ukarofi

12664 Posts
Shuwagabanni masu goyon bayan Ukraine za su yi taro ta yanar gizo

Shuwagabanni masu goyon bayan Ukraine za su yi taro ta yanar gizo

Fadar shugaban ƙasar Faransa ta tabbatar cewa gungun ƙasashen da ake kira Coalition of the Willing — ƙungiyar da ke ba Ukraine cikakken goyon baya — za su gudanar da wani taro a ranar Alhamis mai zuwa ta hanyar bidiyo. Taron, wanda Birtaniya da Faransa ke jagoranta, zai samu hallarar shugaban gwamnati na Birtaniya Keir Starmer, da Shugaban Ukraine Volodymyr Zelenskiy. Downing Street ta tabbatar da shiga taron. Zelenskiy ya ce Ukraine na shirin gudanar da tattaunawa da jami’an Amurka kan batun sake gina ƙasar da ci gaban tattalin arziki, a wani ɓangare na shirin zaman lafiya da Rasha.
Read More
Australia ta kafa dokar haramta amfani da kafafen sada zumunta ga ’yan ƙasa da shekaru 16

Australia ta kafa dokar haramta amfani da kafafen sada zumunta ga ’yan ƙasa da shekaru 16

Kasashen duniya na zuba idanu kan Australia bayan da ta zama ƙasa ta farko da ta kafa ƙa’idar mafi ƙarancin shekaru 16 ga masu amfani da kafafen sada zumunta, wadda za ta fara aiki daga ranar Laraba. Sabuwar dokar za ta tilasta manyan kafafen sada zumunta goma — ciki har da Instagram, TikTok da YouTube — su toshe shiga ga dukkan masu ƙasa da shekaru 16, ko kuma su fuskanci tarar A$49.5m. An ƙalubalanci dokar daga masana fasaha da masu kare ’yancin faɗin albarkacin baki, amma iyaye da ƙungiyoyin kare yara sun yaba da matakin. Australia na ɗaukar matakin ne…
Read More
Yadda takunkumin Trump kan Lukoil da Rosneft zai iya sauya taswirar man duniya

Yadda takunkumin Trump kan Lukoil da Rosneft zai iya sauya taswirar man duniya

Takunkumin da Amurka ta kakaba kan manyan kamfanonin man Rasha, Lukoil da Rosneft, na iya janyo babban sauyi a taswirar man duniya a shekara mai zuwa, lamarin da zai daƙile tasirin da Rasha ta daɗe tana samu a kasuwannin duniya. Takunkuman, waɗanda suka fara aiki a ranar 21 Nuwamba, sun daɗa rage kuɗaɗen shiga da Rasha ke samu daga man fetur — wanda yake raguwa da kusan kashi ɗaya bisa uku. A yanzu haka, kasashe kamar Turkiyya, Indiya da Brazil sun rage sayan man Rasha, lamarin da ya bar dubban ganga suna lilo a tekuna ba tare da mai saye…
Read More
Duk yunƙurinmu na kifar da gwamnatin Iran ya haɗu da tasgaro – Jakadan Amurka

Duk yunƙurinmu na kifar da gwamnatin Iran ya haɗu da tasgaro – Jakadan Amurka

A wata hira da ya yi da kafar IMI Media Group da ke ƙasar Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE), Jakadan Amurka a Turkiyya kuma Jakadan Musamman kan batun Siriya, Tom Barak, ya yi wani bayani mai girgiza duniya, inda ya ce Amurka ta yi ƙoƙarin kifar da gwamnatin Iran sau biyu, amma babu ɗaya da ya yi nasara. Hirar, wadda aka wallafa a shafin jaridar The National a ranar Juma’a, ta haɗa da bayanan da Barak ya yi game da manufofin Amurka a yankin Gabas ta Tsakiya. A cewarsa:  “Mun yi yunkurin sauya gwamnati a Iran sau biyu, amma dukkaninsu sun…
Read More
Amurka na shirin wajabta binciken kafafen sada zumunta ga baƙi

Amurka na shirin wajabta binciken kafafen sada zumunta ga baƙi

Gwamnatin Amurka na shirin aiwatar da sabon tsari da zai tilasta baƙi daga ƙasashen da ba sa buƙatar biza su miƙa cikakken tarihin kafafen sada zumunta na shekaru biyar kafin su samu shiga ƙasar. Wannan sabon shiri, wanda aka buga a cikin Federal Register a ranar Talata, zai shafi ƙasashe 42 da ke cikin shirin Visa Waiver, ciki har da Birtaniya, Faransa, Ostiraliya da Japan. Yanzu haka, waɗannan baƙin na buƙatar ESTA kaɗai, wanda ba ya buƙatar bayanai masu zurfi. Sai dai a sabon tsarin, gwamnati na neman maido da binciken asusun kafafen sada zumunta da dukkan ayyukansu na shekaru…
Read More
Benin ta nemi a miƙa mata jagoran juyin mulki da ya tsere Togo

