ukarofi

12664 Posts
NNPC da wasu gidajen mai sun zaftare farashin fetur

NNPC da wasu gidajen mai sun zaftare farashin fetur

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Farashin man fetur ya sake sauka a Babban Birnin Tarayyar Nijeriya, Abuja, bayan da Kamfanin Kula da Harkokin Man Fetur na Nijeriya (NNPC) da wasu manyan masu rarraba man fetur suka rage farashin lita a gudajen sayar da man. Sabbin bayanai sun nuna cewa a gidajen man NNPCL, farashin ya koma N915 a lita — daga N920 da ake sayarwa baya-bayan nan. Wasu manyan kamfanonin masu zaman kansu irinsu BOVAS da MRS suma sun daidaita farashin nasu, inda wasu gidajen mai ke sayarwa a N910, bayan da a kwanakin baya ake ganin farashin ya kai N945…
Read More
Za mu ci gaba da kare mutuncin ƙungiyar ’yan gwangwan a Nijeriya — Salisu Lale

Za mu ci gaba da kare mutuncin ƙungiyar ’yan gwangwan a Nijeriya — Salisu Lale

Daga DAUDA USMAN a Legas Babban Sakataren ƙungiyar ’Yan Gwangwan na Gidan Kwali, Ojota, Legas, Alhaji Salisu Lale, ya tabbatar da cewa shugabannin ƙungiyar za su ci gaba da ƙoƙarin kare martaba da mutuncin ƙungiyar a Legas da ma Nijeriya baki ɗaya. Alhaji Salisu Lale, wanda asalinsa daga Jihar Kano ne amma yake zama a unguwar Gidan Kwali, Ojota, ya bayyana haka ne a Legas yayin taron bikin ƙaddamar da sabon shugabannin ƙungiyar na yankin ƙaramar hukumar Alimosho. Ya ce, sabbin shugabannin da aka naɗa za su taka muhimmiyar rawa wajen tabbatar da ci gaban ƙungiyar da kare martabarta a…
Read More
Kungiyar Alƙalan Nijeriya ta karrama Gwamnan Jihar Jigawa

Kungiyar Alƙalan Nijeriya ta karrama Gwamnan Jihar Jigawa

Daga UMAR AKILU MAJERI a Dutse Kungiyar Alkalai ta Najeriya ta karrama Gwamnan Jihar Jigawa Mal, Umar Namadi da lambar yabo a matsayan uban ƙungiyar na kasa, saboda ƙoƙarinsa nayiwa Addinin Allah shidima da gyara albashin Alkalai . Kungiyar Alkalan ta kasa wadda Alkali Mudassir Hassan yake jagoranta tace sunzo gidan gwamnatine domin su jaddada goyan bayansu ga malam Umar Namadi Kuma su bashi lambar girma mawa saboda shidimar dayake yiwa musulunci da Kuma irin cigaban daya kawo abangaran sharia a jihar Jigawa. Ya nuna gamsuwarsa da salon mulki irin na Gwamnatin malam Umar Namadi dubada irin gudun mawar da…
Read More
Cin hanci da rashawa sun yi ƙatutu a Nijeriya — ICPC

Cin hanci da rashawa sun yi ƙatutu a Nijeriya — ICPC

Daga MAHDI MUSA MUHAMAMD Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa ta ƙasa (ICPC) ta ce da ana aiwatar da dokokin yaƙi da cin hanci da rashawa yadda ya kamata, da kusan kashi 80 na ’yan Nijeriya na ɗaure a gidan yari. Kwamishinan ICPC na Jihar Kaduna, Sakaba Ishaku ne, ya bayyana haka a wani taron horaswa kan yadda ake kula da amana a ƙananan hukumomi. Ya ce, cin hanci ya yi tasiri sosai a rayuwar ’yan Nijeriya, kuma yana haifar da talauci, rikice-rikice, da jinkirta ci gaban ƙasa. Ya ƙara da cewa, yawancin dukiyar da wasu ke taƙama da…
Read More
An buƙaci ’yan kasuwar Bichi su rungumi tsarin kasuwanci na zamani

An buƙaci ’yan kasuwar Bichi su rungumi tsarin kasuwanci na zamani

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD An jaddada buƙatar ‘yan kasuwar Bichi su rungumi dabarun kasuwancin zamani domin faɗaɗa harkokinsu da tabbatar da ci gaba mai ɗorewa a yankin. Shugaban Hukumar Raya Kogin Hadejia da Jama’are, Alhaji Rabi’u Sulaiman Bichi, ne ya bayyana haka yayin da ƙungiyar Bichi Traders Multi-Purpose Cooperative Society Limited ta kai masa ziyara a ofishinsa da ke Kano. A jawabin sa, Alhaji Rabi’u ya nuna jin daɗinsa kan wannan ziyara wadda ya ce tana ƙarfafa zumunci da haɗin kai tsakanin hukumarsa da ‘yan kasuwa. Ya buƙace su da su ƙara fahimtarsu a fannin lissafi da ƙididdiga, da kuma…
Read More
Kungiyoyin Kannywood sun koka da cire su daga manyan ayyukan fim na NFC

