Daga AISHA ASAS
Tashar nuna finafinai ta Saira Movies ta yi zarra a jerin tashoshin YouTube a faɗin Nijeriya, inda ta kasance ɗaya daga cikin tashoshi 10 da ke kan gaba a duka faɗin ƙasar, inda ta zamo ta huɗu kuma tilo guda ɗaya kacal a cikinsu daga arewacin Nijeriya.
A ranar 9 Disamba 2025, YouTube Nigeria ta ƙaddamar da wani sabon jerin ƙididdiga da ta kira “2025 Nigeria Creators & Influencers Ranking & Recap Tool.”
Wannan sanarwa ta zo ne ta kafar yanar gizo da kafofin sadarwa — inda aka jera mawaƙa, masu barkwanci, masu shirya bidiyo (content creators) da ’yan fim (musamman waɗanda ke amfani da dandalin don tallata ayyukansu) a matsayin manyan sunaye da suka fi tasiri a wannan shekara.
Ba wai kawai tsofaffi ba, wannan jerin ya binciko sabbin mawaƙa, masu barkwanci da masu ƙirƙira bidiyo masu tasiri — waɗanda suka yi fice a YouTube a 2025, ta hanyar yawan kallon bidiyoyinsu (views), yawan masu biyan su (subscribers), da kuma yadda suke jan hankalin mutane.
Wannan mataki na YouTube Nigeria ya nuna cewa dandamali kamar YouTube yanzu na da ƙarfi sosai wajen ba da damar cin gajiyar basirar Najeriya, wanda ke nufin ba dole ne ka je sinima ko studio ba. Idan kana da kyakkyawar ƙira ko bidiyo — kana da damar fitowa da samun karɓuwa.
A halin yanzu dai harkar nishaɗantarwa a Najeriya bai tsaya ga fina-finai kawai; ya haɗa da nawaƙa, barkwanci, da kuma shirye-shirye na tattaunawa da mutane sanannu, vlogs, podcasts, da sauran nau’o’in bidiyo wanda hakan ke nufin harkar ƙirƙira ta ɓangaren nishaɗantarwa na ƙara samun fage da kuma dama da ta fi ta baya.
Hakan kuwa wata dama ce ga matasa na bajekolin fasaharsu cikin sauƙi.
Idan muka duba ɓangaren tasirin wannan sunayen da suka fitar kuwa, za mu iya cewa ya ƙara buɗe hanyar samun tagomashi ga mutanen domin ya janyo hankalin masu shirya fina-finai, kasuwanci da masu tallata kaya kan cewa, waɗanne sunaye ne ke da ƙarfi da tasiri don su haɗa hannu da su.
Da yawa daga masu kallo ko neman hanyoyin nishaɗantar da kai yanzu sun fi mayar da hankali kan dandalin internet musamman YouTube — don samun nishaɗi, saɓanin da da aka mayar da hankali kawai gun zuwa sinema ko tashoshin satalai don samun biyan buƙata. Wannan ya ba wa matasa dama mai yawa na fitar da irin baiwar da suke da ita.
Wannan mataki ya nuna cewa ba wai Hollywood ko Bollywood kawai ke da tasiri ba — Najeriya ma na kan sahun gaba a samar da kirkire-kirkire na nishaɗantarwa a yanar gizo.
Matasa masu fasaha, ba tare da babbar masana’anta ko babban jari ba za su iya samun damar haska kansu idan sun yi aiki tukuru da hankali a YouTube.