Benin ta nemi a miƙa mata jagoran juyin mulki da ya tsere Togo

Rahotanni daga Jamhuriyar Benin sun tabbatar da cewa Laftanar Kanar Pascal Tigri, wanda ya jagoranci yunƙurin juyin mulki da aka katsa a watan Disamba 2025, yanzu yana ɓoye a Togo. Babban jami’in gwamnati ya shaida wa BBC cewa nan ba da jimawa ba Benin za ta tura takardar neman a miƙa shi. Har yanzu gwamnati ko sojojin Togo ba su yi magana a hukumance ba, duk da cewa dukkan ƙasashen biyun mambobin ECOWAS ne. Juyin mulkin, wanda ya haɗa da harbe-harbe a kusa da fadar shugaban ƙasa da kuma kama gidan talabijin na gwamnati, an murkushe shi cikin gaggawa bayan…
Read More
Hukumar CAC za ta rufe masu ‘POS’ da ba su yi rajista ba 1 ga Janairun 2025

Hukumar CAC za ta rufe masu ‘POS’ da ba su yi rajista ba 1 ga Janairun 2025

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Hukumar Kula da Harkokin Kamfanoni ta Nijeriya (CAC) ta gargadi cewa daga 1 ga Janairu, 2026, za ta fara ɗaukar mataki mai tsauri kan duk masu gudanar da harkokin 'Point of Sale' (POS) da ba su yi rajista da hukumar ba, tare da bayyana cewa lokacin sassauci ya ƙare. A cikin sanarwar da CAC ta fitar a ranar Asabar, hukumar ta jaddada cewa dole ne kowanne mai POS ya tabbatar da cikar dukkan ƙa’idoji, musamman yin rajista a matsayin kamfani ko mallakar kasuwanci na mutum ɗaya, domin daidaita harkokin cinikayya da kariyar tsarin kuɗi a ƙasar.…
Read More
Kwamitin haraji ya amince da tsarin da zai bai wa ’yan soshiyal midiya dama

Kwamitin haraji ya amince da tsarin da zai bai wa ’yan soshiyal midiya dama

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta amince da faɗaɗa shirin horar da ’yan soshiyal midiya, waɗanda aka fi sani da 'content creators' kan sabbin dokokin haraji daga mutum 20 zuwa 50, bayan matsin lamba da suka taso daga ɓangarori daban-daban na jama’a. Shugaban Kwamitin Sauye-sauyen Haraji da Tsare-tsaren Kuɗi na Fadar Shugaban ƙasa, Taiwo Oyedele, ya sanar da faɗaɗa shirin a ranar Lahadi, inda ya ce an bi diddigin ƙorafe-ƙorafen jama’a game da rashin daidaito a jerin waɗanda aka fara zaɓa. A ranar Asabar ne kwamitin ya fitar da sunayen 'yan soshiyal midiya 20 da ya…
Read More
Gwamnatin Tarayya ta yi adalci a sabon tsarin haraji na 2026 – Tegbe

Gwamnatin Tarayya ta yi adalci a sabon tsarin haraji na 2026 – Tegbe

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Gwamnatin Tarayya ta tabbatar wa ‘yan Nijeriya cewa ba za su fuskanci wani zalunci ba a aiwatar da sabon tsarin haraji da zai fara aiki daga 1 ga Janairu 2026. Shugaban Kwamitin Aiwartar da Sabon Tsarin Haraji na ƙasa (National Taɗ Policy Implementation Committee), Joseph Tegbe, ne ya bayyana haka, yana mai cewa kwamitin ya ƙuduri aniyar aiwatar da tsarin ba tare da jawo cikas ga tattalin arzikin ƙasa ba. An ƙaddamar da kwamitin ne a ranar Juma’a a Abuja, ƙarƙashin jagorancin Ministan Harkokin Kuɗi da Kodinetan Tattalin Arzikin ƙasa, Mista Wale Edun. An naɗa Sanyade…
Read More
Ba za a samu layukan mai ba yayin Kirsimeti – Dangote

Ba za a samu layukan mai ba yayin Kirsimeti – Dangote

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Shugaban Kamfanin Dangote, Alhaji Aliko Dangote, ya tabbatar wa ’yan Nijeriya cewa zagayowar layukan neman man fetur da kan addabi ƙasa musamman lokacin bikin Kirsimeti sun zama tarihi, domin matatarsa za ta wadatar da buƙatar ƙasa baki ɗaya. Da yake zanta wa manema labarai a Fadar Shugaban ƙasa bayan ganawarsa da Shugaba Bola Tinubu, Dangote ya ce sun riga sun sanar da Hukumar NMDPRA cewa matatar tana da ƙarfin samar da lita milyan 50 a kullum, wanda ya zarce buƙatar cinikin cikin gida. Ya ce, tun daga shekarar 1972 Nijeriya ke fama da layin man fetur,…
Read More