ukarofi

12664 Posts
Zamfara: APC ta soki Gwamna Lawal kan ɗaukar nauyin yunƙurin tsige Matawalle

Zamfara: APC ta soki Gwamna Lawal kan ɗaukar nauyin yunƙurin tsige Matawalle

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau Jami'ar APC ta Jihar Zamfara, APC ta zargi gwamnatin Gwamna Dauda Lawal bisa hanyar kafa ƙungiyoyi bisa abunda ta bayyana shawo kan Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya kori ƙaramin Ministan Tsaro, Dr Bello Mohammed Matawalle daga muƙaminsa. Sakataren yaɗa labarai na jam'iyyar a jihar, Yusuf Idris Gusau ya yi wannan ikirarin a cikin wata sanarwa da ya fitar ga manema labarai a Gusau yau Lahadi. Jami'iyyar ta zargi Gwamna Dauda da abin da ta bayyana ta hanyar amfani da masu zanga-zanga, shugabannin addinai da ma'aikata daga wurare daban-daban musamman a faɗin Arewacin Najeriya da wasu…
Read More
Ƙungiyar cigaban Funtua ta nuna rashin jin daɗin ta kan yadda shugaban jami’ar Funtua ya ajiye muƙaminsa

Ƙungiyar cigaban Funtua ta nuna rashin jin daɗin ta kan yadda shugaban jami’ar Funtua ya ajiye muƙaminsa

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Shugaban ƙungiyar kwamred Mannir Suleiman ya faɗi haka a wata takardar sanarwa ɗauke da sa hannun sa. Ya ce wannan mataki da mataimakin shugaban jami'ar kiwon lafiya na Funtua ya ɗauka abin damuwa ne da ba zai haifar da ɗa mai ido ganin bai daɗe da hawa kujerar ba. Kwamred Suleiman ya bayyana cewa duk da mataimakin shugaban jami'ar ya bada dalilin sa na ajiye muƙaminsa kan abinda ya shafi siyasa "wannan ba wani hujja bane da za ta kai har ya ajiye muƙaminsa,"Inji Suleiman. Ya kuma gargaɗi kungiyoyi har da kungiyoyi masu zaman kansu…
Read More
Rayuwar mata bayan mutuwar miji

Rayuwar mata bayan mutuwar miji

Daga AISHA ASAS *Ta hanyar gina matanku ne kawai za ku samu tabbacin ‘ya’yanku ba za su tagayyara bayan mutuwarku. Kamar yadda aka sani, shafin Gimbiya na jaridar Blueprint Manhaja bai tsaya a iya tattaunawa da mata kan rayuwarsu ba. Shafin kan taɓo matsaloli, cigaba da kuma wani abu da ke ciwa mata tuwo a ƙwarya, don tattaunawa da kuma nema masu mafita. A yau shafin zai yi duba kan halin da mata ke shiga bayan mutuwar mazajensu, wanda ba kasafai ake fahimtar halin da suke shiga ba. Ita mace rayuwarta gabaɗayanta a ƙarƙashin wani take yin ta. Anan ba…
Read More
Tashar Saira Movies ta yi zarra a Arewa akan manhajar YouTube

Tashar Saira Movies ta yi zarra a Arewa akan manhajar YouTube

Daga AISHA ASAS  Tashar nuna finafinai ta Saira Movies ta yi zarra a jerin tashoshin YouTube a faɗin Nijeriya, inda ta kasance ɗaya daga cikin tashoshi 10 da ke kan gaba a duka faɗin ƙasar, inda ta zamo ta huɗu kuma tilo guda ɗaya kacal a cikinsu daga arewacin Nijeriya. A ranar 9 Disamba 2025, YouTube Nigeria ta ƙaddamar da wani sabon jerin ƙididdiga da ta kira “2025 Nigeria Creators & Influencers Ranking & Recap Tool.” Wannan sanarwa ta zo ne ta kafar yanar gizo da kafofin sadarwa — inda aka jera mawaƙa, masu barkwanci, masu shirya bidiyo (content creators)…
Read More
Dayo Amusa ta zama Mataimakiyar Shugaban ƙungiyar Jarumai ta Nijeriya

Dayo Amusa ta zama Mataimakiyar Shugaban ƙungiyar Jarumai ta Nijeriya

Daga AISHA ASAS  A ranar 8 Disamba 2025, Dayo Amusa, fitacciyar ‘yar fim daga Najeriya, ta samu nasarar zama National Vice President ta Actors Guild of Nigeria (AGN) a zaɓen ƙarshe da aka gudanar a Benin, na Jihar Edo. Wannan mataki ya nuna sabon salo a harkar shugabanci a masana’antar Nollywood, inda ake neman gyara, tsari da inganta harkokin fina-finai a kasa baki ɗaya. Dayo Amusa ta bayyana wannan matsayin a matsayin alamar amincewa da ƙoƙarin ta, tare da tabbatar da cewa zata yi aiki tuƙuru domin ganin ‘yan fim sun samu kariya, horo, da dama don ci gaba a…
Read More
Deepika Padukone na shirin haɗa fuska da Vicky Kaushal a fim ɗin Mahavatar