Kungiyoyin Kannywood sun koka da cire su daga manyan ayyukan fim na NFC

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Kungiyoyin masana’antun fim na Arewa biyu – Motion Picture Practitioners Association of Nigeria (MOPPAN) da Arewa Filmmakers Association of Nigeria (AFMAN) – sun aika wasiƙar ƙorafi zuwa ga Hukumar Film ta ƙasa (NFC), suna zargin cewa an ware su daga muhimman shirye-shiryen gwamnati da ke da nasaba da masana’antar fina-finai. A cikin wasiƙar da shugabannin ƙungiyoyin biyu suka rattaba hannu, sun nuna matuƙar damuwa da cewa tun bayan zuwan sabon shugabancin NFC an samu gurbacewar hulɗa, rashin ganawa da juna, tare da abin da suka kira nuni da wariyar cin zarafi ga masana’antar fim ta Arewa.…
Read More
Fitar da ɗan takarar gwamna a Kano a APC a yanzu zai haifar da rarrabuwar kai — Ganduje

Fitar da ɗan takarar gwamna a Kano a APC a yanzu zai haifar da rarrabuwar kai — Ganduje

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Tsohon gwamnan jihar Kano da ke arewa maso yammacin Nijeriya, kuma jagoran jam'iyyar APC mai mulki a jihar, ya gargaɗi masu fitowa suna ayyana wani mutum a jam'iyyar da cewa shi aka amince ya yi takarar gwamnan jihar a babban zaɓen 2027. Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya ce har yanzu lokaci bai yi ba da wasu za su riƙa fitowa suna cewa ga wanda zai yi takara ba saboda a cewarsa hakan zai sake haifar da rarrabuwar kai a jam'iyyarsu ta APC. Tun da farko dai wasu manyan 'yan jam'iyyar APCn ne a Kano…
Read More
Yadda muhawara ta ɓarke bayan ganawar Atiku da Jonathan 

Yadda muhawara ta ɓarke bayan ganawar Atiku da Jonathan 

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Muhawara ta ɓarke a fagen siyasar Nijeriya, bayan wata ganawa da tsohon mataimakin shugaban ƙasar Atiku Abubakar, ya yi da tsohon shugaban ƙasar Good Luck Ebele Jonathan. 'Yan siyasar biyudai basu fito fili sun yi bayanin abubuwan da suka tattauna ba, amma mutane da dama na alaƙanta ganawar ta su da shirye shiryen tunkarar zaɓen shugaban ƙasar na 2027. Ana dai raɗe raɗin cewa dukkansu, na da sha'awar tsayawa takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2027. Ganawar jiga-jigan 'yan siyasar ta gudana ne a Abuja inda Atiku Abubakar ya ziyarci tsohon shugaban Nijeriyar Good Luck…
Read More
Kungiyar ’yan takarar ADC ta Kano ta gudanar da taron tattaunawa kan cigaban tafiyarsu

Kungiyar ’yan takarar ADC ta Kano ta gudanar da taron tattaunawa kan cigaban tafiyarsu

Daga RABIU SANUSI a Kano Kungiyar ’yan takarar Jam'iyyar African Democratic Congress (ADC) ta Kasa reshen Jihar Kano ƙarƙashin jagorancin Hon. Haruna Yahaya Kadana ta gudanar da taron tattaunawa domin duba matsayin jam’iyyar cigaban da aka samu da kuma kalubalen da ke gabansu yayin shirye-shiryen zaɓen da ke tafe. A jawabinsa yayin taron Shugaban ƙungiyar Hon. Kadana ya bayyana irin ƙoƙarin da jam’iyyar ke yi wajen ƙarfafa tsarin ta da tabbatar da cewa tafiyar siyasar ADC ta samu gagarumin ci gaba a Kano. Ya ce jam’iyyar na ƙara samun karɓuwa a wuraren al’umma daban–daban. Ya kuma bayyana cewa kwanan nan…
Read More
Gwamna Adeleke ya koma Jam’iyyar Accord, yayin da Fubara ya koma APC

Gwamna Adeleke ya koma Jam’iyyar Accord, yayin da Fubara ya koma APC

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Gwamnan Jihar Osun Ademola Adeleke ya bayyana komawarsa Jam'iyyar Accord, inda ya ce a cikinta ne zai yi takarar neman wa'adin mulkinsa na biyu a zaɓen da za a yi a shekarar 2026. Gwamnan ya bayyana haka ne a wani taro da ya gudana a fadar gidan gwamnatin jihar, inda ya yi maraba da jagororin jam'iyyar na jiha da na ƙasa. "Tun a ranar 6 ga watan Nuwamba na yanke shawarar komawa Jam'iyyar Accord domin in yi takarar tazarce bayan tattaunawa da na yi da masu ruwa da tsaki da mazauna jiharmu ta Osun."…
Read More