta aiki ga jama’a a jihar. Da yake jawabi a wajen ƙaddamarwar da aka gudanar a KATDICT, Gwamna Raɗɗa ya bayyana wannan mataki a matsayin “babbar tarihi a tafiyarmu ta kafa gwamnati ta zamani, mai inganci kuma mai mayar da hankali kan ‘yan ƙasa a Katsina.”Inji Dikko. Ya ce wannan shi ne mataki na farko na shirin gwamnati marar takarda, “gyaran da aka tsara don sauya…