Deepika Padukone na shirin haɗa fuska da Vicky Kaushal a fim ɗin Mahavatar

A ranar 9 Disamba 2025, masana’antar Bollywood ta fara tattaunawa da fitacciyar jarumar Deepika Padukone domin haska ta a fim ɗin Mahavatar, fim ne mai taken tarihi da al’ada (mythological) wanda za ta jagoranta tare da Vicky Kaushal. Wannan mataki ya motsa tsumin sha’awa tsakanin masoya fim, musamman ma waɗanda ke son ganin waɗannan manyan taurari biyu sun haɗu a fim mai girma irin wannan.  Haɗin taurari biyu masu tasiri kamar Deepika da Vicky zai sa masoyansu cika sinima da kuma yin tsokaci a kafafen sada zumunta kamar dai yadda ake yi a yanzu tun kan fitar fim ɗin. Wannan…
Read More
Da ɗumi-ɗumi: Mahara sun kashe wata mata mai juna biyu da ɗanta mai watanni 18 a Kano

Da ɗumi-ɗumi: Mahara sun kashe wata mata mai juna biyu da ɗanta mai watanni 18 a Kano

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano Al’ummar yankin Sheka Sabuwar Gandu da ke ƙaramar hukumar Kano Municipal sun shiga firgici da tashin hankali, bayan wasu da ba a san ko su wanene ba sun kashe wata mace mai juna biyu tare da ɗanta mai wata 18. Lamarin ya faru ne a daren Asabar, lokacin da mijin mamaciyar ya dawo gida daga wurin aiki da misalin ƙarfe 8:00 na dare, inda ya tarar da ƙofar gidansu a kulle. Rahotanni sun nuna cewa mijin, wanda aka ɓoye sunansa saboda dalilan tsaro, ya tambayi maƙwabta bayan ganin gidan a kulle. Sai aka shaida masa…
Read More
Diyar sarki ta haƙura da masarautarsu don ta auri talaka

Diyar sarki ta haƙura da masarautarsu don ta auri talaka

Wata gimbiya 'yar gidan sarauta ta yi watsi da dukan jin daɗin gidan sarauta ta auri wani talaka gama-gari. Wannan na zuwa ne bayan haɗuwarsu a shekarar 2012 a makaranta, lamarin mai ban sha’awa, jama’a sun yi tsokaci sosai kan masoyan, inda aka tattaro maganar jama’a kan batun. Tashar Aljazeera ta ruwaito cewa, za a ɗaura auren gimbiya Mako ta ƙasar Japan da wani talaka mai suna Kei Komuro a watan Oktoba na 2021. A baya kaɗan, an lura cewa ma’auratan sun yi ta yawo a intanet kwanakin da suka gabata bayan dangantakarsu ta zama sananniya ga jama’a. Ta bar…
Read More
Rabari: Kabilar da ke fifita rayuwar dabba a kan ta mutum

Rabari: Kabilar da ke fifita rayuwar dabba a kan ta mutum

Sanin kowa ne cewa abin al’ajabi ba ya ƙarewa a duniya, domin kuwa ga wata ƙabila da ke fifita rayuwar dabba a kan ta mutum, waɗanda su ke ganin da dabba ta shiga cikin wahala gara ace mutum ne ɗan adam ya shiga. Ita dai wannan ƙabila ba wata ba ce fyace al’ummar ‘Rabari’ da ke garin Gujarant ta cikin yankin ƙasar Indiya. Al’ummar ‘Ribari’ sun kasance makiyaya ne, ma’ana masu kiwon dabbobi daga wani ɓangare zuwa wani ɓangare na yankin ƙasar domin nema wa dabbobinsu abinci, basu da takamaiman wajen zama guda ɗaya kasancewar su dai ba mazauna waje…
Read More
Netanyahu zai gana da Trump kan mataki na biyu a shirin Gaza

Netanyahu zai gana da Trump kan mataki na biyu a shirin Gaza

Firaminista Isra’ila Benjamin Netanyahu ya bayyana cewa mataki na biyu na shirin Amurka na kawo ƙarshen yaƙin Gaza ya kusan kaiwa ga aiwatarwa, duk da cewa akwai muhimman batutuwa da ba su warware ba — musamman batun ko za a tura sojojin ƙasashen duniya a matsayin dakarun tsaro a Gaza. Netanyahu ya faɗi haka ne yayin taronsa da Shugaban gwamnatin Jamus, Friedrich Merz, a birnin Urushalima. Ya ce zai gudanar da muhimmiyar tattaunawa da Shugaban Amurka Donald Trump a ƙarshen wata domin tabbatar da yadda mataki na biyu zai tabbata. Fadar Firaminista Isra’ila ta tabbatar a ranar 1 ga Disamba…
Read More